← Book details Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 138

Sashe 92

Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahrau ta yi murmushi ta dukar da kanta ta bata damara tsagawa sannan ta kuma daukan wani kitson
A sanyaye ta furta" me kika ji a zuciyarki a lokacin da kika ga wata fuskar a matsayin matarsa bale Nadiarki? Yaya kika ji da ya furta maki baya son bak'a?"

A hankali saurin kitsonta ya ringa ragewa sakamakon irin zafin da ta ji ya ringa dawo mata sannu a hankali,
Tabas ta ji wani irin zafi mai girman gaske, faduwar gaba, da jin an gama wulakantata

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin irin yanda idannuwanta suka cika da kwallah, a hankali ta furta " *RAINA YA BACI SOSAI*

wani murmushin Zahrau ta yi a bayane ta kuma aiko mata da wata tambayar da ta sakata tsayar da kitson harma ta kurawa wajen da ta tsaga da tsirarun gashin kan na Zahrau ido,

ZAHRAU ta dago kanta tana kallonta ta ce" Tall me an mata, zaki iya beman sakin ki ne a hannun Ammi, ki fito ki yi zawarcinki, ki samu bakin mutumen da kike hasashe ya aureki a matsayinki na bazawara ku je ku samu irin rayuwar da kike tsarawa kanki ki barawa NADIA da ZINARIYA mijinsu?"

*MIJIN SU?*
Abinda ya fi tsaye mata a kasan zuciyarta, 'aman a kan me Aunty zata ringa yi mata irin wannan? Dan ta tayar mata da hankali ne ta sakata kuka ko dan ta birkita mata lisafi ne? Mijinsu? Ita har ya saketan ne da aunty zata kirayi namijin da ya gama karbar du wani tanadinta ya kare amshe du wani guzurinta sannan ya shiryata kafin ya sakata a jikinsa ya bata rungumar da ya kusan minti biyar a tsaye da ita a hakan ya furta mata kalmomi kamar haka :Ki kula da kanki, ki tsaftace harshen ki, Allah ya sa ki wuni lafia....: ya karashe yana mai kara matseta a jikinsa wanda tuna hakan da ta yi sai da ta ji wani irin yarrrrt a jikinta na ba gaira babu sabar

Du tunanin nan da take, sam bata san har Zahrau ta janye kanta tana kallonta ba
Kwalar da ta cika mata ido ce ta samu damar zubowa a hankali saman fuskarta

Zama ta yi kusa da ita hakan ya ankarar da ita

Dumin da ta ji a fuskarta ta laluba cike da mamaki tana kallon lema lemar da ta lalubo
Zahrau ta harde hannayenta ta ce " zan fada maki gaskiya, kin taki sa'ar samun miji haka mai tsada bayan kina zaune a waje daya, a gaskiyar magana a irin wannan zamani koda kuwa da gasken baya son bak'ar fatar ba zan ga laifinsa ba, domin kuwa yanzu zamani ya zo da wani irin kida wanda ya saka mata hawa suka cenza salon takun kidan
Ba komai bane sai irin yanda yawancin maza suka fi son farar fata kan bak'a,
Zaki ji namiji ya furta shi fa farar ko maya ce, ko mahaukaciya ce yana so, koda bata da nasaba!, hakan ya bada gudunmuwa sosai wajen shafe shafen yan matan zamani, Najeeba, ke shaida ce irin yanda kawarki burinta ta taba magana da shi, sai kawai Allah ya malaka mata shi,
Wa'inda basu kaishi bama daraja sun samu ana wawarsu bale shi? Ki cire masa rawanin ki ajiye shi ba ko sisi na tabata jinnin Ammi da mai martaba zai kawatu a idannuwan da zasu furta: ko bashida ko sisi sunna so!"

Hannun Najeeba ta kamo ta rike a nata ta ce" zaki iya zama da shi?"

Najeeba ta kasa budar bakinta, du kuwa da irin yanda take son yin magana, sai ya mata nauyi na gaske

Zahrau ta ce" zaki amshi abinki cikin ruwan sanyi! Bakya son sa? Ai kin fahimci an wuce wajen so ko? Baya son ki? Zamu jaraba mu ganni......, matansa? Zasu yi yaki ne dominsa, kema kuma zaki yaki abinki .......kowa salonsa ya fishe shi"

Najeeba ta kifta idonta a sanyaye ta furta" bana son hada bawa da wata, ban taba tunanin kasancewata a gareshi ba, lalle Allah shi ke da byro da takardar bawansa"

"Hakkun, kuma a yi masa biyaya koda ba'a so a hakan za'a samu rabauta" Zahrau ta karasa fada

Da sauri Najeeba ta kamo hannunta tana kallonta, a sanyaye ta furta" ta ina zan fara? Ta ina zan iya wannan yakin? Aminiyata da kuma ZINARIA, wa ya fi so cikinsu? ta yaya zai dubi bak'ar fata bayan ga farare nan a gabansa?"

Zahrau ta yi yar daria tana jin sanyi a ranta, sannan a lokacin ta ga tsantsar yarintar NAJEEBA, wai ita nan ta yarda da kalamansa cewar ya tsani bak'ar fata? Sai ta tsinci kanta da kuma yin yar daria, tun a yau zata fara gwadawa, ita kanta ta fi so mijinta ya dawo da kansa su koma dan kawai ta maidawa Gimbiya maganar da ta yi cewar ya halarci auren nan dan zumuncin dake tsakaninsu na sarauta ba wai dan zai kara aure ba, bayan auren kuma ta furta mata lalle bakake kun fara kasuwa fa, aman ki koma mu gani.....tana son ya zo da kansa su koma sai ta tabatar cewa lalle bakaken sun yi kasuwa

A hankali ta ce" kan abinda kika fi kwarewa, ina so ki buga wasan da kike bugawa a kan kowa, idanma yana tunanin karantarki ya yi ya san ko wacece ke to zamu yi anfani da sannin nasa mu gwada masa bai san komai ba!

