Sashe 118
Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da mamaki Najeeba ta kaleta, kaikaikai Nadia ce ke gaisheta? Me hakan ke nufi? Sai dai bata nuna wani abu ba saima kallonta da ta kara yi
Murmushi ta sakar mata ta ce" tsakaninki da Allah kunyar su ce ta sa kika gaida ni ko kin haukace? In ba iskanci ba Nadia yau kuma ni zaki gaida? Tunda Allah ya halice mu baki taba gaida ni ba, kin ga bana son iskanci ni walahi "
Murmushin ne itama ya kubce mata, harda sauke ajiyar zuciya ta samu kanta da kai lomar abincinta wanda tun dazu ta kasa ci hankali kwonce sai jujuyawa take
NAJEEBA ta ce" yaya kafarki? "
Nadia ta amsata har wata kwallar farin ciki na son zubo mata ta yi gagawar kokarin mayar da ita gannin hararar da ta wanka mata wace ta tabata ta kwalar ce
Kamar daga sama UMMU dake murmushin farin ciki ta ji NAJEEBA ta ce" wai lafia yau Mama ta yi wannan kwaliyar harda saka jan baki ko ni daya na fahimta? "
Ummu ta zaro ido ta ce" NAJEEBA ina ruwanki? "
Ai kau Ummulkhair da yake itama yar rigimar ce sai ta shiga kilkila daria ta ce" ke yau ne fa, ai na fada maki kin ga shadar da Abih ya saka yau tun karfe shida ya zo gidan nan"
Najeeba ta zaro ido, UMMU ta rankwashi kan Ummulkhair ita kuwa ta rike kan tana kwalkwal da ido, yan uwan kuwa sunna ta kilkila daria
AMMI ta ce" wato yau ku duka kun takan dokar cin abinci ko? Najeeba zaki min shiru a wajen nan har cikinki ya koshi kafin ki min surutu"
Shirun sukai aman Najeeba sai sauri take ta gama
Tana gamawar ta dauke plate din ta kai shi kicin ta wanke ta ajiye ta fito
Tun kafin ta zauna ta shiga ratabo abubuwan da ta zo da su, maganar zuwan Yarima, fadan a kan me basu lekata ba, tambayar yanzun wace makaranta yar uwarsu take domin ta tafi school, ta idasa da fadin ya dace su kira makadin da zai masu casun auren soyaya
Yanzun kam AMMI din ce da kanta ta kilkile da daria ta dauki dan filow din kujera ta jefawa Najeeba ta ce " ja'ira "
Ummu kam wata irin kunya take ji, wace da safen murje idannuwanta ta yi tasss ta fito abinta aman yanzu NAJEEBA du ta sakata jin wata irin kunyarsu walahi
....................FADA................
An gurfanar da sarkin Bulala dake rusar kuka tamkar ransa zai fita yana magiya da fadin shi bai taba yarda da maganar kisa ba
Sabon sarkin dogarai ne ya doke bakinsa cikin wata irin razananiyar murya da tsoratarwa ya ce" tuf, rufe mana baki maciji! Yi mana shiru mai fuska biyu, da na halak baya cin duduniyar uban gidansa koda kuwa za'a karsa idan bai bada hadin kai ba, tunda har ka rike shi ka kasa fada mar Sarkin Damagaran ai mai sauraronka ne, na so ace a nan za'a bara min kai da ka bambance horo shashanci "
Kara hade hannayensa yake yana rusar kuka da magiya,
Shaheed ya dago idannuwansa daga yannayin zamansa na saraki ya sauke dubansa a kansa, irin yanda suke nema masa aduwa da sauransu , suke fatan Allah ya huci zuciyarsa du gasu a zube a gabansa sai ya dan juya kai cike da haiba ya ce" Na yafe maka "
Baki daya mamaki ya saka su dagowa, bai kasa da gwuiwa ba wajen furta" ku daina hantararsa, ku daina wulakanta shi, ku bar shi da halinsa "
Da sauri sarkin Dogarai da yake wani irin jibgegen katon da ya ninka amintace a kirar da kamar mazan da dakiyar ya kai gwuiwarsa kasa ya hade hannayensa , cikin wata zaburariyar muryarsa ya shiga" Adali ne, dan halal ne, shi daya ne tak irinsa babu, Gafara dai malan dan malan jikan malan, gafara dai mai gida mai dawa, mun yarda cewar a saman hanya ka kwana, mun ruguje mai sauko min mangari mai harara, takawarka lafiya bijimi uban gaya, ya karba ya gode, Allah ke kare gabanka da bayanka, sannu sannu sarkin sarakuna, mai dogarai a baba dogarai ya gaishe ka ubana "
Da kansa yake amsawa har aka kama sarkin bulala aka fitar da shi daga fadar
Zama aka kara yi , zaman da aka gabatar da nasiha mai ratsa zuciya, aka gabatar da sharuda masu girgiza munafuki, aka tashi a kan magana daya cewar du wanda ya taka doka zata taka shi!
