← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 138

Sashe 33

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabanta ne ya kara tsinkewa ya yanke ya fadi har tana dafe gaban nata, ita? Ta shiga motar sarki? Ta zauna a ina? Wato ya makure mata wuya ya karya mata kai ya halakata ya kasheta dama abinda yake nema kennan ya ga ta mutu? Bama wannan ba, ita da zata je wajen cen dan ta yi neman magana ta hanyar samun kula alakar soyaya da mijin matar nan idan suka je aka yi mata binciken a gabansa aka shaida masa lafiyarta kalau yaya zasu kwashe?
Ita kam ta rasa meye aikin wannan jarababen! Idan ba jaraba ba ko abin aunawar ka nemi a kawo maka ai kawo maka shi za'a yi har dakinka na baci ka yi aune aunen aman shine zai wani je da kansa?

Fuskarta ta kara shagwabewa ta ce" Anmy, to ya bani sakon mana na yo masa ni, ko kuma ki ce da shi ya tafi kawai ni fa na warke

Anmy ta dago daga danna watar da take tana magana da mahaifiyar Najeebar kan Najeebar ne kuwa uwar na so ta hasko mata ita a hoto ta ganta aman ta rasa ta yanda zata daukar mata ita ta harareta ta ce"

YAU NA YI DA YAWA😓[1/27, 7:59 PM] Ummu Suhan😍: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

19

Sai da Anmy ta harareta ta ce" NAJEEBA MUTALLAB, tashi ki dauko min alkyabarki

Najeeba ta kara turo bakinta ta mike jikinta a sanyaye ta dauko alkyabarta fara aman kuma adon baki ne ya fi yawa a jikinta ta saka sannan ta bade jikinta da turare ta dauki yan cenji da wayarta ta dawo falo

Jakadiyar dake duke ne ta shaifa mata cewa har sun fito ita suke jira

Kollan Anmy ta kuma yi, sai ta ga Anmy din ta dauketa hoto da wayarta tana dan murmushi ta ce" ki fan saki fuskarki mana kema an mata

Bakinta ta kara turawa gaba ta juya tana tafe a hankali tamkar wace kwai ya fashewa a ciki jakadiyar na biye a bayanta tana nuna mata inda zata bi din hanyar da zai bi ya fita ba budadiyar hanya bace

Gabanta banda faduwa ba abinda yake, har sai ta fara jin da gaske wani zazabi na son kamata da karfin gaske ba da wasa ba
Ita dai ta san ya tsaneta, duda bata san falilinsa na tsanar nata ba
Takan kama mugun kallo daga gareshi, harma da kallon da zata iya kiransa na kyama

Tun fa ta nuna mata motar sai ta ja ta tsaya kanta sade

Najeebarma ta tsaya tana kallonta, muryarta na dan rawa rawa ta ce " mu, mu je mana

Da sauri Jakadiyar ta dago, sai kuma ta mayar da kan nata tana dan girgiza kai ta ce" Allah ya huci zuciyarki amintacen sarki kadai ke shigowa wannan waje ko ZINARIYARMU bata taba saka kafarta a wannan hanya ba, domin hanyar boyayiyar fita ce ta sarki

Sai ta ji ta kara tsorata da bayannin jakariyar, hanyar boyayiyar fita? To a kan me za'a zo da ita nan? Ko dai a nan ne ya yi niyar kasheta ya huta?

Idannuwanta ta rintse tana jimke wayarta a hannunta
Najeeba mana, meye haka ne? Ki je, ki je kawai, ki yi tawakali da Allah, ba zai kasheki ba ......zuciyarta mai karfin ke karfafa mata gwuiwa, nan take matsoraciyar shawararta ta ce" aa, ki rubuta message ki bari a wayarki, idan aka ga kin bace shine! Dan mutumen nan shi kansa kama yake da aljannu!

Hannayenta na rawa ta fitar da wayar ta rubuta message ta yi seving a wayar nata sannan ta shiga karasawa jimin motar jikinta du a mace

Mutumen dake tsaye ne ya saka gabanta yankewa ya kara faduwa
Wani irin girma ne da mutumen tamkar wanda ya fi ka'idar tsayin dan adam
Gashi da wani irin jiki mai abin tsoro, fuskarsa kuwa zata rantse bai taba sallah ba dan ba annurin hasken sallah a tatare da ita ko daya!

Bude mata motar ya yi ba tare da ya furta ko A ba

Da sauri sauri ta daka dan tsale ta shige motar gabanta na faduwa ta zauna tana ta waige waigen tsoro

Wata kwalba ce ajiye saman kujerar daga tsakiya haka, kwalbar mai duhu ce sannan ga duhun cikin mota hakan ya saka sam bata gane ko meye a ciki ba
Cikin motar ba kowa sai wani irin sanyin AC din dake kunne da kuma wannan dadadan kamshin turaran nasa

Hannayenta ta dora saman cinyarta ta jingina da jikin kujerar ta saki wawuyar ajiyar zuciya da tarin sarewar dake adabarta
A hankali ta ringa furta kalamai kamar haka" ke kuwa ta haka zaki mutu ashe Najeeba? Koba motar zai yi ya ce na yi hatsari ko wannan katon zai saka ya dane min hanci sai na daina motsi? Wayo su auntyna zaku yi rashina, wayo yayana kana ina? Yau du ban ganka ba kuma ban nemeka ba, yayana ka yafe min irin rashin jin da nake maka
Wayo Anmyna ki gafarta min ba zan kuma yin karyar ciwo ba kin ji?
Ya Allahna ka bani ikon mutuwa da kalmatus shahada ,
Allah ka yafe min laifukana ka rufa min asiri

