← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 138

Sashe 22

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya sanyaya muryarsa sosai sannan ya ce" da me kike jiran ganni bayan kin ce zaki amshi abubuwan hannayensu?
NAJEEBA ke baki yarda sun san gidanku ba, wanda ya san gidanku ya tabata mai naci ne ya kai kansa gidanku
Najeeba ke baki yarda sun san kina da mahaifi tsayaye da kuma yayan da zasu ringa shaku ba
Najeeba, kin mayar da aljihunsu wajen wasanki , kin kware wajen iya juya tunaninsu su fitar da dukiyarsu su kashe maki

Dubanta ya yi ya ce" me kike jira? Me zasu so su kuwa a wajenki? Bayan sun san ba su kadai bane, sun kwana da sannin basa layin wa'inda zaki aura
Me zai hanna su yi tunanin iskancin kike so bara su nuna maki ba?

Kansa ya sada gannin ta kure shi da ido kuma harga Allah du ta fi su magana ga shegen karfi da idannuwanta ke gare su

A hankali ya ce" kin san wani namijin na nuna irin haka dan ya gane shin matar ya kilace ce ko matar a watse ce?

Wanin kuwa da kika gansa dama dan a watse din ne
NAJEEBA, shi irin haka a haka ake rasa na kirkin
Tsorona a haka na kirkin ya sulube maki ke kanki baki ankara

Hannunta ya kamo ya dago yana dubanta ya ce" idan kika kare mutuncin kanki, kon kare mutuncinki ne a farko, kin kare na y'ayanki, sannan kin kare namu
NAJEEBA, kin fito daga tsatson da ya yo sunna, Allah ya daukaka
Abu kankani ake jira karamin abu ya zaga gari
Shi yasa nake maku nasiha cewa ku kama kanku ku rike mutuncin kanku

NAJEEBA ta lumshe idannuwanta a hankali ta ce" ya, kai ka san ni ba yar iska bace ko?

Kansa ya daga yana dubanta
A hankali ta dantse lebenta na kasa tana jin ciwon abin a kasan zuciyarta
Dan kawai na so abin aljihunsu sai su so jikina?
Ta tambayi kanta da kanta
Sai ta girgiza kanta tana mai bawa kanta amsar cewa" da ya kare aikatuwa a duniya, da na gile shi da hakorina na kashe shege! Kudinka sai na ci idan har kana iya saki aman fa ba zaka zo ajiyata ba karya ne!

Hannun yayan nata ta kamo ta ce" zaka raka ni wajen Anmy? Kar ta min fada

Murmushi ya yi ya bude motar suka fita

Sunna tafe tana tsara irin abinda zata yiwa Ambasador, sai na ci ubansa na rantse! A haka har ta dauki alkyabarta da ta ajiye ta dora ta kara gyarawa suka nufi ciki

...........................................
Karfe biyu na dare

Alkyabarsa yake cirewa a hankali
Sai da ya cireta sannan ya shiga warware rawanin kansa

A hankali ya gama warwarewa sannan ya kama babar rigar ya sauketa

Sai wata riga dake ciki baka ta kama jikinsa sosai sai wandon shadar dake kasan rigar

Mikewa ta yi tana karasawa inda yake tsaye ya baiwa wajenta baya

Sai da ta dawo gabansa ta daga kanta tana kallon fuskarsa

A hankali ta kai hannunta wajen sajen fuskarsa ta dora
A hankali ta shafa tana kallon yanda idannuwansa ke lumshe

Hannunta ta saka ta shiga kokarin cire masa rigar sai dai tsayinsa ya saka sai dadafe take ta kasa cirewar

Dan murmushi ya sakar mata ya tayata ta hanyar rage tsayinsa

Rigar ta cire masa sannan ta kai wajen hancinta tana sinsinawa tare da lumshe idannuwanta

A haka har ta kai hancinta wajen bakon turaran da ta ji a hancinta

A hankali ta kara rintse idannuwanta jin yannayin kanshin Princsss a jikin rigar

Tana kallonsa ya shige bayi ita kuwa ta zauna saman lafiyaye tatausan bed dinsa da rigar a hannunta jikinta a mace ranta a bace hankalinta a tashe

Ya jima sosai a bayin kafin ya fito yana tsane ruwan wankan da ya yi

Turarensa yake shafawa yana hangenta ta madubin dake gabansa
Ya so ya yi nafila, sai fai gannin ta zo harka tana zaune har warhaka ya saka shi karasa kimtsa kansa ya saka kayan baci riga da wando mai dogon hannu sannan ya karasa saman bed din

Hawa ya yi ya kwonta yana kallon sama

A hankali ta karasa ta haye saman kansa ta dora kanta saman kirjinsa
Kamar wace take fada ta sada kanta sosai ta ce" Allah ya ja zamanin sarkina, Allah ya karawa mai martaba lafia da jisan kwana, Allah ya tsare mulkinka mai gidana

Idannuwansa kawai ya lumshe, bai san yaya aka yi yake jin kalaman nan a waje sannan ya ji su a dakansa ba, yana son jin wasu kalar kalamai na kulawa ba irin wadinnan ba masu zafi yake son ji wasu kala daban aman sai ya fita waje ya ji kirari ya dawo daka ya kebance da macen da ta fi kowa sannin sirin jikinsa wace suka rigaya suka zama daya itama sai ta bi shi da kirari

Hannayenta ta kai ta kashe wutar dakin, yar karamar dake gefen bedma ta saka hannunta ta kashe

Sannin cewa bai taba mu'amalantar mu'amala da ita da haske ba ya saka ita da kanta ke kashewa a irin wannan lokacin, kwarai ta fi kowa kiyasta sanninsa domin ba idannuwanta suke gane mata ba, jikinta ke daidaita mata irin girmansa

