← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 139

Sashe 83

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  ka dauko ta muje kamar ya fasa ihu haka yake ji ji yayi kaf duniya ba macen da yafi tsana irin wannan yarinyar gashi sanadin ta tasa mahaifiyar sa nayimasa fada shikuna aduniya inda abun da ya tsana shine fada ya tsani ayi masa fada ko kadan,

yasan duk abun da mahaifiyar sa ta fada gaskiyane hakan zai iya faruwa indai abu yaji labari to shima fadan zaiyi masa shiyasa bashiri badan yaso ba yana bata rai yasa hannu daya ya dagota,

ummy ta kalle sa tace oh yanzu kuma karya mata hannu zakayi to Allah baka sa'a tana kaiwa nan tayi ficewar ta daga dakin,

tsaki ya doka tare da janta zai fita da ita Ameesha ta saki kara saboda bazata iya taka kafar ta ba shikuma ya tsayar da ita da kafafun ta saboda tsabar mugun ta yasani sairai zataji zafi saboda yaga kunburin da kafar tayi amma ya maze yake niyar janta jin tasaki kara yasa ya galla mata harara murya kasa kasa yace wallahi na kara jin kin daga min murya sai shakeki anan kin mutu banza mayya kawai,

Shiru tayi bata kara buda baki ba,

shikuma ahaka yafara janta tana dan dingishi tana dafa bango tana cije baki take taka kafar da kyar tana jin azabar da take mata amma sai hawaye kawai yake fitowa ba karar kuka saboda zuwa yanzu amugun tsorace take dashi,

gani take idan tayi yunkurin daga muryar zai kashetan kamar yanda yace dan haka tayi shiru tana karbar azabar da takeji,

ahaka suka fito har suka wuce falo suka fito waje suka fara taka bene saida yaga sun kusa saukowa falon gudun kada ummy taga ayanda suka fita yasa ya dauke ta ya karaso falon da ita saida ya duba ko ina yaga ummy bata falon sannan ya dire ta da karfi yanda yasan zata kuma bige kafar haka yayi mata ya tsayar da ita da kafafun ta kuma yasake ta,
kasa kasa tasaki kuka tare da saurin zama kan kujerar da take kusa da ita tana hawaye,

hada ido sukayi da shi ya galla mata harara yana girgiza kai irin sai naci uwarki,

da sauri ta sauke kanta kasa,

ganin ta sunkuyar da kanta ya kuma duba yaga har yanzu ummy bata fito falon ba yasa ya matsa kusa da ita kamar abun arziki zaiyi sai kawai yasamu daidai gurin da ya kunbura yataka da kafarsa harda cije baki sannan ya dagata take ta saki wani kukan me sauti tanayi yamake mata bakin yace wallahi idan kibari taji sai na balla miki dayar kafar shifa haushin ta yake ji so yake yaga kawai yayi mata duk abun da zai mata da zasa taji zafi tayi da nasanin biyoshi shi yake so yayi mata,

da sauri ta kara hadiye kukan,

amma saboda rashin imani irin nasa sai ya kara daga kafar zai takata caraf akan idon ummy kafin yakai yajiyo muryar ta,

"au daman rashin tausayin naka har yakai nan bansani ba yaushe ka kara zama haka ta fada tana karasowa gurin kallon ta yayi cikin hade rai yace ummy me kuma nakara yi bakince in kawota ba kuma gata nan ko kinga nakara yimata wani abun,

"bakayi ba amma ai kana shirn yi din ko yanzu ba taka ta naga kana kokarin yiba saboda tsabar mugunta ko to ka kyauta kayi daidai,

cike da jin kunyar kamasan da datayi yace nifa ba haka zan mata ba kawaide idon kine yagane miki haka yana gama fada ya juya zai bar wajen tace dawo kazo ka fita kasamo mata maganin zafi,

ummy ina dashi ai shi zanje in dauko ko kuma idan kingama gasa mata kawai ki kawota sai inshafa mata yayi maganar ahankali kamar gaske,

da dan mamaki ummy ta kalle sa amma ganin fuskar sa ba wata alama na rashin gaskiya sai taji dadi ta dauka yafara saukowa ne ya dauki fadan da tayj masa saikawai tace to shikenan bari in gasa mata amma de kasan bazan iya daukan taba kabari kawai ingama gasa mata sai kuje tare ka dauketa ka shafa mata nikuma sai inje in hado mata abun da zataci,

dawowa yayi falon ya samu kujera ya zauna yace to ummy ba komai gama matan sai mutafi,

nan ummy ta shiga gasa mata kafar ita kuma tana kuka dan da kyar ma tabari saida taji meer yace zai karba yagasa mata tasan halin sa sarai shiyasa tayj saurin tsayawa ummy ta fara gasa mata tun tana kuka har tafara yin shiru saboda taji dadin gashin ya ratsata taji damadaman kafar,

ana gamawa ummy tace yazo ya dauke ta tashi yayi kamar na kirki ya dauke ta yafara hawa saman benen da ita,

suna tafiya yana zabga mata harara ta gefen ido itade tunda ta fahimci hararar ta yake ta dauke kanta daga kansa ta kawar gefe,

saida ummy taga hawansu sanna ta bar falon ta nufi kitchen din dan ganin abun da zata dafa musu gaba dayan su saboda suma basu karya ba duk suna bacci,

yana shiga falon ya direta akasa yanzu bataji zafi ba kamar dazu dan haka kawai ta dafa bango ta tsaya tare da dan dage kafar me ciwon,,

gaba yayi abun sa batare da ya kulata ba ganin hakan yasa tafara binsa abaya har suka shiga dakin kan capet ya nuna mata yace ta zauna,