Daga nan masalaci aka shige dan gabatar da sallah, bayan an gama ne aka mayar da auren NANA MARYAMA UMMU, DA ABIH WATO ELHAJ MUTALAB gaban dubin jama'a ciki harda yayan Mardiya da bai san da zancen ba, suka hadu kuwa suka ringa taya shi murna domin sam hakoransa sun kasa rufuwa murmushi yake abinsa hankali kwonce
A lokacin da SARKI ya mike sunna dan takawa da kimah, dogarai na tafe da lema baba wasu da bulalai gaba da baya sunna tafe a hankali, haka kuma masu kira na yi Liman ya ce" ALLAH ya taimake ka, sai nake gannin kamar bai dace a saki sarkin bulala na da haka a cikin gari ba, idanfa ya kara aiwatar da wani cutar ta hanyar hada baki da wani a cutar da kai? "
Sai da SHAHEED ya kara taku kamar biyar sannan ya dan ja ya tsaya,
Hannunsa mai dauke da zobunnan azurfa biyu na dama ya mika ya kama hannun Liman cikin rawaninsa, a sanyaye ya ce" ALLAHN da ya fargar da ni kan wannan yinkurin cutar da ni din da suke, shi zai kuma kare ni Liman, na tabata ba abinda ke samun bawa face wanda Allah ya hukunto masa, ban raina mutun ba, na san ba abinda mutun ba zai iya shukawa ba, sai dai kuma na yarda cewar akoy wanda ya halici mutun, shi yasa nake kai masa kukana kan ya hanna, ya kare, ya kuma kiyaye jinnin ALIYU "
Murmushi ya yi yana gyada kai, ba shi ya juya ba hat sai da suka karaso kusa da bangaren Ammi sai shi ya ja ya juya, aman kuma a lokacin Yarima ya iso, hakama da manyan mutanen da suke tafe dan su shigo su yiwa AMMI ALLAH sanya albarka
Kasancewar shine a gaba sauran na take masa baya , sai da ya fara saka kansa
Sai dai maimakun ya bada hanya jama'a su samu shiga sai ya juyo ya yi tsaye a kan kofar ya kasance mutanen suma du suka tsaitsaya sunna kallon sa
Sarkin dogarai ne ya karaso ya duka sosai ya shiga tambayar ko da abinda ya manta ne a je a dauko? Sai dai bai ce uffan ba, hasalima lebensa na kasa a dan dantse yake ya yi shiru bai bada amsa ba
Gannin haka ya saka sarkin digarai mikewa ya shiga salamar mutane, yana mai fadin sako zai ishe GIMBIYA , sarki na godiya
Haka dai du aka watse saura Yarima da shi,
SULTAN ya dan yi gyaran murya a hankali ya ce" dan dakata ina zuwa "
Daga haka ya juya ya shige falon da tun shigowarsa ta farko yan matan suka nutsu, UMMU kuwa mikewa ta yi ta shige dakinta dan iya shegen yan matan nata kam yana beman hanna mata zama , AMMI sai daria take tika abinta nishadi take ciki sosai
kasa suka zube suka shiga gaishe shi,
Bai amsa ba daga tsayen da yake yake bin su da kallo
A hankali ya ce" Ummu, ki tashi ki shirya, yar uwarki ta raka ki bangaren saukar baki ku gaisa da yarima, kar ku jima "
Daga haka ya samu waje ya zauna ya maida hankalinsa wajen mahaifiyarsa
Ciki suka shige su uku, aka bar Nadia zaune kanta kasa, da yar uwarsu wace ta taso daga school nesa kadan da su aman su dukansu sun nutsu sosai
A cikin daki kuwa dama a shirye suke, sai kawai suka kara kawata shirin Ummukulsum, wace jikinta du a mace yake, karara ta nuna masu tsoronsa take ji, aman sun ki su bata dama hasalima suna karfafa mata gwuiwa ne
A lokacin da suka fito sai baza kamshi suke
Niyatsu tafia ne tatare su duka sai da AMMI ta yi kirran sunnan Najeeba
NAJEEBA na tahowa da hannunta ta nunawa biyun su tafi,
Boyayiyar ajiyar zuciya ya sauke, domin tun shigowarsa yake satar kallonta, a lokacin da du suka duka har ita har Nadia, haka kuma da suka tashi sukai ciki bayanta ya bi da kallo, a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake 'na shiga uku ni kau da yarinyar nan, so take ta masheni wani wawan namiji da alamu'
Tana dawowa ta dan duka wajen AMMI daga gefe tana mai fadin" Na'am Ammina? "
AMMI ta yi mata murmushi tana shafa gefen kumatunta, bata ce komai ba ta mike tsaye ta kama hannunta ta zaunarta a nan, sannan ta kamo na Nadia da Ummi ta zaunar da NADIAR kusa da ita kadan sai kuma ta tafi da ummi din rana dan masu murmushi dan kuwa maganar da ta gama masa kennan kan ya dace su yi zama irin wanda ake yi, su yi magana ya masu nasihar zaman lafia sannan ya raba masu kwanaki bisa shawararsu, idan ya so Nadia ta koma dakinta itama auntynta na nan tafe idan an jima dan ta yi waya ta fadi abinda ya tsayarta bata gama hada kayanta bane
Shiru ne wajen ya dauka, tamkar ba kowa haka wajen ya dauka, su dukansu kawunnansu a kasa yake sunna kallon kas, shi kuwa tamkar bai san an yi ruwansu ba ya share su yana zaunensa dai kikam abinsa
A hankali NAJEEBA ta dago dan walahi wuyanta ya sage ta kai dubanta wajensa, ido hudun da sukai da wannan kallo nasa na tsana da yake binta da shi ya sakat kawar da dubanta tana turo bakinta gaba, a kasan zuciyarta ta shiga fadin 'shin yaushe zai bar yi min kallon tsana ne ni '
Shi kuwa kuma binta da kallon ya yi, shima ayannawa yake 'kamar ba ita ta gama min rashin kunya ba, ko me ta yi a bayin ?'