← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 139

Sashe 122

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nandai aka samu aka lallaɓa gwaggo tayi shiru ta zauna sannan akadai cigaba da tattaunawa akan matsalar inda papa yake cewa ayanzu dai baza a zargi kowa daga cikiba saidai za afara bincike ne har a tabbatar kuma ta inda za afara doke a fito da wanda ya sanar da mutuwar ta ranar da akace ta mutu idan akayi haka tanan za agano ko waye saboda duk wanda ya fara sanar da mutuwar ta dole shine tunda Saida yayi yanda zaiyi ta fice daga gidan sannan aka sanar ta mutu saboda kar ayi wani bincike shiyasa aka rufe musu baki da cewar ta mutu dan kar kowa yaƙara yin maganar saboda,

waziri ne yace "wannan maganar taka gaskiya ce yana da kyau afara da binciken kafin azargi wani saboda zargi bashi da kyau bamusan ta ƙamaimai mai waye da sa hannu acikiba dole sai anfara bincike dan akama mutum da hujja yanzu sai muyi tunanin wanda yasanar da mutuwar ta yanda za ayi mugano shine kowa zai tuna wanda yagaya masa shima sa a tambaye sa waye yagaya masa kunga dagana dole za aje ƙarshen inda maganar ta fito sai mukama koma waye.......,amma yakuka ce da shawarata?

kowa na'am yayi da shawarar da yabayar kuma wasu har sun fara tunanin wanda yasanar da su ɗin Saida babu wanda ya fito ya faɗa saboda ba abada damar faɗan ba,

surutunne ya ƙara yawa kowa da abun da yake fitowa daga bakinsa  sai hayaniya ta nemi ta kaure aciki akayi saurin dakatar dasu......

   da ƙyar aka dakatar dasu daga hayaniyar da suke sannan kafin wani ya ƙara cewa wani abun gimbiya ta miƙe cike da ƙasaita dan ta tuna baya takun da take na matar sarki gimbiya shi tafara yi yanzu saida taga kowa yaɗan nutsu tashiga binsu da ido tana kallon kowa da kyau sannan ta maida kallon gun Meer dake tsaye har yanzu sai ta taka taje har gaban sa sannan ta kamo hannu sa baimata musu ba ya shiga binta sai da taje gaban papa sannan ta sakesa sai ta koma gun da Ameesha take itama ta taso da ita takawo ta gaban papa da hannu tayiwa Abu alama da yazo dan haka yataso cikin rashin ƙwarin jiki dan shifa har yanzu yakasa yarda da abun dake faruwa jin abun yake kamar amafar ki da sanyayyen jiki ya ƙaraso inda suke ya tsaya,

maida duban ta tayi ga papa da ya kafesu da ido yana ta kallon su kamar yasamu T.V yasaki baki kawai,

nuna masa abu tayi sannan tace "mai martaba dawa wanann yayi maka kama inaso ka faɗa da kanka basai anfaɗa maka ba,

kallon ta papa yake cike da rashin fahimtar maganar da take sai kawai ya maida duban sa ga Abu ya kallesa sosai sai ya janye daga kallon sa yamayar kan maama sannan ya shiga girgiza mata kai tare dacewa bansani ba,

kallon sa tayi tace "yakamata dai kagane dan idan nafaɗa bashi ba kai ka yarda?

kai ya girgiza sannan yace "a'a,

Meer ta nuna masa tace wannan ba shifa dawa yake kama nan ma cemata yayi bai sani ba cike da ƙaguwar jin ko SU WAYE SU  aransa yana fatan Allah yasa su kasance jinin sa duk dadai alabarin da aka bayar ba afaɗi wani abu da yashafesu ba,

shiru tayi tana kallon sa taso yagano da kansa saidai daman da kamar wuya da ace dai babu gemu a fuskar Abu tasan zai ganesa gashin da ya rufe masa fuska ne yasa kamannin sa canzawa gaba ɗaya itama da bata gansa a hoton nan ba zai wuya ta gane sa loƙaci ɗaya,

da fuskarta ba aɗan sake ba yabo ba fallasa ba fus as ta saketa loƙacin da take masa magana amma yanzu kuma sai ta ƙara canzata ta koma ta kala tare da shiga tsakanin Abu da Meer ta riƙo hannun ko wannen su sannan ya kalli kowa dake falon cike da dakiya tafara magana,

duk alabarin da akabaku nasan bakuji wanda zai firgita kuba maƙiya yo ta Allah bataku ba yau gani da gudan jinina wanda kuka rabani dashi tun yana yaro yau gashi agaban ku harma da ɗa wannan da kuke ganin sa ɗana ne SAMEER yaron da na fara haifa aka sace min acikin gidan nan to gashi yau ya shigo gidan ubansa da ƙafar sa anfita dashi loƙacin da baisan shi waye ba yanzu kuma yadawo adaidai loƙacin da baku taɓa zato haka ba wannan kuma ɗansane kuma jika agare ni ɗaya tamkar da dubu dan kufara kuka da kanku kodashi kaɗai na barku ya isa ya tarwatsa kwakwalwar ku baki ɗaya ni kuka cuta kuka zalinta kuka musgunawa rayuwata tsawon loƙaci ina kwance batare da nasan inda kaina yake ba batare da naga koda mutum ɗayane da sunan naga mutum kuma nasansa ina ganin mutane tamkar dodanni bana bambamce baƙi da fari ni kaina bansan ko ni mutum ce ko ba ita bace kun mantar dani komai kunjuyar min da hankali na kun rabani da ƴaƴan kun rabani da mijina kun rabani da ƴan uwana saboda son zuciya irin taku to kusani bani zan rama abun da kukayi min ba kuma ba ɗana ne zai rama ba jikanane zai ɗaukar min fansa akanku sai nasa yayi rugu rugu daku sai rama min abun da kukayi min fiye da kallar abun da kukayi min sai yaga bayan ko wannen ku dan bazan taɓa yafewa kowanne kuba dan haifi wanda ya haifi wanda zai iya da kowannen ku babu wanda zai ƙale dan haka kukuka da kanku tun kafin kuyi arangama dashi ina gefe ina kallo hankalina kwance zaiyi duk abun da ya dace, kuma sarautar da bakuso suyi dole suyi da yardar Allah zuri'atace zatai ta yaɗuwa dagana ha ƙarshen rayuwakan mu baki ɗaya jinin zaicigaba da zama a sarauta duk wanda kuma ya ƙara gigin shiga abin da banasaba Allah ya tarwatsa rayuwar sa ko waye shi,

