Sashe 97
Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji kayi hakuri da maganar sa kazauna ayimana afuwa munshigo kai tsaye batare da sanin kuba,
maganar da Abu yayi ce tasa dady dan jin dama dama sannan yasamu waje ya zauna gaba dayan su zama sukayi banda meer, yana tsaye saifaman harhade rai yake ya cika yayi fal kiris yake jira ya fashe, dady kwa sai tukwicin harara yake samu daga gare sa sarai kuma yana sane da irin kallon da yake masa kawai rabuwa yayi dashi,
shiru falon ya dauka bKajin motsin kowa kowa yayi shiru ana sauraron Abu,
gyara zama Abu yayi sannan yace "kamar yanda nagaya muku sanadin wannan yarinyar muka hadu ina fatan ai kunsan sanadin barinta nan kunsan da batan ta, to dan gurina ne ya hadu da ita a hanya wasu sun biyo ta yataimake ta ya kwace ta a hannun su bayan ya kaita gida kuma wannan baiwar Allahn da kuke gani ya nuna maama da tayi jigum kana kallon ta zata baka tausaayi ita kadai tasan kalar tunanin da take aranta,
cigaba yayi da cewa"tana ganin ta tace wannan duk inda ta shiga ta fito jinin tace munajin haka duk abun yabamu mamaki dan har muka fara tunanin ko ciwon tane yatashi saidai da mukayi duba sosai sai muka gano kamannin da suke da ita shine muka zauna muka tattauna yarinyar tafara bamu labarin ta tunda taji labarin ta ta kara tabbatar mana da jikarta ce dan haka itama tabamu nata labarin yanayin labarirrikan su shiyasa muka kara yarda da gaskiyar maganar ta,
duk abun da kakarta ta baku labari muma tagaya mana anan take sanar damu kune kuka taimake su suka zauna anan tare daku ita kuma ta koma wani gidan da zama dalilin hakanne yasa mukace ta rako mu nan dan muga kakartata kuma wadanda suka ce zasu fara bincike akai muka suma mugana dasu dan muji ko sun samo wani labari sai sugaya mana sai muci gaba daga inda aka tsaya mu hada hannu karfe wajen gano masu hannun acikin wannan lamarin,
maganar da nake muku yanzu wannan baiwar Allah da kuke gani itace kakar wannan yarinyar itace uwa ga wannan yaron da aka buge masa ita akan titi atakaicedai wannan mata da kuke gani matar sarkin garinnan ce tun ada amma yanzu bansani ba shine sarkin ko kuma wani halin gidan sarauta aka nuna mata aka koreta daga cikin gidan ita da yayan ta bayan ta fita daga cikin gidan ma aka kara binta aka bigeta da mota saboda ba aso taci gaba da rayuwa sai kuma gashi Allah ya nuna musu karshen su ta warke sumul ta samu lafiya kuma babu abun dabata tunaba saidai makara yiwa Allah godiya da samun lafiyar ta,
har gidan tasani saidai yanzu baza mushiga gidan kai tsaye ba dole sai mun fara bincike tukunna mutunkari cikin gidan ayi kan me uwa jawabi domin da shedarmu zamu shiga tayanda zamu kama mutum dumu dumu bashi da damar kare kansa ko kuma yayi yunkurin kai wani harin ga rayuwar ta ina fatan kun fahimci inda maganata ta dosa,
