← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 139

Sashe 71

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Memakon tabasa amsa saikawai tayi zunbur ta mike tana girgiza kai tace "sameer ina ni i na nutsuwa ai banga ta zamaba zama bai kamace niba ahalin yanzu bani da ikon zama hankalin bazai taba kwanciya ba,

ya ilahi sam ya fada afili tare da dafe kansa da yaji yana sara masa cike da gajiyawa yace momma nifa nagaji tundazu sai abu daya kike fada kinqi sanar dani yakike so inyine yana kaiwa nan ya mike tsaye ganin haryanzu batayi magana ba yasa shi nufar hanyar waje dan zuciyar sa tagama kaiwa karshe yaga inba haka yayi mata ba bazata fada zata cigaba da bata masa lokaci ne kawai,

ganin zaifita yasata da sauri cikin rawar murya tace sameer daman akan batun yarinyar da kukawoq jiya ne........sai kuma tayi shiru takasa qarasawa,

cak ya tsaya tate da juyowa asukwane yadawo da baya yazo gabanta,

WHAT...!!!?
yafada da qarfi yana kara matsowa kusa da ita,

"momma what u say yarinyar da muka kawo jiya kike magana akai me yasame ta me yafaru da ita wayataba ta?

tsorone yaqara kama momma ganin yanda duk ya rude lokaci daya sai faman tambayoyi yake jero mata,

shiru tayi bata basa amsaba, "momma kigaya min abun da yafaru da yar mutane,

"daman dazu da safe tunda suka tashi bayan sunkarya suka fita cikin gida suka gaiggaida mutane suka dawo sai ita ta kwanta bacci sukuma suka qara fita,

Sainaje dakin ingano lafiyar ta sai kawai na tarar da ita azaune tayi tagumi nake tambayarta abun dake damun ta take sanar dani cewa ai ta tashine bataga su Amra ba shiyasa tayi ta gumi nace tayi hakuri tazo nakaita gurin su shine muna fitowa ma sai mukayi karo dasu sun shigo da gudu sukace wai yaya Ammar yace taje yana son ganin ta da farko ma kin amince musu nayi sai da suka hadani da Allah da annabi sannan nace to suje basu dade ba da fita ba suka qara dawowa sukace yace wai sushirya zai kaisu shopping da murnar su suka shiga suka fara shiryawa.....
dan dakatawa tayi da maganar tana kallon sa ganin yanda ya zuba mata idanu yana kallon ta ko kiftawa bayayi,

hada ido sukayi dashi hakan yasa tayi shiru takasa cigaba tare da yin qasa da kanta,

hannu yasa yadago da ita suna facin din juna sannan yace momma me kikeson kice min kiyi maganar ki kai tsaye kigaya min abun da yafaru da ita kawai kibar duk wani bayani a yishi daga baya ina jinki accident sukayi ko kuma wani mugun abunne yasameta,

janye jikin ta tayi daga riqon da yayi mata sanan tace gaba daga inda ta tsaya batare da tabi tayanda yakeso din ba,

"tace dole inyi maka bayani ko kanaso ko bakaso,

shiru yayi tare da nade hannayen sa a kirjin sa yaci gaba da sauraron ta,

bayan sungama shirya suka fita to tunda suka fita basu dawo ba sai bayan sallar magariba dan har ina tunanin kiransu sai gasu sun shigo da gudu suna kuka natare su nace me yake faruwa suke sanar dani wai bayan sunshiga sungama yo shopping suka fito tare amma da suka shiga mota sai suka nemeta suka rasa sama ko qasa sun nemeta sun rasa.......

sun nemeta sun rasa sun nemeta sun rasa yafada yana jinjina kai momma me kikeso kice atakaice de kina nufin kice basu ganta ba tabata kenan ko me kike nufi,
"Eh" wallahi haka nima naji abun kamar amafarki wai basu ganta ba,

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, inna lillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake nanatawa a fili yace momma momma momma saida yakirata sau uku yakasa kuma cemata komai, idon sa har yafara canza kala,

da sauri tayi kansa tare da riqo hannun sa tace yanzu meye mafita nagaya maka dan kasamo mana mafita gashi kuma naga kai kana ma neman kafini shiga damuwar ni wallahi ma iyayen yarinyar nan nake ji ga wancen yayan nata ma dake waje bansan da wane ido zan kalle sa ba yaran nan sunso su tafi da ita jiya na hanasu suka hakura saboda bayanda zasuyi amma gashi kuma abun da yafaru yanzu meye abunyi,

daurewa kawai yayi tare da cewa ina su Ammar din suke,

"na korasu nace suje su lalobota kar wanda yasake shigowa inda nake inba tare da itaba gabadayan su na kora daga shi har su Amran wannan ai shirmene da shiririta ace kuna tare da mutum har yayi wani wajen baku kulaba koma dauke ta akai ai kamata yayi ace sunga wanda yazo daukan nata amma dake daga su har shidin bamai cikakken hankali sunje sundawo batare da ita ba kuma suka iya dawowa cikin gidan nan suka gaya min saboda tsabar sakarci,

