← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 139

Sashe 7

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

      *AMEESHA*
da gudu ta tashi daga kan Ammi ta koma wajen dadda tana zuwa ta rungume ta tare da fashewa da wani kukan cikin kuka tace dadda kiyi hakuri da irin abubuwan danayi miki ashe haka kisha wahala akan iyayena da kuma ni kaina rashin sani yasa har nake yi miki wasu abubuwan dan Allah ki yafe min duk abun da nayi miki bazan qaraba shafa bayanta tayi tare da cewa ya isa haka ni baki min komai ba hasalima ni yakamata in baki hakuri tunda duk ni ce silar dayasa har suka kusan kashe ki baniya yin komai ba akai a'a dadda karma kice haka duk wani qoqari kinyi akaina kuma kina kan yi hannu dadda tasa ta raba ta da jikin ta sannan ta share mata hawayen ta kana tace ya isa haka ki manta da komai yanzu nasamu in tayi in sha Allahu zaki ga mahaifin ki duk inda yake zamu nemo miki shi adaina yi miki gorin mahaifi ko kai ta daga mata tare da cewa dadda to yaushe zan ganshi wlh harna matsu inganshi ashede ina da uba ake cemin bani dashi aikwa yana dawowa gareni zanje innunawa aunty  Rasheeda da mom suganshi sudena zagina dadda tace kwarai kuwa shalelena daga lokacin ba wanda zai qara zaginki akan uba saboda naki ubanma yafi na wasu,
ganin de alamaun sun mantama da zaman si agun yasa hajiya yin gyaran murya batare da tace komai ba dagowa sukayi gaba dayan su suna fuskan tar su Ameesha ce ta kalli bossay tace yaya bossay ai zaka kaini wajen aunty Rasheeda ingaya mata ina da mahaifi ko mahaifita kuma tarasu tun ina qarama tana qarasa maganar kuma sai jikin ta yaqara yin sanyi tunawa da yanzufa bata da uwa kenan ita marainiya ce kula da hakan da bossay yayi ne  yasa yayi saurin tashi daga inda yake yakoma kusa da ita yazauna tare da ruqo hannun ta sannan yace karki qara yin kuka yanzu bakiga  nan gurin gaba daya iyayen ki bane dukan su zasu daukeki kamar 'yar cikin su daga yanzu baza ki qara neman wani abu kirasa ba uwa sai wacce kika zabama gasunan ga kuma daddar ki akusa dake itama tamkar uwa take kula dake dan haka karki qarajin ba dadi agame da mahaifiyar ki kiyi mata addu'a kawai kinji meesha na kai ta daga masa tare da dan qaqaro murmushin yake da iyakacin sa kan labba ahakanli tana kallonsa tace thanks shima murmushin ya mayar mata zai qara magana kenan Ammi tayi sairin  katsesu da cewa yanzude komai ya kusan zuwa qarshe kamata yayi mu tattauna akan yanda za abullowa al'amarin ko bahaka ba hajiya, hajiya tace eh hakane gwara asan abunyi yanzu ku yakuke ganin za ayi duk kunyi shiru ba wanda yace komai  tafada tana kallon su shettima shiru sukayi sai daga bisani sannan shettima yace hajiya ni wlh bansan ma mezan ceba dan wlh kaina yagama daurewa gabadaya akan wannan lamarin tace yama kunce tunda kukazo kuka tambaya aka baku labari ai dole ku tsaya tsayin daka ganin komai ya daidaita tunda kune maza daman mace bazata iya ba dole saida namiji aciki tana kaiwa qarahen maganar ta maida kanta kan SAM da yayi zurfi cikin tunani dan hankalin sama gaba daya ba akansu yake ba saida hajiya ta tabashi tace to kai kuma fa me zakace akan wannan labarin ya kake ganin za ayi dan girgiza kansa yayi tare da maida hankalin sa gareta sannan yace tunanin da nakeyi kenan inason yin dogon nazari akan maganganun ta kubamu lokaci zamuyi shawara muga ta ina yakamata mufara Ammi tace to hakan ma yayi daman dole sai anyi dogon nazari akai hajiya tace hakane wlh abunne duk wani iri danni labarin ma ba komai na fahimta ba kafin ingama tantance wannan sai inji wani abun da yafi nabaya abunde sai ahankali ,
Sam ne yace kar kudamu kubar komai a hannun mu zamuyi komai  maida dubansa yayi ga dadda da itama hankalin ta na kansu sannan yace yauwa dada kike ko dady hararar sa tayi tace kaifa matsalata daki kenan naga alamar baza mushirya dakaiba ka rainani wlh to kairani da hadizatu na kawai kai tsaye da ka tsaya kana lalata min suna yanzu inbanda abu irin naka ina sunan dadda yayi kama da dada  ko dady kanade sane kawai daman dan kasani magana ne  shiyasa kafadi haka to ka kyauta banza yayi da ita be tanka mata ba saida yaji tayi shiru sannan yace what ever de ni banda lokacinki kinajina tambayoyi zan miki tace to inajinka dan ta fahimci kamar yana da miskilanci be fiya zama ana jayayyar magana dashi ba.........✍

❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿5&6
Bismilah.......✍

____________*AZEEMA*
        Ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi saurin sunnar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannun ta wani bafade ya daka mata tsawa da cewa ke zonan dan ubanki daga ina kike wacece ke jiki ma kyarma ta daga qafa da kyar amma sai taji takasa tafiya saida ya qara dakama ta wata tsawar bata san lokacin da ta qaraso gurin sa ba zubewa tayi a wajen sai kawai ta fashe da kuka shide sarki tare da wasu mutanen har sunyi gaba saura mutum biyu awajen,
cikin kuka tace dan Allah kuyi hamuri ni marainiya ce iyayena duk sun mutu shine nazo nan ataimakamin daya yace to waya baki iznin shigowa ko ance miki nan gidan mabarata ne kai ta girgiza musu tare da cewa a'a ammade na tambaya na shigo me gadi ne yace inzo abani abinci yau kwana na biyu banci komai ba sai ruwa nake shi dan karku koreni ku taimaka min kumin rai bani da inda zan iya zuwa neman taimako da ya wuce nan wanine ya daga hannu zai kifa mata mari akayi saurin dakatar dashi tsayawa yayi tare da juyawa danganin me maganar duk dade daman yagane muryar Amma ce (maman 'yan biyu) itace ta qaraso wajen tace me nake gani haka wannan 'yar yarinyar zaka daka tafada tare da saka hannu ta dago da Azeema tsaye tace yarib me yake tafe dake nanmade cike da kuka tayi mata bayanin abun da yakawota bayan Amma nagama jin labarin nata sai tacewa muta nan suje kawai suka juya sukatafi itakuma sai tace to ya isa haka share hawayen ki zan taimaka miki kinzo inda ake taimako zo muje tafada tare da ruqon hannun ta suka fara tafiya,
ran Azeema fari tas dan ji take kamar ta kama tsalle awajen saboda murna da kyar take iya riqe murmushin da yakeson kwace mata dadi be gama cika ta ba saida ta ganta acikin falon Amma anzaunar da ita akan kujera wani irin farin cike ne yasake lullubeta wanda duk son dannewar ta idan ka qura mata ido sai ka fahimci tana cikin farin ciki  bayan ta zaunar da ita sai takira wata jakadiya tace ga wannan yarinyar nan kije da ita dakinki tayi wanka kisa ma mata kayan da zata saka sannan kibata abinci taci ta qoshi sai ki kawo min ita zamuyi magana da sauri jakadiyar ta amsa da to tare da cewa Azeema tazo su tafi tashi tayi tabi bayan ta suka bi wata hanya suka bar falon,
Chapter 7 · 0% Book details