"Ammi ce ta tashi daga inda take ta dawo kusa da maama tana ta sakin murmushi tana cewa Alahamdulillah Allah kaine abun godiya ashe zanga wannan ranar yau naga jinin Ameesha abun da bantaɓa tunanin ba ko amafarki gaskiya naji daɗin wannan lamarin su kuma waɗanda sukayi muku wannan abun Allah ya toni asirin su Allah habayyana su,
juyawa ta ƙara yi ta kalli bossay tace Aliyu kaji fa yanda Allah yake haɗin sa ta inda ba azata su saceta daga gurinku gashi kuma fitar tata daga gidan daman shine sanadin haɗuwar tasu maza ka kira dadda Allah sarki nasan yanzu tana cikin damuwa baiwar Allah yau tazo taga mahaifiyar ɗanta nasan sai tafi kowa farin cikin wannan rana,
Ammi duk tabi ta rikice kana ganinta zakaga tsantsar farin cikin da take ciki,
bossay ma sosai ya nuna farin cikinsa da wannan labarin daman yagaywa su Sameer matar nan suna da alaƙa da Ameesha suka ƙi yarda amma shima baitaɓa kawowa wai ko kakar ta bace shidai kawai yaga sunyi kama sosai ashe babbar alaƙa ce atsakanin su, baisan loƙacin da yatashi ba yaje ya rungume Ameesha yana tayata murnar haɗuwar ta da kakar ta kuma zata haɗu da danginta,
agurin dai babu wanda bai nuna farin cikinsa ba amma banda dady da komai yatsya masa abun damuwar shine maganar da maama tayi masa wai tasanshi kuma yana ɗaya daga cikin masu laifi wanann maganar ba ƙaramin ɗaga masa hankali tayi ba,
bayan sun ɗan tsagaita da surutun
ummy tace "yanzu tana ina kakar ta take akira mana ita ina ta tafi,
Ammi ta kalle su tace dadda ai tafi neman Ameesha tace bazata sake dawowa nan ba saida jikarta nan dai ta basu labarin abun da yafaru tabar gidan sannan tace musu ayanzu dai dadda tana gidan sarki taje nema jikar ta cikin gidan sai daru take musu wai sai sunkaita wajen sarki takai ƙarar su Aliyu wai su suka kashe mata yarinya saboda tayi mafarki ta mutu kuma sutagani dan haka dole mafarkin ta gaskiya ne da ƙyar de aka lallaɓata ta haƙura tana cen ita da yara suna ɗebemata kewa amma nasan suna gamawa ne dadda da bata da mantuwa yanzu dai bamusan meke faruwa ba, Aliyu ka kiramana su muji sai agaya musu suma duk suzo ana neman su,
ummy tace Allah sarki gaskiya ta burgeni ai gwara da take jajirtacciya badan hakaba ai da tuni sunci galaba akanta kuma mutane da yawa zasuna cutar ta amma data tsaya tsayin daka akan ta kinga gashi sunkawo har yanzu kuma Allah zai fara bayyanar da gaskiya, zanso ganin matar nan wallahi dan tayi matuƙar burgeni kwazonta ya burgeni,
"nima dai haka wallahi jin tana mace tayi irin waɗannan abubuwan shekara da shekaru ta iya jurar ko wane irin tashin hankali ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba,Abu ke wannan maganar.....
cike da murna bossay yazaro wayar sa a aljihu ya dannawa sam kira batai wani ringing me yawa ba sam ya ɗauka yana ɗauka bossay yace "ka koma gidane?
