← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 138

Sashe 40

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anmy ta sauke ajiyar zuciya tana dubansa kafin ta maida dubanta wajen yayanta, a hankali itama ta furta" burina, bai fi zumunci ya dore ba Allah ya ja da ran sarkin damagaram

Shaheed ya lumshe idannuwansa ya maida dubansa wajen Abih

Abih ya buda idannuwansa da sukai masa jajajir , a hankali ya furta" Allah ke bada girma, koda kuwa yaranmu sun zamo shuwagabaninmu mu masu biyaya ne, Allah ya kara datako Mai damagaram

Kuma lumshe idannuwansa ya yi sannan ya maida dubansa wajen DAYABU

Kansa ya sada , a hankali ya furta" na yi kuskure, baki daya ni na ja ragamar wanzuwar wannan fitina,Allah ya ja da rai daga yanzu daga kan DAYABU MUTALAB, har zuwa NUSAIBA MUTALAB bamu da wariya, Allah ya huci zuciyar sarkin garina

Da sauri Najeeba ta kankame NUSAIBA a hankali a jikinta sannan ta sakar mata dan murmushi tana shafa kitson kanta wanda tun wanda ta mata ne ba'a tsefe shi ba kusan sati uku a kan ko wankin kirki ba'a masa ba hakan ya sa ya tsufa duba da sunna da izgar gashi nan da nan gashi ke tohowa a kansu shi ya da du sati sauran ke yawan kunce kansu domin kitso ko saloon a gida ba wani wahala shi ya sa kawunnan nasu ke kara albarka

Murmushi ya yi wanda iya zuciyarsa ne sam bai bayanna a fili ba

A hankali ya kuma furta" Allah ya yi mana jagora

Baki dayansu suka amsa amen banda Najeeba dake kara buda bakin Nusaiba tana kallon hakoranta da suka yi dan duhu hakan na shaida mata bata wanke mata baki har gashi ya kama hakoran yar yarinyar

Shirun da ya dauki wajen ne ya sakata dago kanta dan gannin har ya gama maganar ne?
Idannuwansu ne suka sarke da na junna a lokacin da ya kusan karasowa inda take zaune , da sauri ta mayar da kanta kasa ta sada sakamakon faduwar da gabanta ya yi da kuma irin kallon tsanar da ta ga ya yi mata
A ranta kuwa fadi take" azalumi, ashe harfa fuska biyu ne da kai? Gaka yanzu ka gama maganar wa'azi da masalaha ni kuwa ka tsane ni? Ba damuwa, zaka gane ne dan yanda ka tsane ni ni naka fi ka tsanarka!

Sai da ya fice a fallon da kamar minti goma sannan du suka mike

Irin yanda ta karaso ta warci yarta ta juya buguzum buguzum ya saka baki daya suka zaro idannuwansu

Da sauri Abih ya daga kafarsa zai bita sai dai maganar da Anmih ta yi cewar" idan ka bita yaya zaka rarasheta ne ta maido y'ar?
Ya saka shi dawowa da sauri inda take tsaye da yarensa

Muryarsa har tana hadewa da junna ya ce" yanzu domin Allah Bilkissu ba zaki yi min adalci ba kema? Kema a yanzun ganni kike ni ke daure mata tana haka? Ko so kike na yanke igiyoyin da sukai saura a tsakaninmu ne na jara dauko wata? Ita watar idan na daukota kin san meye halayanta? Wani sabon zama ne za'a kara dorawa da y'ayana shin da me zata shigo?

DAYABU ya yatsina bakinsa yana girgiza kansa, lale ta samu damar da take tunanin har zata iya taka sawun kafarta ta fita da y'ar da sarki ya gama nasiha a kanta

Fitarta kawai suka ganni, hakan ya saka Zahrau kallon Anmy, sanyaya muryarta ta yi ta ce" Eyah, Anmy Najeeba ta fice da sauri Anmy

Anmy ta kallota da sauri, sai kuma ta kalli Ummulkhair ta ce" maza ku bita

Sai da suka fita ta kuma kallon DAYABU ta ce" wai Ummulkhair na tura ta bita, ko ta je ta tayata ba, bi min su ka maido min su ka ji?

Irin yanda take sauri ya yi daidai da Mardiya ta buda gaban motar Abih ta shiga kennan zata rufe ita kuwa ta karaso da wani irin mahaukacin sauri ta tare marfin kofar ta hannata rufewa

Hannunta daya ta saka ta finciko yarinyar ta direta kasa cen gefe sannan ta maida hannayenta ta finciko uwar waje

Da ihu ihu uwar ke fadin" ke baki da hankali ne? Ke wata irin karamar yar iska ce?

Dauke fuskarta ta yi da mari, ta maimaita mata wani sannan ta saka hannayenta ta hankadata jikin motar nan ta rike mata wuya
A masifance ta ce" ke wawuya ce Mardiya, kin so ki ci darajar uwa koda kuwa shekarunmu daya da ke, sai kika bata rawarki da tsale!
Tanas gaskiya kika fada babu wace ta zauna ta yi hakurin zama da shi har zuwa wannan lokacin kamar ke gashi yarki har zata ryfe shekara hudu nan da sati uku da kwana biyu,
Kin san me? Dalilin wannan ni kaina na so na ga mutuncinki, domin a duniya du macen da ta iya jure zaman waje domin y'ayanta nakan bata wani waje mai daraja a cikin mata wanda ba kowa nake ba shi ba
Sai dai ke din kin kasance wawuya a lokacin da kike anfani da kadarar wani ko dama da kika samu na zama matar MUTALAB kina taka mu son ranki!