Idannuwansa ya lumshe yana jin kwarai yana da bukatar hakan,
A hankali ta shiga zamewa ta kwonta sannan ta janyo hannunsa tana sauraron kulawarsa
Ta kasance a kulun sai dai ta yi kwonce abinta shi kuwa ya bada kokarin komai

Hannunsa ya kai jikinta a hankali, sai dai ya ji laushin riga a hannunta
Rigar ya amsa ya ajiye gefe kafin ya shiga kokarin gannin sun samu nutsuwa baki dayansu

Ta fi so su yi ta romance, ta fi ganewa hakan ,
Tana samun hakan, mai sakata samun nutsuwa kuwa sai dai sam gogan nata shi baya samun nutsuwa a iya hakan

Sai da ta kankame jikinta cike da tsoro jin zai kai gareta

Hakan ya saka shi sasauta mata rikon da ya yi mata a hankali ya ce" ki saki jikin ki dan samun gamsuwa cikin salama

Ajiyar zuciya take ta saukewa tana son sakin jikin nata sai dai ta rigaya ta saka tsoronsa da tsoron abin a kasan zuciyarta hakan ke bata wahala matuka

Ta gurzu sosai dan sai da ta biya kwanakin nan kafin ya saurara mata

Bai koma saman bed din da dauda ba sai ya nufi bayi

Sai da ya tsaftace kansa sosai sannan ya fito ya dawo ya tarar ta cenza zannin gadon kamar yanda ya gindaya mata

Sai da ta gama ta dauke wancen zannin ta nade shi sosai ta mike bayan ta mayar da kayanta jikinta

Rigar dake ajiye ta karasa ta dora hannunta zata dauka
Sai dai bata kai ga dauka ba ya saka hannunsa ya rike rigar hakan ya sa ta sakar masa ta kara sada kanta tana dan murmushi ta ce " ka huta lafiya sarkina, Allah ya hutar da gajiyarka uban y'ayana

Cike da kasaita ya sakar mata murmushi yana kallonta ta juya ta fice

Me yasa bata iya zama a bangarensa komai dare bata iya kwonciya saman gadonsa sai dai ta je falo ta kwonta?

Kafadunsa ya daga yana baiwa kansa amsa cewa bata da ra'ayin hakan ne

Rigar d aya lura ta yi ta sinsinnawa da nishadi sai dai daga baya fuskarta ta cenza ya kai wajen hancinsa yana mai sinsinawa

Da sauri ya maida baya baya kusan ciki inda idan ya saka zata kawo masa daidai cikinsa ya shinshina

Da sauro ya cire daga hancinsa yana mai dafe gaban goshinsa
Kanshin turaranta ne wannan
Wani irin turare take anfani da shi mai kamshi mai tsayawa a jikin mutun haka?

Bakinsa ya tabe yana ayanna" idan har kere na yawo.....zabo na yawo na tabata wata rana zasu hade........................

Tun da sasafe suke kinkimtsawa

Sai da suka gama kimtsawa suka hadu a saman tafkeken table din wajen du suka zazauna

Cike da farin ciki ta shiga zuzuba masu abinci da kanta tana yi tana dubansu
Inama ace su dawama da ita haka? Gashi yau har zasu koma gidajensu inama ace mahaifinsu ya iya bata koda matan ne ya rike mazan?

Abincinsu suka ci cikin nutsuwa kafin ta dauko ambulope din nan ta budeta

Abubuwan ciki ta zubo wanda hakan ya saka su baki daya zazaro idannuwansu ciki kuwa harda GIMBIYA

Da sauro ta dauki farar takardar dake ajiye ta buda, a fili ta karanta" *ina rokon alfarmar daga yanzu du wata dawainiyar gimbiyata ta dawo hannuna, idan nace kowace ina nufin kowace ciki kuwa harda kudin kari da kati.....fatan zaki rike wannan catin na banki sannan ki faranta min ta hanyar anfani da shi a kowani lokaci daga ni mai ke in sha Allah*

Wani ihu ihu yan matan suka kwasa sunna dariya, NAJEEBA dake firfito ido ta daga hannayenta duka biyu tana sarawa ZAHRAU ta ce" *AN BASHI DAMA, AN YARDA*

Zahrau kam kanta ta sada da mamakin kalaman ciki, dama zai iya neman wata dama a wajenta maimakun ya bata umarni?

Ashe sarakai na neman dama maimakun su bada umarni ko dai shine mai saukin kai?
Irin kallon da ya ringa yi mata jiya ta tuna hakan ya sakata saurin kara sada kanta tana murmushi kafin ta sauke dubanta saman makudan kudadan da suka zubo wai na karinta ne da kuma katin da yar agogon azurfa kamar dai soyayar yara masu ji da kansu

Kanennta ta bi da kallo tana gannin yanda suke shoki
Sannan ta sauke dubanta saman Anmy

Ganni ta yi Anmy harda su tagumi tana kallon NAJEEBA wace ke murmushi tana kada kai tana hangota ta zama aunty

Anmy ta dubi kananun ta ce" ku tashi ku je falo

Bayan sun bar wajen Anmy ta dubeta cikin nutsuwa ta ce" bana so ki amince masa dan dukiya daughter
Na fi so ki ji kin amince masa duda kin ga ba yaro karami bane da zai zauna yana soyaya irin naku na yara, sannan ba zaman jiranki zai yi ba duba da irin darajarsa
Aman ko da wasa ba zan yi maki auren dole ba kin ji?

Kanta ta ringa gyadawa a hankali sannan anmy ta dubi su NAJEEBA

Murmushi ta yi masu ta ce" kar ku manta, ku ringa kiyaye darajarku ku rike mutuncinku kun ji?
Chapter 22 · 0% Book details