"bawani zancen su koma nemota gwara ma kiyi musu waya sudawo kawai fitar suma baida amfani gwara sudawo kawai dan ba ganin ta zasuyi ba,

ina ganin ba laifin subane anshirya dauketa ne tun farkon fitar su shiyasa har akayi nasarar dauke ta batare da sanin suba,

idan Ammar din yadawo kice yazo ya sameni a part dina,

yana kawaiwa nan baijira cewar taba kawai yayi saurin barin wajen ya nufi hanyar fita yana jinta tana tsayar dashi amma baisaurare ta ba ya bude kofa ya fita tare da jan kofar abakin kofar ya tsaya tare da dafe kansa shikadai yansan abun da yakeji aransa duk wani tunanin sa nema yake ya tsaya yana tunanin sunkusa toshe wata hanyar gashi ankuma jawo musu wani aikin yanzu ta ina zata fara neman tama kuma yana da tabbacin wannan abun yana daya daga cikin shirin wadannan mutane su suka sace ta ko tantama babu, wani tunanin ne yaqara fado masa to idan sune meyasa basu sace ta tun lokacin da take hannun dadda ba lokacin ma da bawani tsaro da ake bata gashi taba zuwa makaran tama ita kadai duk tsawon lokacin da ta dauka awajen ta ba taba kokarin dauke taba amma sai gashi daga zuwan ta gidan su kwanan ta daya ansace ta shida yake tunanin ma ta dawo nan da zama gashi ba aje ko inama ba ansamu matsala abun da baitaba tunani ba,

yanzu tunanin da fargabar sa shine idan dadda taji labarin batan ta yasan bazata taba yarda dasuba bama ita kadai ba gaba dayansu har su bossay kunyar gaya musu yake ace wata matsalar daga gare sane tasanadin sa hakan yafaru shikam yau ina zaisa kansa taya zai sanar dasu wannan labarin marar dadin ji,

ya dauki lokaci me tsawo agun kafin ya daga kafafun su da kyar yajasu yatafi wajen su ransa fall tunani kala kala,

yana shiga falon duk sukayo kansa suna tambayar sa lafiya me yake faruwa amma bai iya basu amsaba,

abun da yafi basu mamaki ganin idonsa ya canza kala gashi kallo daya zakai masa ka fahimce halin da yake ciki basugana cika da mamaki ba saida suka ga yasa hannu yakamo duka hannayen su ya shiga jansu kamar wasu sukaye haka suka shiga binsa abaya batare da kowa yaqara magana ba suka nufi hanyar waje ahaka suka cigaba da tafiya har sukaje part din fulani ba wanda yayi magana, duk sun zuba ido suga iya gudun ruwan sa,

saida sukaje bakin qofar sannan yasake su tare da tura kofar suka shiga ciki su shettima mane suka samu damar yin sallama amma banda sam da ahalin da yake ciki bazai iyayin magana ba bakin sa yayi masa nauyi,

fulani ce zaune kan kujera tana waya shigowar su yasa tayi saurin katse wayar tare da amsa musu sallamar su ba yabo ba fallasa suka gaisa amma banda sam da suna shigowa ya wuce part dinsa,

fulani tace lalle yaran nan kuna sha'anin ku yanzu kaima saikaga dama kake zuwa inda nake yanzuma nasan badan munhadu ba wucewa zakayi baza kanemeni ba daman ance zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai yanzu kaima kafara daukar dabi'ar wancen marar mutun cin da baya ganin mutane da gashi kaima haka kake so ka koma kaima ko to sai kuje kuyi tayi kar kufasa,

dan shafa kai shettima yayi sannan yana dan murmushin dole sannan yace tuba muke mama wallahi ba abun dakike tunanani bane abubuwane yanzu sukai min yawa nan dinma yanzu ba kullum nake shigowa ba wataran kuma idan nashigo bana samun ki anan shiyasa amma de kiyi hakuri za'a gyara,

kai kasani bawani ba ka shigowa jinake ko jiya dare anan yayi muku amma baka nemeni ba idan baka gani anan ba bakasan inda dakina yake ba ko kodan baikamata ma inga laifin kaba wanda kaci kashin sama kaci futsarin sa baigirmamakaba baka da daraja awajen sa bare kuma wanda bakai mishi komai ba shi kallon arziki ma wataran baka isa kasamu daga gurin sa bare har yadaga kai yazo inda kake ya gaida kai, nidai shawara wallahi ku gyara halinku dan wannan ba hali na gari bane,

to mama fulani zamu gyara in sha Allaha kiyi hakuri yanzude komai ya wuce tuba muke kanmu bisa wuya,

"zadai ka canza amma wancen murdadden bazai taba canzawa ba,

kidai yimasa addu'a zaidaina in Allah ya yarda,

tabe baki tayi tace oho de kuka sani,
dahaka de sukayi sallama da ita suka bi bayan sam daman Allah Allah suke tayi ta sallamesu tabi ta tsaresu da surutu,

suna karasawa suka shiga da sallama abakin su,
can kan kujera suka hango sa ya hada kai da gwiwa ya kifa kansa akan gwiwowin sa da sauri suka karasa inda yake shettima ne yafar zuwa yace,

"Subhanallahh"

"sam lafiya meyake damunka haka me yake faruwa?

dagowa yayi yana kallon su daya bayan daya da jajayen idanun sa da suka canza kala,
kawai kallon su yake yakasa ce musu komai.
kallo daya zakai masa ka fahimci tsatsar bacin rai da damuwa da yake ciki,
sosai suka shiga damuwa ganin damuwar da yake ciki,

cike da damuwa shettima ma yace haba sam kasanar damu abun dake faruwa duk kasakamu acikin damuwa,
Chapter 71 · 0% Book details