sameer yace "a'a " amma ina hanya yakamata kaima ka komo yanzu saboda ina dawowa zamu tafi wajen mutanen nan,
bossay yace ok amma kafin nan idan ka koma ka ɗauko dadda kutaho gidan mu gaba ɗayan ku ga Ameesha agidan mu amma dai sauran labari sai kunzo kudai yi sauri kawai,
aɗan zabure sam yace kamar yafa wacce Ameeshan kake nufi yayi tambayar a mamakin ce,
jin yanda yayi tambayar saida yasa bossay ɗan sakin murmushi sannan yace"Ameesha nawa kasani wacce dai muke nema gata nan agabana kaidai kuyi sauri kuzo akwai labari kwaji idan kunzo,
duk yanda sameer yaso bossay yagaya masa abun dake faruwa amma yaƙi gaya masa har ɗan ɓata rai sam yayi wai duk dan yagaya masa amma yaƙi daga ƙarshe ma sai ya kashe wayar yana masa dariya,
duk sunajin sa abun da yakeyi ɗin amma suma daman hakan suke so gwanda kar agaya masa ɗin in yazo yagani,
ummy ce tace "wai nikam kamar naji kince kakar tata tana gidan sarki sarki nawane anan garin,
Ammi tace "sarki ɗaya ne mana nima abun da nake taso intambaye ku kenan naji kunce matar sarkin garinnan ce ko,
Ummy tace "eh haka tace,
tofa nan ake yinta ana wata gawata kenan shi ai yaron da Aliyu ya kira yanzu yaron gidanne yanzu hakama kakar tata tana gidan sarkin da kuke magana,
gaba ɗayan su sai yanzu suka kawo abun da ake magana akai bossay ne yafara magana,
wai daman kuna nufin gidan su sam anan take abun nufi yanzu shin sam da Ameesha ƴan uwane kenan, yayi maganar yana rarraba ido ya kalli Ameesha ya kalli sauran itama kanta Ameeshan jinta tayi wani iri wai daman ita jinin sarauta ce gidan da taje har taji bata son zaman sa daman nanne asalin ta su Hamra da Amna duk ƴan uwanta ne na jini Inna lillahi wa inna lillahi rajiun wannan wane irin abune yazo mata sama taka jin maganar tasu take kamar amafarki har yanzu bata gama yarda da abubuwan da suke faruwa ba,
Ameesha bossay yakira sunanta ɗagowa tayi ta kalle sa sai yasakar mata murmushi yace congratulation ashe keɗin jinin sarautace bamu saniba keɗin jikar sarki ce nataya ki murna kasaƙe tayi tana kallon sa dan ita har yanzu bata yarda ba da abun da yake faɗa,
Abu yace "gaskiya wannan abu yayi kyau daman shiyasa arayuwa akeso ka kyautata mu'amalar ka da kowa karka wulaƙanta kowa dan aduniya bakasan da wanda Allah zai haɗakaba yanzu kuma zaune tare tsawon loƙaci batare da kunsan da hakan ba gashi shi hana niyar taimaka miki baisan ƴar uwar sa yake taimaka ba wannan abu sai lamarin Ubangiji shi yasan yanda zaiyi da kowa yabayar asanda yaso kuma ya hana asanda yaso inmukayi duba gaba ɗaya da haɗuwar tamu da gano wasu abubuwan duk ba wani loƙaci aka ɗaukaba duk tsawon loƙacin da muka ɗauka muna tare da baiwar Allahn akwance bata tashiba Saida Allah yaso ta tashi sannan ta tashi kuma da tashin nata da barowar mu can ɗin gaba ɗaya akwana biyu hakan tafaru,
gaskiya ne maganar ka cewar ummy gaba ɗayan sudai kowa saida ya tofa albarkacin bakinsa,
Meer yace "yauwa to Abu kace abari sai angama tattaunawa to angama yanzu sai adawo maganar kan wannan mutumin da tace tasanshi tun ɗauzu take son yin magana kun hanata sai faman surutu ake,
jikin Ammi ne yayi sanyi jin yanda meer yake magana kansa tsaye yana nuna dady da yatsa yana cewa wannan mutumin itadai tasan mijin ta mutumin kirki ne bata tunanin aduka labarin nan da aka bayar zai iya saka hannun sa aciki wajen cutar da rayuwar su,
da ƙyar ta daure ta buɗi baki tace dadyn su kagaya mana wani abu yataɓa haɗaka da matar nan ko kuma dasaka hannun ka acikin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da aka bada labari ka gaya mana gaskiya dan Allah,
da sauri ya girgiza kan sa yace "nikuma mai zaisa incutar da wani ko kuma insaka hannu acutar da wani ba ɗaya daga ciki ni bansan taba yau nafara ganin ta saidai kawai ko in kama nake mata da wani daban amma bani bane,