← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 138

Sashe 41

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anmy ta yi murmushi a ranta kuwa tana mamakin irin yanda yaron ya kasance tamkar mahaifiya, zai hukunta kannen nasa ya kasa samun nutsuwa
Bambancinsa da mahaifiya daya ne, du irin karfin soyayar uwa tana iya cire kanta ta nuna maka laifinka ta kawar da kanta ta labe ta yi jinyar zuciyarta, aman shi sun gano lagonsa koda ya daga hannu a kansu shi ke dawowa ya zauna ya yi ta rarashi
Sarai ta ga anfanin hakan a yau, sannan ta gane dalilin da ya sa maganarsa take da karfin tasiri a wajensu
Shi din uba ne kuma uwa ne a wajen kannen nasa
Irin yanda yake shanye duka dominsu ya saka shi zamowa shugaba a cikinsu

Hannunsa ya kai wajen fuskar nata da take rike da wajen idannuwansa ya rintse kadan a hankali ya dubi Anmy ya ce" Anmy, ki yi hakuri ki yafe mata bin bayanta da ta yi ta aikawatar da fada a cikin gidan sarki, dan Allah ki yi hakuri

Murmushi ta yi masa tana gannin girman yaron a idannuwanta, ta tabata zai iya zama adali koda a cikin gidansa ne

Shima murmushin ya yi ya mike ya kara tsugunawa ya furta" Allah ya kara girma uwata

Anmy ta ji wani yamyam da wani dadi ya ratsa zuciyarta, a sanyaye ta furta" Allah ya yi maka albarka yarona

Hannun Najeeba ya kuma rikewa kadan kafin ya saketa ya juya ya nufi wajen Ummulkhair dake goye da Nusaiba

Tsayawa ya yi yana kallon yarinyar har ta yi baci
Murmushi ya yi ya dan duka ya mana mata kiss a goshinta sannan ya kalli Ummulkhair a hankali ya ce" Khairiya, kar ki bari khulsum ta yi kukan maganar da ta fada mata kin ji? Sannan kar ki yarda bacin ran mamanta ya saka khulsum tsanar Nusaiba

Ummulkhair ta gyada kanta itama tana rike da hannun yayan nata ta ce" yaya auntu Zahra na tare da ita a dakinmu, tama ce na goya Nusaiba idan ta yi baci a wajen khulsumbdin zata kwana

Kansa ya gyada yana mai jin nutsuwa ta shige shi, dan baya so laifin mahaifiyar yarinyar ya saka kannen nasa gannin bakinta

Yaya, wayar tawa fa?

Gaban goshinsa ya dafe ya ce" ke ba na manta ba, aman kin san meye yayarki ne tace ita zata siya shi yasa na manta zan tambayo maki ita yayane an siyan ne ko yaya?

Murmushi ta yi tana jin dadi a ranta, tap, idan aka ce auren yayansu ne bata san irin abinda zasu yi ba, fatansu Allah ya sa yanda yarinyar ke nuna masu kauna a waje har cikin gidan haka ne, Allah ya sa matar yayansu ta zamo uwa a garesu baki daya

Sai da ya kara shafa bayan yarinyar ya furta" kaita ki shinfideta ki yi mata adu'a sannan ki ajiye wani dan abin ci a kusa dan kar aje ko tana tashin tsakiyar dare neman abinci

Amsa masa ta yi ta nufi ciki

Kanta sade yake a kasa tana tsoron dagowa sakamakon irin kakausan kallon da Anmy ke binta da shi

A hankali ta furta" Anmy ki yi hakuri

Anmy ta yi dan murmushi ta ce" wani abin kikai min ne NAJEEBA Mutalab?

Najeeba ta kara sada kanta a hankali ta ce" Anmy, a gabanku fa take wannan rashin mutuncin

Anmy ta dan daga kafadunta ta ce" eh na gani, ke kuwa sai kika zaneta a bayan idannuwanmu aman a wajen da duniya zata iya gani ba, ai haka ne danka dama ka zane shi kawai

Najeeba ta kara sada kanta dan ta san yaufa tana hannu

A hankali ta budi bakinta zata yi magana Anmy ta ce" ai ban yarda cewar, bayan rashin kunya, rashin sannin ciwon kai, rashin kawar da kai yanzun harta da darajar kanki baki sani ba?

Da sauri ta ringa girgiza kanta ta ce" Anmy

Anmy ta ce" ki yi min shiru malama!
Idan ita ta nuna halayen tarbiyarta ta marar kunya da rashin sannin girman na gaba da ita da raini ke sai kika nuna taki tarbiyar wace kika gada ta masifa?

Kanta ta kara sadawa kasa
Anmy ta ce" ina sannin ciwon kai ga macen da zata yi anfani da karfin damatsunnanta ba dan ta yi ibada ba? Ina hankali ga macen da zata kai hannunta jikin wata da niyar zu gwada karfi bayan ta san wani abu na iya faruwa a wajen ko ita a ga tsiraicinta ko a ga na abokiyar fadan nata ta hanyar yage mata hijab ko zannin dake daure a jikinta ko rigarta haka kawai ta jazawa kansu abin kunya domin na tabata du wace ta san kanta zata ji kunyar a ga tsiraicin yar uwarta mace bale nata! Yaushe kika raina gida mai daraja irin gidan nan da zaki yi dambe a cikinsa bayan wanda bai san irin darajarsa bama ya kiyaye ya girmama shi bake ke da kike cikinsa kika san meye shi?
Yaushe kika raina haduwarki da yayanki wanda nake iya yina dan rufe izgilinki?
Ina kika zubar da class dinki da har zaki mike ki tarbi mutun da fada bayan kin san ance shiruma amsa ce ga mai hankali?