tunda ta fara magana kowa ya sha jinin jikin sa tabbas tunda aka bada labari babu abun da yafi ɗagawa wasu hankali kamar wannan maganar tata ɗanta na farko da ransa bai mutuba gashi harda ɗa shima namiji ga kuma wancen ɗan nata da bai fito ba shima namiji dole kwa sarauta ta dawo hannun su gaba ɗaya kamar yanda tace,

daga cikinsu babu wanda yayi yunkurin yin wata magana saboda tsoro da furgici da suka tsinci kansu fiye da na ɗazu,

papa da gwaggo suman zaune sukayi saboda tsabar mamaki sunma kasa motsawa saida ƙyar gwaggo taje ta gaban Abu tana kallon sa kamar tasamu T.V sai ta kallesa sai ta kalli maama da ƙyar dai ta iya cewa dan Allah wai maganar da nakeji kina faɗa gaskiya ce kodai kunnu wanane suka jiyo saɓanin abun da kike faɗi jinayi fa kince kamar wannan ɗankine Sameer, Sameer dai wanda kika haifa aka sace shi, shine yanzu agabana nake kallon sa ko kuma dai ƙarya kunnuwa na suke faɗa min,

maama ce ta kamo hannuta cike da kulawa tace gwaggo ba ƙarya kunnu wanki suke miki ba abun da kikaji gaskiya ne kuma zahiri ne ba mafarki ba ki kalle sa da kyau jikanki ne,

nandai itama tabasu labarin ta yanda ta ganesa da kuma halayyar Meer da ta zama iri ɗaya da ta gwaggo harma kamannin su da suke shigen kama,

hannu gwaggo tashiga tafawa tana sallallami akan wannan lamarin da abun yagama kasheta da mamaki daga wannan sai wancen komai sai faruwa yake loƙaci loƙacin da basu taɓa tunanin wannan ranar zatazo itakam wane irin farin ciki zatayi na wannan ranar da ta zamemata babbar rana, rana ta musamman,

papa ma tasowa yayi yana ƙara kallon Abu yaudai Abu yazama abun kallo agun family ɗin sa, hannu papa ya buɗa masa suka rungume juna papa yana ta faman sakin murmushi sosai ya nuna farin cikin ganin ɗan nasa da yagama fitar da rai akansa sai gashi yau Allah ya dawo masa dashi kana ganin sa zaka fahimci tsantsar farin cikin da yake ciki marar misaltuwa,

daga nan papa yasaki Abu ya koma wajen Meer da yayi wani kicin kicin da fuska kamar baya farin ciki da dangin mahaifin nasa rungume shi yayi shima yana ɗan tsokanar sa na kaka da jika sannan ya sake shi shima sai yakamo hannun Ameesha itama ya nuna farin cikin ganinta da tausaya mata yanda tasha wahala a rayuwar ta,

gwaggo ma cike da farin cikin ta shiga rungume su tana share ƙwallar farin ciki da ta tarar mata saidai tana zuwa kan Meer zata rungume sa yayi saurin matsawa daga kusa da ita tsayawa tayi da mamaki tana kallon sa, maama ta ɗanyi murmushi sannan tace bazakaje gurin gwaggon taka ba gwaggo ai tun kan muzo ma nake bashi labarin ki saboda halin ku ɗaya ba inda ya barki kaje mana ka matsa itace gwaggon da nake gaya maka mai kamar ka tayi maganar tana ɗan turasa wajen gwaggo, gwaggo daɗi ya ishe ta ance suna kama kuma halin su ɗaya cike da ƙara wage baki ta ƙara nufar wajen sa zata taɓasa ya ƙara matsawa fuska a haɗe yace ni karki taɓani kin tsofa da yawa mai kike jira baki mutu ba, yanayin maganar ya maida bakin sa yanda yake sai ka rantse ma bashi yayi ba,

kasaƙe gwaggo tayi tana kallon sa kafin daga baya maganar ta ƙara tsaya mata arai aranta tace da ina yabonka sallah zaka kasa alwala ashe baza muje dakai ba, a fili kuma sai ta kalle sa tace "ubanka nake jira yazo sai mumutu tare marar mutunci daga yimaka abun arziƙi shine zaka gaya min magana to ahir ɗinka harda wani cewa wai mai nake jira dake daman ni zankashe kaina kenan to Allah baiyi zan mutun ba kuma babu wanda ya isa ya kasheni loƙaci na baiyi ba tafaɗa tare da buga tsaki harda su harara,

ko kallon inda take baiyi ba bare yasa ran zai kulata haka tagama bambamin ta ita kaɗai su maama nayi mata dariya,
Chapter 122 · 0% Book details