← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 138

Sashe 138

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tana gama mikewa ta ringa takawa da kafafuwanta dake dauke da farar safa kal kal da alkyabarta har ta karasa gabansa
Sakamakon ya darata a tsaye sai ta dago dubanta tana kallon idannuwan nasa
Gannin a yau yan sarautar aka tashi da su, ga shara'a ta samu a irin wannan lokacin sai ta saka hannayenta a hankaki ta dan ja rawanin nasa kasa kadan ya kasance lebunansa a waje sannan da girarta ta yi masa tambayar menene?

Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya dora hannunta na dama daifai kahon zuciyarsa sannan saman labansa ya furta" *KISHINKI NAKE, SON KI NAKE, ND I NEED U A SAMAN GADONA* "

Murmushi ta sakar masa mai tsada kafin ta dube shi da kyau itama a kan lebenta ta ce" *BURINA NA DAWAMA A CIKIN JIKIN KA, ZAN JE NA YI JURANKA HAR ALLAH YA KAWO MIN KAI....* hannunsa ta ja ta dora a wajen mararta ta dan shafa ta kara tsura masa ido ta ce" *Marata a shirye take da daukan ajiyarka ko da kuwa mace na iya dauka sau billion a rayuwa.......zan amshi ruwa daga mai dauke da ruwa, zan baka hardar karatun da kake koya min fila fila KHALB* "

Har ga Allah sai kawai ya ji jikinsa ya fara bari bari, yana kallonta kamar wani wawa har ta shige ta kofar da ya biyo

Ji ya yi tsayuwa na neman gagararsa, da duba ya ringa bin jama'ar dake wajen du kawunnansu a kasa

Wani yawu mai santsi ya hadiye ya ja ya mayar da rawanin har wajen bakinsa

Muryarsa na crakin ya kai dubansa wajen Yarima ya dan limshe idannuwansa a kasam zuciyarsa kuwa fadi yake 'Ina, koda na ce zan gabatar da shara'ar nan ba zai yiwu ba, ta lalata komai ta tsatar da komai sannan ta tafi da komai', sai kawai ya dan kara gyara tsayuwarsa ya ce" *YARIMAH ABDUL JABAR, KA GABATAR DA SHARA'A WA AHALIN GIDAN SHAHEED ALIYU DA MUTALAB NA BAKA WUKA NA BAKA NAMA*

Yana gama fada ya juya da dan hanzari ya shige ta hanyar nan,

Ai kau ta dan dage alkyabar dake jikinta ta juya da niyar kwasawa da gudu tana daria dama ta dan tsaya ne dan ta ga shin zai zo ko sai ta yi jiran nasa?

Shima dariar ce ta kubce masa ya shiga warware rawanin kansa ya kara hanzari dan cin mata domin kuwa shi Suktan Shaheed ya jima da gane cewa ifan yana daka shi din sunnansa Shaheed khalb din BEEBAH, sarauta na hannun *NAJEEBA MUTALAB*

ALHAMDULILAH

ALHAMDULILAH

ALHAMDULILAH

Allah yaa nuna min kamalawar wannan labari nawa mai sunna MAGE, Mage kirkiraren labari ne, idan har ya yi shige da rayuwarki/ka an ci sa'a ne, dan haka a gafartawa yar mutan Niger

Ya Allah ina rokonka da sunnayenka tsakaka ka yafe min kuraran dake cikin wannan labari da wa'inda na yi a baya da wa'inda nake tunanin yi idan har da raina, ya Allah ka bani ikon rubuta alkhairi da yan yatsunna ka hane ni lalata tarbiyata ,
Ya Allah ka jikan iyayenmu ka sa mu cika da kyau da imani

Sakon gaisuwa

*Zuwa gare ku daukacin al'umar da sukan nunan kulawa, soyaya, a aikace da aljihunsu a kan wannan sako more specially Mage grup fans, ku din nawa ne, nima taku ce, ina mai baku albishirin cewa in sha Allahu zan dawo da sababi har kwaya uku, da ba dan daukan sunna ba da na furta maku sunnayensu, sai dai ina mai rokon ku da ku kasance tare da ni bayan azumi idan Allah ya nufemu da gannin lokacin, ku ci gaba da bani kwarin gwuiwa da hadin kai dan kuwa na fada da karfin murya cewa ni dai ina rubutu ne domin ku, idan ba ku ba ni, Allah ya yi maku albarka, ya kara lafia, ya kara imani, ya kara arziki mai anfani, ya sa a gama da duniya lafia*

Jinjinar ban girma

*JINJINAR BAN GIRMA ZUWA GARE KU YAN UWANA, TAURARI WRITER MA YAR UWATA SAMIRA HARUN, MA Y'ATA RAHIMA, MA KANWATA NAZIFA, MA KAWATA HALISA WATO LISSA AND MA NUSEE, ALLAH YA BARMU TARE, YA KARA DANKON ZUMUNCI YA KIYAYE MIN KU AMEN*

Alfaharina

A duniyar yanar gizo ina alfahari da Allah ya hada ni da masoya, har suka kasance yan uwana

*BILKISSU KANAR, ND SAMIRA HARUN* Zan iya dukan mai yi maku cune da baki Allah wallahi😁

Daaukaci

DAUKACIN marurubuta na gaishe ku, na kuma gaishe ku, inai maku fatan alkhairi

Sako zuwa ga jama'a

MAGE ba na siyarwa bane, kyauta ne, idan kika biya kudi wani kato ya siyar maki kin yi kyauta ne😁

Dan ALLAH du wanda na batawa a wannan labari ya yafe min, domin mutun nake dan adam ban fi kowa ba ban isa na kamo kowa ba👏👏👏👏😁😊😁

*Alhamdulilah SAJIDA CE YAR MUTAN NIGER*
Chapter 138 · 0% Book details