← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 139

Sashe 33

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani iri taji aranta kamar zatayi kuka harga Allah da yabata labarin ta zata ko da ita yake amma jin yace yana tunanin wata kuma har yace wata yake tunani yadade be ganta ba tasan to bada ita yake ba kuma bahaka taso jiba taso ace ita yakeso ashe duk kulawar da yake bata ba sonta yake ba ashe ita fa yaudari kanta tun farko aikwa yazam dole tayi qoqarin cire shi aranta tun ba ayi nisaba duk da batagama sanin  soba amma tabbas tasan tana sonshi so tunfarkon haduwar su taji ya burgeta kuma insuna guri tare bata son taga sunrabu idan ta dade bata gansaba sai taji tana kewar sa tunawa tayi da wani lokaci da yadade be zo gurin aunty Rasheeda ba taji tadamu da rashin ganinsa agidan gashi bata da damar da zata tambaya yana ina sai kawai taje tana gyara mata daki sai tayi karo da qaramar wayar rasheeda kuma tasan daman da ita suke waya sai kawai ta dauka ta tura masa message akan dan Allah yazo tana bukaqatar ganin sa akwai wata magana mai muhimman ci da zasuyi haka ta rubuta ta tura masa amatsayin Rasheeda ce tana turawa tagoge message din daman kuna ranar rasheeda bata nan ba jimawa kuwa yazo gidan tanajin qarar motar sa ta fita tana ganinsa taji dadi aranta sai ta basar kawai ta nufi hanyar fita irin batasan da zuwan sa ba saboda tasan dole yakirata hakan kwa akayi tana danyi gaba ya kirata ta dawo bayan sungaisa tame cemasa ai bata nana yanzu suka fita amma watakil ba nisa tayi ba tayi masa hakane dan yajirata ita kuma tasamu dama sutayin hira tana kallon sa tanajin dadi,

batasan lokacin da numfashi ta kufcema ta "baby meesha ya akayine naga sai faman murmushi kike ina ta magana ma amma kin tafi tunani me kika tuna haka bani labari ko kintuna saurayin kine dan wannan murmushin naki yayi kama da na soyayya,

dan harar wasa tayi masa tare da basarwa da kawar da duk wani tunanin sa da yake neman hana ta sukuni lokaci daya taqara qaqaro wani murmushin dolen  sannan tace haba wace ni ina yar qaramata inkama tunani saurayi ni yanzu ina naga lokacin soyayya soyayya ai sai ku, kaga ma nidan gayamin ma budurwar taka a ina take haka inje infara nemawa yayana fada agunta kar wani yayi mana wuff da ita muyi dakon banza gwara inje inkafa in tsare in hana kowa kulata,

duk wata damuwa da yakejin ta sai yanemeta yarasa yashiga yin dariya saida yayi me isarsa sannan yace to shikenan kar kidamu zan kaiki har inda take amma ba yanzu ba kiban lokaci,
"wani abu taqara jin ya dakar mata zuciya qara dannewa tayi "sanna tace to Allah yakaimu lokacin dan har na matsu inganta "yace karkidamu zakin ganta very soon,

shettima da duk suna jin hirar dasuke yayi mamakin jin abun davyake cemata sakamakon kuma agabansu yana cewa ita yakeso matar sace amma gashi ita ya boye mata,
dan kallon sa yayi ta mudubi da har zaiyi masa shiru sai kuma yakasa  yace  malamin soyayya naceba ina da magana irin wannan tsara mutum haka,

kalllon sa bossay yayi sannan yayi murmushi yace inajinka dalibin soyayya gaba dayansu dariya sukayi banda Ameesha da ta tafi duniyar tunani batasan me suke ba shikuma dayan wato sameer dake gefe tunfarawar surutunsu yaji sun damesa ya dauko headphones ya toshe kunnuwansa dashi ko me yake ji oho dan haka sukadai suke kidansu suke rawarsu bayajin abun da suke cewa,

Shettima yace zanzo akoya soyayyar daman ban iyaba nima gashi kuma nima daman inason wata yarinya danake fatan nima ta zama matata,
bossay da yagane da wacce yake tunda yana magana yana kallon Ameesha ta cikin mudubi, shikuma lura da hakan yasashi cemasa a ina take shettima yace anan gurin mana gashima ina kallon ta yanasane yayi masa haka saboda zacen da yaji yanayi shiyasa yakeson yagano da gaske itan yakeso ko kuma wata dince daban kamar yanda yafada din,
kallon sa bossay yayi tare da hararars yace to kwa kwalelen ka dan bazaka taba samu ba gwara ka canza hanya tun kar lokaci ya qure maka dan wannan anriga da an siyar,

dan murmushi kawai shettima yayi batare da yace komai ba kamar bazai yi magana ba sai kuma can yace kanaji  na ko kai yadaga masa yana qara kallon gefen fuskarsa tunda tuqi yake baya ganin fuskar sa gaba daya,

zan baka shawara kar kayi wasa da damarka kadena boye abu ko riqe shi hakan zai iya haifar maka da matsala nan gaba kazo kana da nasani kasan kuma danasani bata dawani amfani kayi amfani da lokacinka alokacin da yazo maka inkabari yatafi tofa bazai taba dawowa ka riqe wannan duk abun da kasan kanaso to kawai go to the street point kar katsaya wani kwana kwana dan haka bashi da amfani yaqarasa fada masa daidai lokacin da suka qaraso tamfatsetsan gate din masarauta yayi horn aka bude suka shiga ciki,

