← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 138

Sashe 49

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunsa ya saka ya rufe bakin Ummukulsum sannan ya ringa bin Najeeba da kallo wace ta zama uwa wata wada ke son tashi sai tsale take tana kai kawo sai kuma ta tsaya tana kallonsa gashi kanta baki daya ta balbaza shi hannunsa ya saka ya jata kasa da karfi hakan ya sa ta yi wani irin zama dabar a gabansa gabanta na yi mata wani irin tsalen albarka kamar zai bale ya fito daga kirjinta

Wayarsa ya dauko ya shiga galeri
Hoto ya fitar saman wayar tasa ya mika masu

Har rige rigen amsar wayar suke suka tsurawa hoton ido

Yannayinsa a kansu ya ce" sunnanta *HUWAILA* , sati daya ne tsakaninku ita da Najeeba,
Tana nan garin zaune gidan kannin mahaifinta tana karatu a lycee

Du da iein tarin kamanin da take kamar an tsaga kara ita da su bai hanna Najeeba cewa " yar gidan waye? Me hadinmu da ita mu kuwa?

Murmushin takaici ya yi yana kallonta ya ce" NAJEEBA MUTALAB idannuwanki sun samu matsala ne? Wannan da kike ganni yar gidan MUTALAB ce, jinnin MUTALAB ce wace ya samu a zamanin da baya jin magana!

Kamar ya kuma dima masu guduma haka suka kasance du sunna kallonsa
Sai cen Najeeba ta yi ihu tana zazaro ido a firgice ta ce" lalle akoy tashin hankali a gabana, ina tare da wannan lamari a tsatsona nake tata rashin mutunci a garin damaram? Ashe nima da nama lamarin a boye a tare da ni ban sani ba? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une

Ummulkhair ta ringa share hawayenta tana jan hanci ta ce" ko shine abinda yake saka matarsa yi mana wata magana cewar y'ayan yan iska?

Ummukulsum ta yi murmushi, ita abin sai take ganninsa wani iri, ashe ba mahaifiyarta kadai ce ke tare da wani mugun lamarin rayuwa ba?

DAYABU ya sasauta muryarsa ya ce" ku zauna

Irin yanda ya yi maganar ya nuna masu gabansa ya saka suka zazauna sunna kallonsa

A sanyaye ya ce" a kadan zai kai shekara shida da na san da yarinyar nan
Na bibiyi rayuwarta da ta mahaifiyarta har na samu cikaken bayani a bakin kannin mahaifinta wanda ke rikonta
Ya ki amsar yarinyar a bayane ya amsheta a boye ne
Komai nata shi ke mata , karatunta bukatunta aman kuma hakan na nufin kar ta yarda ta fitar da ko waye mahaifinta a garin nan,
Ban san nufinsa na yin hakan ba,
Yana yi ne dan ya boye sirinsa saboda idan sirrin nasa ya fita zai shafi y'ayansa, mutuncinsa ko yana yi ne dan son ransa??
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" abinda na sani shine kasata kasar hausa ce, mai dauke da al'umar da idan irin haka ta faru yakan zama matsala, yakan shafi y'ayan mutun, abin ya zama na gori, idan mata ne ka ga har ana gudun aurensu bayan ba su suka aikata ba kuma shi kansa wanda ya aikatan na tabata da ya san abinda zai je ya dawo da ya hanna kansa aikatawar

Kamar yanda na fada maku, ni DAYABU MUTALAB, na baku umarnin fitar da mijin aure kwana kusa ba nesa ba!
Sannan Abinda aka yanke shine.....Anmy ta roki Mai martaba alfarmar hadaku da masu tsaro sakamakon abinda ke faruwa a cikin gidan wanda yake cikin bincikensa
Ya zama dole ku dawo nan da zama sanadiyar abinda ya faru da Ummu, ta rantse ba zaku bi Abih gida ba shima kuma sai bai ja ba na tabata yana tsoron kadaicewarsa da mu yana gudun tambayoyinmu hakan ya sa aka dora dokoki a kan shiga da fitarku baki dayanku
Zaku ringa zuwa wajen neman iliminku a kan lokaci ku dawo a kan lokaci
Zaki bude saloon dinki wajen karfe goma na safe ki rufe goma na dare ku dawo gida tare da masu tsaronki

Tap.....shine abinda Najeeba ta fada a zuciyarta kennan, masu tsarona? Ana nufin za'a hada ni da wasu langayayun dogarai su ringa bina ko police? Ta yaya zan samu mijin na ware da wasu karti a bayana? Hala ba zan ringa zuwa wajen hutuna ba?

To yaya, zance fa? Ka san da dole sai mun ba wanda ke neman aurenmu dama zamu iya aminta da shi ko?

Idannuwansa ya zaro ya ce" Ummulkhair, ni da ni aka bi ba zaku yi wani zance ba! Sai Anmy ta kuma rokar cewa kuna iya baiwa mutun dama ya zo nan, ku gana da yama ya koma inda ya fito a falon da mai martaba ke saukar baki

Da sauri Najeeba ta ce" kana nufin falin da yana iya ganninmu sannan ya ji du abinda zamu tatauna da saurayin yaya?

NAJEEBA ko baki da gaskiya ne? Ya tambayeta yana mai kallonta da son jin amsa

Kanta ta ringa girgizawa ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, wani irin zance zata yi ita kuwa bayan ta san wannan mutumen da ya tsaneta na iya ganninta yana jin abinda zata fada?
Sai kuma wani abu da ya diro mata shine yayan banki! Yanzu idan aka ce ta zauna da saurayi daya ana nufin nauyin aljihunta zai rage?

