← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 138

Sashe 18

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga mamakinta sai ya saki abin karewar ya bata damar fita kennan
Hakan ya sakata dan kure shi da ido tana mamaki, sai dai gannin ya hade rai shima yama daina kallon nata ya sakata daga kafadunta har tana ayanna lale gidannan sun fara sasauta tsaro

Shi kuwa tana fita ya juya ya danna kira ya shaidawa mai bayar da tsaron fada cewa eh ta fita

A hankali take takawa tana gannin yanda garin ke walwali idan dare ya yi

Manyan fitilun bakin hanya masu bada jan haske sun gama ko'ina sun haske garin

Motoci da mashin da keke da masu tafiar kafa kowa na kai kawonsa tamkar ba dare ba
Shagunna du a bubude
Shagunnan atampopi ne, na dogayen rigunna ne, na jakunkunna ne abin dai ba'a cewa komai garin nada yannayi mai dadi da tsaro koda dare ya yi

Bata da fito da ko sisi ba, dan haka ta yi niyar takawa a kafarta duda wajen sa dan nisa ta tabata ba zata rasa mai rage mata hanya ba

Wayarta kuwa ta kunna ba zata kiraye shi ba sai ya kuma kira idan yana nan sai ta fada masa inda take idan kuwa baya nan ya yiwa kansa

Har ta gifta tankamemen shagon da ake siyar da kayan kwaliya da su atash da turaruka na yan gayu masu jiji da kansu ta dawo

Da wayo ta ringa hangen ciki
Gannin yau Elhajin ne da kansa ba yaron nasa ba ya sakata hawa yar matatakalar kofar shagon ta tura baban madubin kofar dake kofa ta shiga

Irin sanyi da kamshin yannayin shagon ne ya buso mata baki daya jikinta hakan ya sa ta lumshe idannuwanta sannan ta kuma budewa tana kallon shagon

Bata yiwa kowa magana ba kamar yanda kowa ke sha'anin gabansa yana siye siyensa

A hankali ta ringa bin wajajen tana dudubawa

Abin turawa ta dauka ta shiga bi waje waje tana zabar manyan hodoji da su turaruka masu kyan gaske da tsada tana sakawa

Sai da ta ga an rarage mutanen cikin shagon sosai sannan ta nufo wajen Elhajin tana tura keken daukan kayan

Tana zuwa ta sakar masa murmushi cikin sansanyar muryar nan tata ta ce" barka da warhaka Elhaj

Elhaji dake zaune da katon tumbinsa a gaba shima ya sakar mata murmushin yana fadin" barka dai yar budurwa sannunki da zuwa

Bata amsa ba sai dauka da ta shiga yi da daidaya tana dora masa a saman table din bayan ba nan ake kaiwa ba akoy masu amsa su irga komai su fada maka nawa ne ka biya a zuba maka a leda a raka ka har wajen abin hawanka

Daya daga cikin yaran ne ya taso da sauri yana fadin" Hajia ba nan ake kai kayan ba cen ake kaiwa

Da sauri ta ce" eyah, ban sani ba ai

Hannayensa ya saka zai kwashe kayan sai ya ji muryar Elhajin na fadin" aa kai bubakar barsu a nan nima ai ba wani abu nake ba zan irga mata

Bari yaron ya yo ya koma suka ci gaba da kulawa da mutannen

Sai da ta gama ajiye masa komai sannan ta dan taka karfen jikin kujerar dake gaban table din ta hau tana lumshe idannuwanta

Ajiyar zuciya ta sauke tana yarfe hannunta ta saci kallon Elhaj ta ga ita yake kallo dan haka ta dube shi ta dan yatsina fuskarta ta rage muryarta sosai a hankali ta ce" na gaji sosai

Kamar wani wawa ko yaro karami haka Elhaji ya saki daria yana fadin" sannu hajia ai da kin sakani dauko maki da kainama sai na yi aikin gashi kin sha wahala bayan kin fi karfin shan wahala

Murmushi ta yi tana kara sauke ajiyar zuciya

Muryarsa ya dan daga ya ce" kai dahiru dauko faro maza

Da sauri saurayin da aka kira da Dahiru ya juya ya dauko ruwan faro ya ajiye har biyu a gabanta

Kayan Elhajin ya shiga warewa yana sakawa cikin manyan ledojin kampanin yana yi yana kallon Najeeba wace ta kawar da dubanta tana danna wayarta

Kiran gangan ta kara a kunnayenta ta shagwabe fuskarta sosai ta turo dan lebenta na kasa sannan ta lumshe shanyayun idannuwanta ce" yaya

Irin yanda ta fadi yayan dole ko ke mace ki kaleta harma da sakin baki, domin jan yayan da ta yi sannan ta idasa da wani dan gurnanin kukan shagwaba

Yan kafafuwanta dake jikin table din ta shiga dan bubugawa ta ce" yaya ina kampanin fa, har na zo na zabi abubuwan da nake so ka yi ka zo ka kawo kudin mana......