ganin inda sukazone yasa bossay bai bashi amsaba yashiga bin masarautar da kallo Ameesha ma haka dukan su kallo suka bi masarautar dashi kowa da abun da yake kiyastawa aransa da irin kyau da tsaruwar da tayi,
parking shettima ya daidaita sannan ya bude qofa ya fito sam ma sam fitowa yayi ya rage daga Ameesha sai bossay acikin mota duk sun kasa motsawa bare su fito ta barin da Ameesha take shettima  yaja murfin ya bude mata ya leqa yana kallon su yace ko sai an fito da kune zaku fito kuntsaya kufito bossay ne yayi murmushin jin kunya sannan ya bude qofar ya fita ita kuma taqi fitowa sam ne ya cire abun da ya toshe kunnen sa yayo gaba wajen da suke yana binsu da kallon meye ya tsayar dasu ganin Ameesha aciki yace anan dinma sai kin bata mana lokaci kishiga taitayin ki wlh banason shirme duk inda akaje sai anjiraki yafada yana zabga mata harara kamar zai maketa,

duk da ta tsorata dashi amma hakan besa taji zatafito ba hasalima sai ta make kafada murya ciki ciki tace nifa ba inda zani ku shiga kufito kawai duk tsayawa sukayi suna kallon ta da mamakin abun da tace bossay ne yace meyasa ke da za abarki anan bafa dake zamuba sai min dawo sai kutafi kofito dan Allah kinga kina qara bata mana lokaci yafada yana qoqarin kamo hannun ta zai fito da ita amma ga mamakin su sai kawai sukaga tasaka kuka tana ita baza ta fito ba da kyar de shettima da bossay suka lallabata akan zata fito din amma shikam sam ta kaishi qarshe kadan yarage ya hau kanta yavkoya mata hankali ya sauke mata wannan iskancin da takeji dashi,

bossane ya miqa mata hannu dago nata tayi ta dora akan nasa yafara jawota daga cikin motar itama ta yunqura ta zuro qafafunta shikuma ya matsa dan bata damar gurin da zata tsaya qarasa fitowa tayi ta tsaya da qafafunta tana qara bin masarautar da kallo gaba suka farayi su shettima kuma abayansu tana daga qafa tayi tafiya daya biyu zata daga ta ukun kenan wata iriyar qara me kama da kururuwa da sauti me qarfin gaske da taqamaimai baza ka tantance qarar meye ba haka masarautar ta dauka gaba daya duk wani wanda yake cikin ta babu wanda be tsorata dajin ta ba masu qarfin haline kawai zasu iya tsayawa da qafafun su bayan qarara kuma sai masarautar gaba daya tayi wani duhu da dan gibgibtawar abubuwa kafin daga bisani kuma sai ta washe ta dawo yanda take lokaci guda kuma masarautar ta dauki shiru tsit kake ji bakajin sautin komai saboda yawancin mutane abun ya razanar da su da har yakai ga wasu sun sussuma a inda suke saboda babban al'amarin da sukaji wanda tunda suke arayuwar su basu tajin irinta ba Ameesha tana daya daga cikin masu suma inda saida tasaki qara itama kafin ta sume tunkan gurin ma yadauki duhu gaba dayansu sukayi kanta sukayi mata runfa,
nanfa kankace me masarauta ta kidime wasu nasurutu da al'ajabi wasu kuma na koke koke inda zukatan wasu daga cikin masarautar ya girgiza su tare da furgice da tsoron faruwan abu duk yakamasu alokaci guda abubuwa da dama suka faru wannan ranace tadaban akan yawancin mutanen gidan wannan ranace ta farin ciki wasu kuma ranace ta baqin ciki agaresu...........✍️✍️✍️✍️

Hmmm shin me yake shirin faruwa amasarauta me yakawo musu wannan sabon yanayin ko kuma ince abun mamaki da ban tsoro😠😠😠,

ga Ameesha acikin masarauta kuma ga Azeema aminan juna💏
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿31&32

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

      " wata iriyar qara sukaji da yasa mutanen da suke bakin ward din a tsaye susu biyu suna magana jin ihunta yasa suka  kwasa aguje suka shiga dakin ganin halin da matar take ciki yasa su shiga tashin hankali dayane yayi saurin rufe qofar  dayan kuma yayi kanta da sauri yanaso ya hanata kunce igiryar da takeyi dan already ma harta kunce na hannuwan ta tana qoqarin kunce na qafar sai wani fisfisga take kamar zata tashi sama tanayi tana jijjiga gadon asibitin da take kai shima kamar zata karyasa saboda wani irin qarfi da take ji ajikin ta,
sosai hankalin su yaqara tashi,
"gaba ki dayansu sukayi kanta suna rirriqeta tana tafaman fisge fisge gabaki dayan su babu wanda be tsorata da yanayin da matar ta shiga ba lokaci guda duk yanda zasuyi suriqeta amma sun kasa duk qarfinsu nema take tafi qarfin su sai wani irin kuka take tana fusgewa tana sunbatu ni kusakeni kar wanda yaqara riqeni idan bahaka ba duk sai na kasheku tafada tana zazzaro manyan idanun ta qoqarin saukowa daga kan gadon asibitin da take,

  "Suna cikin haka aka turo qofar da qarfin gaske cikin tashin hankali da zafin nama yaqaraso wajen su,

"da qarfi yace kusake ta!!

matsawa sukayi suna faman rarra ba ido,
Chapter 33 · 0% Book details