Warto hijab dinta da Dayabu ya yi da murya a dan dage yana fadin" Najeeba me kike haka? Sakar mata hijab kin san da labari na iya iske sarki har yanzu a cikin gidansa kike fa kin manta a wajen ajiye mitoci kike

Fuzge hijab dinta ta yi, Ummulkhair kuwa na gefe rike da yar ta juyar da ita gefe guda tana dan jijigata har ta yi shiru daga kukan da take na rabota da su ta kwonta a kirjin Ummulkhair duda ita Najeeba take so ta dauketa aman ko a Ummulkhair din aka tsaya da dama domin mamanta ta cika duka da fada da zagi abu ga yaro inda ta fi jin dadi nan ta fi zuwa

Gannin sai kakari Mardiya take ya saka wannan karron ya fardota baki dayanta daga jikin Mardiyar da ta yiwa shakar mutuwa

Yana rike da ita tana tirjewa sai da ya matsar da ita gefe ya riketa a hannunsa da karfi karfi ya ce" zaki dawo hayacinki ko ba zaki dawo ba?

Wata tirjewar ta so yi ta hanyar kuma ridar Mardiya dake tsugune tana rike da wuyanta sai dai bai bata dama ba ta hanyar dauke fuskarta da marin da ya sakata saurin ja ta tsaya tana mai dafe kuncin nata da hannayenta bibiyu dan walahi bata son mari, kai ina dalili za'a maren mata fuska? Ita bata son mari ko kadan

Randa bace ya ce" ke baki isa na tankwasa ki bane ko ke idan ranki ya baci mahaukaciya kike zama?
Na fada maki ki daina, na maido ki da laluma , na nuna maki hanya sai tirje min kike kinai min tijara? Wani irin iskanci ne wannan? Sarki sa'ankine da zai tasheki daga magana yanzu yanzu ki fito ki aikata? Ke din banza ke din wofi?

Da kakausar murya ya ce" ki kiyayi haye a wajen da wargi bai samu wajen zama ba!

Yana gama fada ya hade su da Ummulkhair ya ha su da Nusaibar suka yi ciki

Tana nan tsugune har Abih ya karaso

Yana kallonta ya san an yi ba dadi da y'ayansa, gannin yannayin da take ciki ga kuma ba y'ar a tatare da ita

Shima da nasu da yake jira da ita dan haka a kausashe ya ce" tashi mu je

Mikewa ta yi ta je kusa da motar zata shiga

Waigowa ta yi ta kalli baban filin wajen
Zata nemi gannin sarki, zata labarta masa irin marin da Najeeba ta yi mata komai dadewa, sannan ta daukarwa kanta Alwashin yanda Najeeba ta kasance mai tara samari sai dai ta mutu a haka, domin kuwa ta rantse da Allah sai ta wulakanta rayuwarta
Ba ta taka dokar layar da aka saka masu ta kai hannunta kanta na biyu kennan ba ? Itama zata dawo daga zagon kasar ta bi ta hanyar kasa! Abih kuwa yanzu ta fara zama da shi bata ga ubanda zai rabata da mijinta ba, zumunci ne tsakanin mararsa kunyar y'ayansa da y'arta ta haramta!

Har yanzu hannunta dafe da kuncinta suka shigo Fallon Anmy

Sai da suka shigo ta ja ta tsaya sannan ta waiga dubanta kan yayanta wanda shima yake jin zafin marinta da ya yi

A hankali ta ce" yaya, aman ka san ba dadi marin fuska ko?

Yayanta ya ce" ke kuwa kika mari matar ubanki? Marar kunya?

Kanta ta sada sai ga hawaye masu zafi sun fara fita daga cikin idannuwanta a hankali ta kuma furta" yaya, ka ga irin rashin kunyar da ta aikata a gaban sarkin da kake cewa kar ni na yi ya ji labari? Yaya ka ga yanda take son rabamu da Nusaiba bayan ni ina sonta?

Hannunsa ya saka ya kama hannunta suka karasa ciki, a lokacin kuma Anmy ta fito daga dakin yan matan da ta kai ta shinfide tana kallonsu ta karaso

Zaunar da ita ya yi ya zauna , shima sanyaya muryarsa ya yi ya ce" koma me ta yi, baki ji abinda ya maimaira cewar shi shugaba shine wanda zai iya shanye komai ba? Najeeba ba dan bashi da zuciya ba
Sannan ke da ita idan nace da ke ba faya bane zaki fahimci bambancinku?
Ke kanwarsa ce, wace ya isa ya saka belt ya yi maki dukan tsiya koda kuwa babu rawani a kansa
Ita kuwa matar Abihnsa ce, wace koda da rawani a kansa zai iya daga mata kafa ya kawar da kai ya bita da nasiha yau da gobe har ta fahimta
Najeeba kamar yanda kika fada cewar tana anfani da damarta hakan ne,
Kwarai Mardiya ta taki sa'a a rayuwarmu, ta yi nasarar auren ubanmu dan haka uwa take a wajenmu koda kuwa bata dauki girman hakan ba
Chapter 40 · 0% Book details