Ta kasan ido ta saci kallon elhajin, irin yanda yake sakin murmushi baki daya hakoransa a waje hakan ya baiwa kumatunsa damar kara girma, micik micik din idannuwansa suka kara dan shigewa sai dai kamshi kam yana ta fitar da kamshin miski kansa kuwa sanye da huka

Hular dake kansa ya kara turowa gaba yana kallon shagwababiyar yarinyar
Tashin hankali ya furt a kasan zuciyarsa
Yo wannan na sameta nima na koma danye sharaf, dan na tabata idan muka fara wasan yar tserenmu a cikin falo ta dora tabara tana bubuga kafa ta ce sai na goyata

Murmushi ya kara saki ya shiga zube mata kayan a cikin ledar

Gannin haka ya sakata dan zaro ido ta kara fadin" aman yaya kace na fito sai mu hadu kuma kace yanzu an kirayeka wajen aiki? Shikenan ba komai

Yi ta yi kamar ta kashe kiran ta dubi Elhajin

Hannayenta masu tsararun yatsotsi ta hade, bakinta ta kara zumburowa ta kyabe fuskarta ta ce" ka yi hakuri Elhaji ka ji? Ka ga dama a kafa na fito motana ta samu matsala na yi tunanin mu hadu da yayana ya maida ni gida idan ya biya kudin kayayakin nan , sai dai kash ka ji wai an kirayeshi aikin gagawa ka san likita bashi da lokacin kansama

Dan Allah ka yi hakuri Elhaj na bata maka lokaci da tsarin kayan nan

Har yana inda inda ya ce" aa aa, idan yayanmu bai siya ba ni kuwa aikin me nake? Idanma da karin wasu a kawo su nan Hajia ai ke din baba ce

Kikifta idannuwanta ta yi ta ce" ban fahimta ba Elhaj

Wayarsa ya dora saman table din yana dubanta yana murmushi ya ce" ki dora min numberki nake nufo yan mata sannan ki bar maganar wai kudin kaya bayan shagonku kika shigo

Murmushi ta yi a kasan zuciyarta tana ayanna zaka fada ne

Sai kuma ta dan zaro ido tana girgiza kai ta ce" aa aa, ka rufa min asiri idan na je da kayan nan na ce wa ya bani? Yayanmu baya bari bayan nan yaya daga shigowa dan fita da kaya haka? Aa ba zan iya amsar kayan nan ba gaskiya Elhaj

Kamar da wasa sai ga Elhaj na lalabar Najeeba cewa ta amshi kayan nan ba wani yawa kuma ai ita mace ce tana iya adana kayanta a dakinta

Da kyar ta yarda aman tana ta dafe gaban goshi irin ya takurata amsar nan

Cike da kulawa ya kara turo mata wayarsa ya ce" wanenen yayan nan namu mai sa'a a duniya da ya zama yayan wannan kyakyawar shagwababiyar budurwar?

Wayar tasa ta kala kirar samsung ce babar gaske sannan sabuwa ce dal sai walwalin sabunta take aman bata dauka ba ta lumshe idannuwanta tana masa murmushi ta ce" sunnansa Ibrahim Adam , likita ne a baban asibiti na kashi

Kansa ya ringa gyadawa cike da murnar jin hakan, nan take ya kuma tambayarta mahaifinmu fa?

Dubansa ta yi duba irin ja wai Allah? Ta tabata wannan mutumen ya girmi Abih, aman da yake irin abihn ne gashi sai kira yake mahaifinsu sannan Yaya DAYABU yayansu ko me? Oh duniya yanzu du wace ta dan yi masa shagwaba kennan sai ya fada ya karba da gudu gudu shi kuwa?

Sauka ta yi daga saman kujerar tana ganni yaronsa na jidar kayan yana fitarwa sannan tana gani ya saka kudi a leda guda irin kar ta gannin nan ta ki amsa

Byron dake ajiye ta dauka ta duka ta rubuta masa number kanninta Najeeb ta ajiye masa tana murmushi ta ce" na gode Elhaj

Shima murmushin ya yi da sauri ya saka takardar a aljihunsa har ya fara tunanin sauka da wuri yau dan ya je gida ya loda number ya yi kiranta
Gasgi bata fada masa sunnan mahaifinta ba, aman ba komai koma yar gidan waye zai sani kuma shi ba da wasa ya zo ba da girmansa ba zai tsaya bin layi da kannanun yara ba dan ya san wannan samarin na zamani sunna yiwa wannan yar cakwai din layi

Tana fitowa ta harhada kayan ta tsayar da dan adaidaita

Yaron ne ya ce" an ce a kaiki fa

Ta juya ta kalli wanda zai kaitan

Kanta ta girgiza masa kawai ta shiga adaidaita sahun nan

Direct sunnan shagonta ta fada masa sannan ta shiga lalubawa ta zaro kudin nan

Murmushi ya saki tana gannin masu aku biyu wato jaka ashirin cif sababi

Kanta ta gyada tana ayanna" yanzu haka baya fitar da zakah!

Dan sahu na ajiyeta ta bashi kudin nan , nan ya shiga neman cenji dan haka ta amsa ta shige ciki ta saka a kawo masa

Saloon din a cike take , sai aiki ake kuma a tsaftace take dan haka ta ji dadin hakan sosai

Kayan aikin ta bude ta shiga lolodawa abinta wajen kayan siyarwarta, a hankali ta furta" halal na ci

Zuwa ta yi ta zauna lokacin kuma karfe tara ta yi kuma a lokacin kiran ambasador ya shigo wayarta

Bata daga a kira na fari ba sai a na biyu

Zuwa lokacin ta amshi takardar tana duba wa'inda ke son kwaliya

Byro ta amsa ta shiga dangwala ok a kan wa'inda zata iya yiwa a cikin satin nan sannan tana dora lokaci

Sauraronsa take yana ta surutun dan me take bashi wahala ne

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce" ka san dai na yi missing dinka a lot ko?

Shima ajiyar zuciyar ya sauke yana jinta

Ta ce" ina saloon ka zo na ganka ka ji?
Chapter 18 · 0% Book details