← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 138

Sashe 71

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai kallonsu kawai take har suka fita kafin ta ja wani uban tsaki har mahaifiyarta ta yi gagawar banka mata wani kallon da ya sakata sada kanta domin masu kwaliyar ba tafia suka yi, su kansu da mamaki suke kallonta haka kawai sai suka ji girmanta ya zube a idannuwansu domin mahaifiyar mijinta ne ta yima haka, yo kishi hauka ne? Bale gidan sarauta ai ta san da za'a mata kishiya!

Dakin Nadia suka shiga
Irin yanda ta sada kanta abin ya basu sha'awa, gaishe su ta yi kanta a sade sosai
Ummu ce ke kallonta, kwarai ta so shaida ta sai dai sam sai ta ki yarda ko wacece, a haka itama suka ajiye tanfatsetsiyar sarkarta suka fadi cewa nan da minti ashirin za'a shigo a tafi da ita

Daga nan sai suka yi wajen Najeeba

A lokacin da suka shiga, ZAHRA ce tsaye tana ta yi mata vidio tare da wani sauti mai sanyi da ratsa zuciya su duka tana daukansu vidion ne har ita da yaya Dayabu wanda shima ya shigo a karo na uku a yau yana hankalce da kin maganar Najeeba sai dai ya yi murmushi kawai ya kyaleta, gwara ta yi shirun da ta ringa ihun kuka haka kawai kan abinda ba za'a fasa ba

Tun da Anmy ta shigo sai ta ji idannuwanta sun cika da kwallah
Ta kasa yarda cewa Najeebanta ce zaune a wajen nan, saman wata kujera mai alfarma an rufa mata alkyabarta a saman daurin dan kwalin da ta sha mai tsari da kyan fasali

Karasawa suka yi su dukansu sunna kallonta

Anmy ta fi kusanci da ita inda yan matan du suka kara rukunkume Ummu, hakama yaran da ta yi yan kwanakin nan sun matukar sabawa da ita kamar wata mamansu

Anmy ta kamo habarta kadan ta dago dubanta
Sunna hada ido Najeeba ta yi raurau da idannuwanta

Kai Anmy ta ringa girgiza mata a hankali ta ce" kar ki bari su zubo su bata kwaliyar nan an matana, kin ga yanda kika yi kyau? Kar ki bari wannan rana ki yi hawaye
Najeeba kin san farin cikin da nake ciki kuwa?
Da kin san yanda nake jin nutsuwa da auren nan da sai kin fi kowa murnarsa

Kuma juyota ta yi sosai tana amsar sarkar da Dayabu ya bude ya ciro ta zinari ce su dukansu iri daya

A hankali ta shiga daura mata kafin ta ce" abinda muna tare, ina nan fa, ina tare da ke fa

Najeeba ta ringa sauke ajiyar zuciya

Mahaifiyarta ce ta matso kusa da ita

Itama idon ta kura mata, wai ita ta haifi santaleliyar yar nan? Lalle Allah ya mata kyauta ta saka kafa ta shure ta tafiarta?

Murmushi ta yiwa Najeebar dake kallon fuskarta, mamanta sam bata tsufa , bata da kaurin jiki hakan ya sa bata wani zaune ba, sannan cikinta bashi da yannayin wace ta haihu dan mace ce mai matukar kula da kanta
A hankali ta dan lumshe mata ido bata cire dubanta da karfin nan ba hakan ya saka Ummu sakin ajiyar zuciya a boye tare da saka ran watarana zata dubeta

Nan suka lalace sunna ta daukan hotunna da vidio,
Ba wanda ya dauki maganar nasiha, Anmy ce ta katse hakan cewar su bar mata y'a zata yi mata a nitse, to nasihar wacece ba'a mata ba, har mai wa'azi aka kirawo ta mata sosai sai dai abinda ba za'a rasa ba

Sai da aka dauki kusan minti arba'in sannan su Anmy suka fara tafia

A lokacin da suka nufi runfar aka shaida masu Sarki ya hana zama a nan ya umarci a je falonsa na kurya mai dauke da su camera da sauransu

Nan suka nufa cike da ayar tambaya, sunna cike da mamaki

Kasancewar tuni yana cen ciki ya saka Anmy na samun waje suka hakimce ita da Ummu tana hangen su Gimbiya kusa da zinaria da wata yayarta, hakama Nadia tana tare da aunty da wasu yan uwansu biyu manyan mata du sunna zazaune ne saman manya manyan kujerun falon sun cika sosai sosai kowace na dan murmushi idan sun hada ido da wata, su kuwa matan kowace kanta sade da alkyabarta

Wayar da ta dauka umarni ta bada kan a rako Najeeba da zahrau, da dayar matar sarkin

Tana kashewa ta kuma kiran SHAHEED

A lokacin an gama masa wani nadin ana ta binsa da turaruka ne

Tambayar da ta masa kan me yasa ba'a zauna a rumfa ba?