Allah ya huci zuciyarki....Najeeba ta fada tana kara sada kanta

Anmy ta dago dan yatsarta guda ta ce" zaki nutsu ko bakya so ne Najeeba Mutalab!
Tashi ki je dakinki ki yi nafila ki shirya yin baci

Sai da ta kara dukawa ta yi godiya tana kallon fuskar Anmy din da ata daure mata sannan ta shige ciki

Washe garima sun wuni ne sunna gyare gyaren fata, sai dia har zuwa lokacin ba wani sake masu baki dayansu Anmy ta yi ba, idannuwanta a kansu, tana ta daukan dukan abinda bai mata ba tana rubutawa a litafi da byro sannan tana dora question mark a sama, kan neman yanda zata biyo da su
Sai irin dabi'un da ta shiga koya masu na rayuwar gidan sarauta, wace da yawa sun iya sai dai kuma da yawa basu iya ba dole sai an zauna dan ba karamin aiki bane
Irin magana da ido, magana da kai, sasauta kallo ga sarki , irin kallon da zaka masa a cikin jama'a a matsayinsa na sarki, irin wanda zaka iya masa idan daga kai sai shi ne, irin yanda zaka ringa kiran sunnansa a waje da kuma idan dqga kai sai shi ne
Murmushi Najeeba ta yi tana lumshe ido da anmy ta furta" MAI GARINA, a daka kuwa tana iya yi masa special sunna kamar MAI NI

Bayan salolin su magariba da isha ta fito dauke da Nusaiba

Sai da ta duka har kasa ta ce" Anmy, ina son zuwa saloon na dauko abin kitsonta

Anmy ta dubeta, a hankali ta ce" ki dauki kys din motana, ku je ku dawo

Najeeba ta kara yin godiya ta dauki kys din

Tana cikin tuki mesage din Anmy ya shigo
Sai da ta tsaya a saloon ta dauko abubuwan bukatarta sannan ta dawo motar ta duba mesage din

*ki kula*

Murmushi ta yi tana kallon Nusaiba ta ce" wa ke son ice cream?

Ai kuwa Nusaiba ta ringa daga hannunta tana ihun ni ni ni

Daria ta yi ta karkata ta nufi wajen mai Ice cream

Siya ta yi sannan ta sayan masu kilishi ta nufi wajen hutunta dan bata son komawa yanzu yanzu

Tun da suka tsaya daga inda yake tsaye yana hangen motar gidansa mitar Anmynsa har suka fito ta fitar da darduma ta kawo wajen da take zama ta shinfida

Wayarta ta kunna wakar hausa ta breaker ta ajiye a gefe sannan ta zaunar da Nusaiba dake dan rawa rawa ta buda mata takardar naman tana kallonta ta ce " sai kin ci wannan sannan ki sha ice cream

Ai kuwa yarinyar ta maida hankalinta ta fara ci din domin ice cream din shi ta fi so a bata

Kara gyara tsayuwarsa ya yi ya dan matso kadan dan jin abinda suke fada

Ta dauka ta saka a bakinta tana dan taunawa sai kuma ta ja tsaki a hankali ta furta" idan ya san wa'azin zumunci ko ya san na zalinci?
Sai ta yatsina fuskarta ta mayar da muryarta tamkar tasa wato ta sanyayar da ita ainun ta furta" meye ilar gaba a musulunci?
Ta murguda bakinta a hankali ta furta" yana magana tamkar mace, yanzu haka sarautar samunsa dai ta yi aman sarki ai zaki ne!

Idannuwansa ya zaro da mamakin wai ashe wannan abin du shi ake yiwa?

Kansa ya girgiza a hankali ya karaso ya zagaya ya zauna yana masu salama

Tun da ta gansa sai ta hadiye na bakin nata da sauri sannan ta cire hannunta daga cikin takardar tana mai binsa da kallon mamaki

Hannunsa ya saka ya dauki naman nan duda yana tunanin da wahala ya iya ci domin a rayuwarsa baya son dabi'ar cin abu a titi sam bai iya ba bai saba ba ya daure ya kai bakinsa bayan ya yi bisimillah
Yana ayanna idan ba shaidaniya ba me zai hada ki da kunna waka da dare a wajen nan duda da haske da kuma mutane aman ai ka kiyaye kawai!

Ita kuwa hannun nasa ta bi da kallo irin yanda ya dan jujuya naman sannan ya saka a bakinsa
Da mamakin rashin yi mata salama, da haye mata darduma uwa uba ya kamo kanwarta ya rike a jikinsa sannan ya ci mata namanta take kallonsa

Dagowa ya yi ya kai hannunsa ya danna wajen kashe wakar sannan ya hada idannuwansa da ita
Ido daya ya kashe mata ya dage mata gira daya hakan ya saka ta yi gagawar cire dubanta a kansa tana furta" meye wannan kuma kamar wani dan iska kana kashewa mutun ido, ko dau a yar iska ya daukeni?
Shi bai san ko kawance bana yi da mace farar fata ba shine zai ringa damuna shi wani garjejen fari, yo farin mutun ai sangarta ta kare a wajen, kayan tsantsane kawai

Dubansa ta kuma yi ta ga yana son bude ice cream din, hakan ya saka Nusaiba yin dare dare a saman kafarsa har tana masa daria tana nuna masa

Kai yaro, yaro, bashi da hankali, ta fada a kasan zuciyarta
Chapter 41 · 0% Book details