Najeeba kallonta dai take,
Zahrau ta mike tsaye tana mai kokarin kwontar da ita ta ce" abinda nake son ki kula wanda da alama idan kina tare da shi yake bale kansa shi ne *Harshen ki*, ki kiyaye furucinki, ki tsadanta muryarki da kalamanki

Kallon yayar tata take cike da wata kaunarta, tabas ita kanta da ta irga irin abubuwan da ta ringa furtawa sai ta ji wani iri, kamar wata wace aka kunna?

Abin rufa ta ja ta rufa mata har wajen wuyanta kafin ta yi murmushin tsokanarta ta ce" zaki iya jure kwana shida baki je turaka ba?"

Ido Najeeba ta zaro a dan rikice ta ce" Aunty fa"

Zahrau ta yi daria ta ce" yeah, zan rikita iyayenmu, da yan uwanmu dan fara gannin zargin da nake yi idan har gaskiya ne? Ko kuwa hasashena ne

Najeeba kam bata iya cewa komai ba sai rakata da kallo da ta yi kafin ta maido dubanta waje guda, wani irin dukan jikinta ke kwasa du idan ta hango shi a kasan idannuwanta, gaba daya jikinta sai ta ji wani irin yar yar yar take iya bude idannuwanta da sauri
.......................
SULTAN

Yana cikin aiki da computersa bayan ya gama da taron mutanen da ya gama da rigimarsu yan kasuwa ne sannanu da suka kawo karar junna kan a masu tsakani da junnansu bayan sun kasance makota ne sosai, wannan shara'a sai da ta saka aka kirawo manya manyan malaman da suka zo suka ringa kawo manyan ayoyi bisa hakan, dayan ne ya kasance mai neman fitina ko rufe ido ne? Sun hada makotaka da junna, layi daya aman sana'a ta zamo tak tak iri daya, kuma abin kamar da gangan yake yi domin baya tashi siyan abu sai ya ga dayan ya siyo ya zuba shima sai ya kawo da yawa ya zuba sannan da neman fitina ya rege kudinsa sosai ta yanda zai kwacewa wancen mutanensa sai daidaiku, yana yi masa haka sosai da sosai har asara yake saka sho tafkawa wanda karshe ya gane da wata a kasa, domin shima ba wani uban kudi yake sakawa kayansa ba, yar ribar da zai bi shi sai ya ki dorawa ya bada kayan a yanda ya sara, hakan ya matukar saka masa tashin hankali duba da shi din yanzu ya fara tashi yana ta kokari ne dan ya ciyar da iyalansa ya fi karfin yan matsalolin rayuwa, shi kuwa dayan shagonsa cike yake makil sannan zai kai ukun na dayan kuma sana'arsa wace aka fi saninsa fa ita saifa kayan abinci ne, aman tsabar neman fitina a yanzu ba abinda baya saidawa domin daga makocin nasa ya saro wani abin shima sai ya saro ya kima karya, sam baya so ya ga yana samun na rufin asiri shi kuwa abin ya kaishi bango ya maka shi a gidan sarki

Lamarin ya so ya ja daga sosai sakamakon mutumen da aka baiwa damar magana ya nuna Niger din shin ba kasa ce ta republic ba?, yana da yancin yin sana'ar da yake so da zarra ba satar kudin ya yi ba, ya dora da fadin ya san yancin kansa ba zai kawo shi kara kan wannan ba

Wannan lamari ya saka sai da ya yi kira ga manyan malaman fada da na garin baki daya, suka amsa kira kafin a fara gabatar masa da nasiha mai ratsa jiki, da manyan hujoji da ayoyin da suka zo da maganar haka, kafin ya samu ya gabatar da shara'ar

Hakan ya saka kansa ya dauki zafi sosai ga harkar kasuwancinsa da yake son zama ya hada kan irin abubuwan dake shigowa da irin abubuwan da aka fi muradi wa'inda yaronsa baba zai je shaina da kansa ya yi oder su

A hankali ya mika hannunsa ya dauki cofin glass mai dauke da jus din ananas ya kai bakinsa ya dan sha kadan kafin ya ajiye ya ci gaba da dane danensa

Yar karamar wayarsa wace yawanci ahalinsa ke nemansa ta layin ce ta dan motsa alamar vibration

Dauka ya yi ya duba
Sakon Zinaria ne, rabonsa da ita yau zai kai kwana hudu, sako ne tana son zuwa bangarensa idan ya gama hutawa

Amsa ya tura mata da ok kawai kafin ya ci gaba da aikinsa

Yana nan zaune a falon nasa kamar da minti talatin, har ya gama dane danen ya rufe ya daga kansa sama ya lumshe idannuwansa ya tsinkayo tafia daga corridor din dake kawota bangarensa

Bai daga kansa ba, har ta shigo ta karaso dan kusa da shi kadan

Kamar yanda ta saba ta zube kasa kanta a kasa ta jimke hannunta guda ta sanyaya muryarta ta budi bakinta ta fara magana kamar haka"

......................🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻

*Na*

*SAJIDA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

48
Chapter 92 · 0% Book details