Aby daya da ta sani shine lale lale zata samo mijin aure, zata tsayar da daya kwalin kwal wanda zai zama mijin Najeeba

Bai bar dakin ba sai da ya kara kwontar masu da hankali, shi kansa ya samu hankalinsa ya kwonta da damuwar da yar uwarsa ta tsinci kanta a ciki kafin ya mike ya fice a tankamemen dakin nasu

Su duka sun yi shiru ne a kwonce, a hankali Najeeba ta lalubo wayarta ta turawa Zahrau message kamar haka" me kike ?

Zahrau dake zaune kunyar Mai gidan nata na neman kasheta sai hira yake mata yana kara son ta saki jikinta ita kuwa tarin kunyarsa ta lulubeta da tsoron yannayin kusancin da suke ciki ya hanna mata daukan wayarma bale ta ga message din hakan ua sa Njaeeba ta fita a wajen Zahrau ta shiga contact dinta ta ringa bi daya bayan daya sunnayen samarinta tana kallo tana tuna yannayin mutun da halayensa da komai da komai

Zaune yake bayan ya fito daga bangaren Zinaria wace ya taka yau da kansa ya kai mata ziyara dan gannin yaya yannayin jikinta yake? Ciki dai ya lalace domin bai kai lokacin haihuwarsa ba a dole aka fitar da shi akai mata wankin mahaifarta hakan ya sa take kwonce cikin damuwa da tsoron daga wayar mahaifiyarta
Ko da ya je ganninta ta yi mamakin ganninsa a bangarenta sai dai bata iya bashi wata kulawa ba har ya bar wajen dan hankalinta bama a jikinta yake ba

Sosai yake jin ba dadi na lalacewar cikin jikinta, sai dai ya dauki dangana ya barawa Allah tare da fatan samun wasu masu albarka masu zama

Alkyabar jikinsa ya saka hannunsa a hankali zai cire,
Da sauri ya dakata sakamakon wani abu da ya fado masa a rai

Idannuwansa ya daga ya kai dubansa kan agogon dakin.........................

Da sauri ya mike tsaye yana sauke Alkyabar kasa ya shiga taka kyawawan kafafuwansa saman lalausan cafet din wajen ya nufi wajen kujerar dake ajiye

Zama ya yi ya dora kafarsa daya kan daya ya shiga warware rawanin dake kansa

Sai da ya warwareshi tas sannan ya kuma tsurawa waje daya ido
A cikin ransa ya shiga ayanna : *IDAN FA BA BINTU AKA ZO KASHEWA BA, NI AKA ZO KASHEWA?*

Ba zai manta ba, ana zaune a dakin karatu a lokacin da aka gama daurin aure du kawunansu a sade sai ya so yin raha da su, domin mutanen dake wajen daga amintatunsa, sai iyayensa wa'inda suke tsofafi da datijai ne

Ba zai manta kalmar da ya fada ba, wace ya ce" *NI ZAN JE DAUKO FADIMA BINTU*
Ya fadi kalmar ne dan ya saka su sakin raha, sai dai maganar ta so ta bada armashi a lokacin da mahaifin Bintun ke godiya cike da farin cikin jin shi da kansa zai je daukota

An rarage mutanen dake ciki sai ya kasance saura mutun shida

Amintacen bafadensa ne ya kuma tambayar maganar cewa" ALLAH YA KARA MAKA LAFIA, SHIN A WACE MOTA ZAMU JE DAUKO GIMBIYAR?

Ba zai manta amsarsa da ya bada a bayane ta hanyar fadin : Sabuwar motar nan a ita zamu je dauko gimbiya.........................ya katashe yana mai sakin murmushi mai dan sautin da ya saka du mutanen wajen suma sakin murmushin sunna jinjina maganar cewa wai da gaske zai je ne da kansa?

Da sauri ya mika hannayensa ya janyo farar takarda da byro ya dora sama

Sunnayen mutanen dake wajen ya shiga rubutawa daya bayan daya
Sai da ya gama rubutawar aman bai saka na amintacensa ba

Bin sunnayen ya shiga yi da kallo
Idan akoy abinda rayuwa ta koya masa shine jiran komai daga kowa
........ya jima yana wannan tunanin har ya ga dare na tsalawa

A kan sunayen ya ringa dora number tun daga 1 har na karshe kafin ya mike ya nufi bed dinsa dan samun hutu komai kankantarsa domun rabonsa da ya huta har ya manta tun ihun fitinaniyar yarinyar nan

Wata irin mika ya yi a saman bed din , bukatar kebewa da mace yake, hakan ya saka baki dsya jikinsa ya mutu wata irin kasala ta dirar masa

Tsintar kansa ya yi da kiyasta irin abinda ya dace da damkarsa
Da sauri ya rintse idannuwansa sakamakon hotunnan da suka shigo zuciyarsa
Korar shedan ya ringa yi ido rufe dan samun nutsuwa kafin ya mayar da kansa ya kara dannawa a saman fillow din yana jin yanda bugun zuciyarsa ya cenza
Dolema ya auro uku ya jera!
Daga bakin lokacin da ya fahimci cewa daya ba zata iya da shi ba ya san cewar sai ya kawo, zai karo uki ne a kwana kusa ko dan ya ringa zagaye su
A cikinsu ya tabata ba zai rasa wace ta dace da bukatar zuciyarsa ba!

..........................................

Aiki take da kanta yau, tana kitsa gashin wata bafulatanar mata mai son gyaran kanta, ana yi mata kitso kananu masu kyan gaske

Idan tana kitso a tsaye take yinsa wanda take yiwa kuwa sai ta hau kujerar saloon sunna yi tana kallon abinta
Chapter 49 · 0% Book details