A kadan ta dauki wasu mintina talatin gaba daya ta gama hada zufa ta gama ficewa a hayacinta harda yar kwalarta, jira ai ko na result din exam bashi da dadi bale jiran kila wa kala za'a kasheka ne ko za'a wujijigaka a yarda banza? A yan sekwanin sai ta samu kanta da wata irin nadamar rayuwa,
Yo ita me ta masa?
Duk irin sufanta shi da take da abubuwan da ba su ba sai ta ringa fadin" wasa ne, ban taba tunanin hakan a cen cikin zuciyata ba, na tabata kai ha barawo bane kar ka kasheni ka rufa min asiri

Bude gefen damar da aka yi, da murya kasa kasa ana fadin" takawa sannu sannu dan sarki jikan sarki, takawa sannu sannu mai damagaram ikon Allah, gabanka haske, bayanka haske d'a daya kake mai ja da arne

Kamshin turaran nasa da ya fara shigowa motar mai yawan gaske ya sakata sauri kara buda idannuwanta sannan ta rabu da jikin kujerar ta yi gagawar gyara zamanta ta nutsu ta sada kanta tamkar wace ta zo makaranta

Kafin ya daga kafarsa ya shiga motar ya jima kamar wanda zai hau mahaukacin doki
Shigowa ya yi cikin motar ya yi wani irin zama irin na hamshaki sannan aka mayar da marfin aka rufe

Mutane biyun nan sune suka shiga cikin motar , gabjejen nan shine amintacen sarkin shi ya ja motar a hankali sai wanda ke dan kurarin a gefensa rike da abubuwan makamai kamar wanda zai yi artabu da mugun abu a gabansa

Kwalbar nan dake ajiye wace ta gaje wajen harma tana gogar jikinta ya dora fari kar din hannunsa mai dauke da jijiyoyi a jikinsa manyan gaske ya bude marfin kwalbar

Hannunsa ya zirawa safar hannu ya saka cikin bakin kwalbar ya janyo abinda ke ciki

Wani irin kuuuuuu da cikin Najeeba ya yi a lokacin da wutsiyar macijin ta dan hau gefen cinyarta har tana wani irin yawo da dan karfi tana neman a saketa

Wuyansa ya rike raf sannan ya dan gyara muryarsa kasa kasa sosai ya ce" *bani matacen*

Da wani irin gagawa na gefen direban ya buda wata kwalbar, ashe ita kuwa tana dauke da abin sanyi ne wanda zai hanna macijin rubewa ya yi tsami ya lalace ba tare da an yi binciken da ake son yi da shi ba

Amsa ya yi ya dago kansa ya daidaita da mai ran

Irin yanda yake dilo harshensa yana yi masa tamkar giftawar mashi ya sakata sakin wata wawuyar ajiyar zuciya gaba daya jikinta ya dauki rawa
Irin yanda ya rike macizan a hannayensa sai shi kansa ya zama wani abin tsoron a gabanta

Kamar mai cutar asthma haka ta ringa jin numfashinta na yi mata rawa

Kallon macijin yake kallo irin na tsanaki
Sai da ya gama a kasalance sannan a gajarce ya ce" *aman yaya aka yi shi wannan yake da kiftu a gefen kansa dayan kuwa bashi da shi?*

Allah ya huci zuciyarka wannan kiftu da kake ganni shine kawai abinda ke bambance macizan da aka kyankyashe a rana daya
Shi kiftun nan kala biyar ne,
Irin wannan dan siririn shi ya kara shaida min cewa shine abokin haihuwarsa sannan kalarsa ne tak tak , du abinda wancen zai yi wannanma yana iya yinsa, Allah ya kara maka lafiya
Ya karashe yana dan kara dukawa

Bai kuma yin magana ba sai mika masa matacen sa ya yi ya karba da hannu bibiyu yana gagawar mayar da shi cikin kwalbarsa, sannan ya kara dago mai ran yana yi masa kallo irin na kurullah

Tabas idan a da wasa ta yi karya ta yi cewar zuciyarta na suka a yanzun kam sukar take, gaba daya jikinta ya mace ya yi mata nauyi har bata iya daga dan yatsarta
Idannuwanta kawai take yawo da su a kansa ta yi wani kasangar tana hangen gashi har ya sakar mata macijin ya kasheta
Aman dan me yake son kasheni da maciji? Ya kasheni da hannayensa mana?

Take tambayar kanta a kasan zuciyarta ga zufa ta gama wanke mata duban wani waje na jikinta

Wutsiyarsa ya kara dokawa a saman cinyarta yana neman a sake shi ya kwaci kansa, irin yanda maciji ke wutsil wutsil dan kwatar kansa
Hakan ya saka ta saki ajiyar zuciyar da ta kara sakata jin tamkar cutar nan mai shanyewa mutun jiki ya zama baya jin yana iya anfanar da komai na jikinsa da kansa ne ya sameta wato cutar hawan jinni da ilolinta

Sai da suka yi tafia mai dan nisa suka samu wani waje mai dan duhu duhu sannan direban ya taka birki ya tsaya

Wani shirun ne ya biyo baya na kamar minti goma,
NAJEEBA ta ringa maimaita kalmar shahada daga yannayin da take dan ta dauka an zo wajen da za'a kashetan ne
Chapter 33 · 0% Book details