Amsa daya ya bata a hade cewar" Eumfar na dauke da hatsari ne

Ajiyar zuciya ta sauke, gaske ta ga dogarai da mai wasan maciji sunna tsaitsaye sun tsare ko'ina da alamu hayaki zai yi

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa tana mai bin wajen da kallo
Waye? Waye ke son gannin bayan auren yaronta? *Shin yaron nata ake son gannin baya ko kuwa matan da zai aura?*
Ajiyar zuciya ta sauke haka kawai ta tsayar da dubanta kan mahaifiyar Zinaria wace fuskarta ba yabo ba falasa tana yake dai irin kar a ga kasawarta aman sam abin bai kai zuci ba

A kansa zuciyar Anmy kuwa tambaya take *GIMBIYA, shin abin iya kishin ya tsaya ko kun saka kanku a ukun rayuwar duniya da kiyama?*, da sauri ta ringa kore shaitan tana cire maganar daga ranta daidai lokacin da aka shiga shelar za'a shigo da NAJEEBA

Du dubansu suka kai banda Nadia, da kuma zinaria da suke nitse kawunnansu sade

Da mamaki Gimbiya ke kallon wa'inda suka shigo da ita, su biyu ne kawai wato kishiyoyinta sai jakadiya da wasu bayin dake tafe sunna zubar da flowers pink da fari a hanyar da take takawa
A haka har suka karaso wajen zamanta suka zaunar da ita sunna mai gyara mata abin rufarta kanta sade alkyabarta ta rufe gaban fuskarta

Kamshin turaranta tuni ya ringa kaiwa hanci hanci, du kuwa da falon kansa yana da kamshinsa aman kamshin nan nata ya rigaya ya gama kama jikinta sandal Rose na ruwa

Gaban Nadia ne ke dukan tara tara , a hankali ta rike hannun auntynta kanta sade tana jin zuciyarta na mata rawa sosai

Ita dai Gimbiya ta ki dauke idannuwanta, burinta ta san wacece a rufen nan? Dan yanda ta damu ta ga fuskar wace kiahiyoyinta suka shigo da ita ko Nadia bata damu da gannin kamaninta ba! Ina danginta? Shine abinda take ayannawa a ranta

Cen ta yatsine fuska a lokacin da ta yi tunanin yanzu haka wata diyar wani kasurgumin talaka ce aka lulube dan kar a gane

A hankali ta kai dubanta kan takalmin kafar Najeeba
Takalmin fari ne kal kal da shi mai dan gashishika kadan a samanta, sau ciki ne takalmin irin babuche, kyalkyalin dake samansa suma fararen ne sannan ya yi yar kwana kadan
Kana ganninsa ka san babar harka ce

Kuma daga idannuwanta ta yi tana juya su suka hada ido da Ummu

Irin yanda Ummu ke binta da kallo, ita kuwa sai ta kakaro murmushi ta sakarwa umu

Ummu ta yi murmushin itama kafin ta kara gyara zamanta ta kuma daga dubanta ta sauke das a kan y'arta, lalle yanzu ta yarda yarinyarta ta shigo cikin mata, ko Najeeba na so ko bata so sai sun zauna sun yi magana!

Ya kara wasu mintunnan sun kai talatin kafin a shiga fadin" *GYARA KIMTSI, GYARA KIMTSI, A GYARA ZAMA A NUTSU, MAI DAMAGARAM ZAI SHIGO, DAN SARKI JIKAN SARKI, SARKI MAI WUKAR YANKA, SARAUTA GADO CE, DAN MUN GADA BA DAN HAYE BA, GYARA KIMTSI GA GURNANIN ZAKI TAFE, GYARA KIMTSI GA FARI MAI FARAR ZUCIYA FARAR ANIYA NAN TAFE, JINNI NA BAREBARI DA SHUWA ARAB, KAI DAYA MUKE DA KAI TALLL TAMKAR GOMA*

Irin abubuwan da aka ringa fada kafin ya sanyo kansa ya shigo cikin nutsuwa

A shigowarsa ne baki daya du wani turare ya risina,
Du irin kamshin amaren sai nasa ya doke su domin an masa wankan turare ne kamar ba gobe

Tun da ya shigo du suka sada dubansu
Cike da takun kasaitar da du takunsa daya sai zuciyoyin matansa sun amsa har ya kai ga kujerar da ta fi kowace alfarmar ya yi bismillah sannan ya samu ya zauna

Sai da ya ringa bin wajen da kallo daya bayan daya, da hannunsa ya yi umarnin dogaran su juya
Suka juya a tatare sannan ya ja numfashi a hankali ya furta" *ASALAMU ALAIKUM*

Wannan salama tasa , itace sanadiyar da ta saka du wata halita a wajen dago kanta

A daidai wannan lokacin ne idannuwa suka ringa garwaya da junna, da yawa sun dauko amsa salamar ta katse daidaiku ne suka kaita har karshe kafin idannuwan matan nan uku su sarke da junna

Kamar hadin baki, koda yake idan abu ya dakeku haka ne, a tatare suka zabura a wajen da bai dace su zabu tsayen ba, kowace cike da tsoro da mamakin abinda idannuwanta ke ganni a zaune

A rikice ZINARIA ta nuna yatsarta kan NAJEEBA wace hular alkyabarta ta fadi kan kafadunta itama kamar sauran bakinta na rawa ta ce *KE?*

Najeeba ta kalleta na second biyu ta juyi wajen Nadia cike da matsanancin mamaki ta nunata da yar yatsarta itama ta ce *NADIA?*

Nadia kam gaba daya mikewar da ta yi na tsoro ne, domin bata san zasu ga junna a nan kusa ba hakan ya saka ta tsorata da ido hudun da suka yi da Najeeba bakinta na rawa sosai ta budi baki ta ce"

Morning people😌🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

38

A rikice Nadia ta ce" NAJEEBA, dan girman Allah ki saurare ni na maki bayani."

Auntynta ta ja hannunta da karfi
Warce hannun nata ta yi ta ce" aa, kin ga, ki bari na fad'a mata, walahi tallahi da na san mijinta ne zan aura da ban yarda na yi wannan gangancin ba."

Irin yanda take bayannin hankalinta tashe , sannan har ta fara takowa zata k'arasa kusan Najeebar da saurinta.
Chapter 71 · 0% Book details