zama tayi tana tunanin Allah yasa kar yayi mata wata mugun tar wajen shafa mata dan bata yarda dashi ba wataƙil yayi hakane kawai dan yana gaban mahaifiyar sa,

tana zaune agun yaje ya ɗauko mayuka biyu ya dawo daga ɗan nesa da ita ya zauna sannan yace ta miƙar da ƙafar kamar abun arziƙi ta miƙar da ƙafar har ta ƙarasa inda yake aboniki ya yafara buɗewa sai ya laƙato ɗan kaɗan ya shafa shi ajikin murfin ya miƙa mata hannu tasa ta karɓa tana jiran jin me zaice sai yace ki shafashi a hannun ki kamar mai haka ta lakace shi daga murfin tasaka atafin hannun ta tafara murtsikawa da tagama sai ta ɗago ta kalle sa cikin ƙara haɗe rai baice mata komai ba sai ya ɗaoko wani kwalban na wani mai kuma ba man zafi bane kamar ma nml man shafawa shi ya lakato wajen kwatan roban ya dan ɓara mata akan ƙarfar sannan cike da mugun ta yafara danna mata ƙafar take ta saki ƙara bai saurareta ba harda cije baki wajen ƙara dannawa gashi ya riƙe ƙafar da ɗayan hannun ba dama ta kwace,

sosai ta shiga yin kuka tana kwace kwace zata kwace ƙafar amma takasa hawaye duk yagama wanke mata fuska harda majina gaba ɗaya fuskar tayi wani gaje gaje da ita,

batare da yasaki ƙafar ba ya ɗago kansa ya dubi yanda fuskar ta tayi, wani daɗi yaji aransa daman haka yakeso yagani dan haka sai yace idan kina so insakar miki ƙafa to kifara saka hannun ki ki goge hawayen nan kar inga ko ɗigon danshi akai,

Allah sarki baiwar Allah jin hakan yasa da sauri tashiga goge hawayen ta da hannun ta manta ta taɓa aboniki shikuma yana sane daman yayi mata haka shiyasa yafara bata ta shafa ahannu sannan yace ta goge fuskar ta dashi saboda idan ta goge hawayen man jiki zai taɓamata fuska gaba ɗaya ,

take tafara jin zafin abonikin a idon ta kif kifta idon tafara yi tun tana daurewa har taji ina abun yafi ƙarfin ta fuskar ta gaba ɗaya ta ɗauki zafi,

yana ganin haka ya tashi yaje ya rufe ƙofar harda saka key ajiki sannan ya koma kan kujera yayi zaman sa yana jinta tana kuka saima ya ɗauko wayar sa ya toshe kunnuwansa yana danne danne wayar sa,

ita kuwa idon ma ya rufe gaba ɗaya ga zafi ga hawaye sai abun ya haɗu ya caɓe mata ga ƙafar sai zugi take mata kamar zata cire haka take ji,

ji tayi ana buga ƙofar amma ba halin tashi ta buɗe saboda tanajin sa loƙacin da yasaka key ajiki kuma yama cire key ɗin daga jiki,

Ummy da tagaji da bugawa gafara kiran sunan sa hayatee ka buɗe ƙofar mana tana magana tana cigaba da bubbugawa amma baisan ma tanayi ba,

loƙaci zuwa liƙaci de yana ɗagowa ya dubeta yaga yanda take kuka sai ya kuma juyar da kansa ransa fari tass haka yake ji yasan zuwa yanzu zafin abun yafara barin ta saboda ɗaki akwai Ac, amma duk da haka ba yanzu zai kulata ba sai tagama gajiya dan kanta ta tashi tace zata fita sannan yayi mata gargaɗin idan tafaɗawa ummy wani abun sai yayi maganin ta,

ummy da tagaji da bugu hankalin ta gaba ɗaya yatashi tayi saurin ajiye try din da ta ɗauko abinci agefan ƙofar ta ajiye sannan tayi sauri ta sauka ta ɗauko wayar ta ta dawo bakin ƙofar sannan tadanna masa kira yana zaune yaga kiran ta ya shigo wayar fara tunanin abun da zaice mata ya shigayi bai ɗaga ba har kiran ga katse yana katsewa sai kawai ya tashi yaje ya buɗe ƙofar yana buɗewa ummy ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa me yafaru ina ta bugu baka buɗe ba na daɗe anan amma bakuji ba lafiya de ko? tayi maganar tana shigowa ciki gurin Ameesha taje da sauri tana yi mata sannu kallon fuskar ta tayi taga duk tayi jaa,

tana ɗagowa tunkan tayi magana meer yayi saurin cewa ina cikin shafa matane taje ta taɓa gurin bayan kuma nagama shine ta taɓa fuskarta da hannun tun ɗazu nake bata haƙuri taƙi yin shiru, sosai Ameesha tayi mamakin abun da yace amma bayanda zatayi bazata iya ƙaryatasa ba shiyasa tayi shiru kawai tana faman shashsheƙar kuka tare da sauke ajiyar zuciya akai akai,

kallon sa ummy tayi kamar de bata yarda da zancen sa ba amma sai kawai tace ayya sorry kiyi haƙuri ko awanke miki fuskar ko zaki fi jin dama dama,
kai ta ɗaga mata alamar eh,
to zaki iya takawa nan ma kai ta ɗaga mata amma aranta tasan bazata iyaba amma bataso tace bazata iyaba ace ya ɗauke ta daga nan kuma yasamu damar da zai ƙara yi mata wata mugun tar,
Chapter 83 · 0% Book details