← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 139

Sashe 41

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

wani irin kallo sam ya wulla masa da yasa shi yin shiru takawa yayi har inda yake yana kallon sa da kyau kafa yaɗaga ya dora akan tebur din nasa sannan yazuba masa idanun sa sannan yace kace me banjiba sai ka maimaita shiru mutumin yayi bai tanka masaba sauke qafar yayi ya daki teburin da qarfi tare da buga masa tsawa yace maimaita nace mu zaka gayawa maganar banza suwaye manyan naka tsuru yayi yakasa magana yana faman rarraba lokaci guda wata zufa ta fara tsatstsafo masa
dan matasawa yayi daga kusa dashi yaje inda ya tashi dazu wani abu yadaga sai ga qaramar waya agun zarota yayi yana nuna masa yadannan ta haske yakawo, ajiye masa ita yayi agabansa da kallo yabi wayar tare da miqewa tsaye yana zazzara idanu tare da kafe wayar da ido alamar kira yagani ajiki kuma kiran na tafiya sam ne yadanna wayar yasata a hands-free tare da dago tasa wayar itama yasaka ta a hands-free sannan ya karamasa ita akunne yace kagane ko har yanzu kana buqatar bayani?
Bossay ne yace ah in baigane ba ai sai ayi masa bayani yanda zaifi ganewa yana fada ya matso kuda shi tare da kifa masa wani gigitaccen mari baigama tantancewa ba yaqara bashi ta dayan barin yace yanzu kagane,
Adade baigane ba amma yanzu da aka mareshi kuma yaji duk muryoyin su acikin wayoyin yagane cewa sun ajiye masa waya tare da connecting din kira atakaicedai sunji wayar da yayi shiyasa suka dawo,
tsoro da furgici duk alokaci daya suka riskesa tunda yadafe kumatunsa baqara yarda ya dago ba gudun kar yaji wani ammafa aransa yana ayyana duk abunsu saidai suyi sugama amma bazai taba gaya musu ba duk abun da zasuyi mishi saidai suyi surabu dashi inkuma suka nemi suyi mishi hauka yanzu yasa akamasu adaure su agun,

bazato ba tsammani yaji wani irin duka ta tsakiyar kansa kamar an doka masa guduma da sauri yajuyo yana kallon sam da ya hade rai idonsa har sun fara canza kala cikin daga murya yace ya sunan shi kuma a ina zamu sameshi waye shi yafada yana tsatstsare sa da ido shiru ba amsa tsawa ya kuma daka masa yace waye shi zaka fada ko sai aikaka inda ba adawowa yafada tare da kaimasa shaqa kif kif yafara da ido shima cikin fakiya da daga murya yace bazan fada ba kuma kasake ni kasan matsayina anan gurin wallahi idan bakuyi wasaba duk sai nasa an kulle ku inga uban da zai kunceku kasakeni nace yaqarasa shima da yimasa tsawa yana rufe bakin sa ya kwasheshi da marin da saida yaga haske ya gifta cikin bacin rai yace kasaka inka isa nikuma sai nasa an qulle duka dangin ku ba kai kadai bama kaiwaye da har ka isa kayi min tsawa ko uwata bata min tsawa sai kai nace sai kai yaqara kai mishi naushi a kumatu na take bakin yafashe,

Amma duk da haka bakin bai mutu ba yaqara cewa kodan waye angaya maka dan babanka yana lauya zanji tsoron kane ko shi bafi qarfin in kulle shiba kuma bai isa yasa akulle niba ko akoreni daga aiki shi asuwa wallahi matsayin sa baikai nan ba yafada yana qoqarin fusge hannun sa daga riqon da yayi masa amma yakasa saboda ba qaramin riqo yayi masaba,
jin hakan yasa sam bayar da wayar kawai yahaushi da duka ta ko ina bossay ma ba abarsa abayaba haka yazo suka tarar masa suna duka suna dukansa suna yafadi gaskiya amma yace saidai su kasheshi amma bazai taba fada musu ba,
saida suka gaji dan kansu suka ga daku iya dakuwa yafita hayyacinsa dan har numafashin sama yafara daukewa sannan suka rabu dashi shettima yace tunda bazai fada ba kawai su tafi da wayar inyaso sai suje sucire sim din su duba number da yayi waya da ita last,
karkada masa kai sameer yayi sannan yace masa ai bazamu rabudashi ba mukai sa mota mutafi dashi duk sanda yagajida azabar da ake masa yafada kallon sa shettima yayi sannan yace kana ganin zasu barmu mufita dashi ahaka ai dole sai suntambayi ba'asi karmuje kuma suyi mana wani abun ma idan sukaga halin da yake ciki nide ina ganin kawai murabu da shi anan inyaso sai mudawo gobe sam kallon baka da hankali yayi masa sannan yace bakaji me yace bane bazai qara bari muhaduba kana ganin yanzu inmuka rabu dashi zamu qara kamasa ne bare kuma idan wancen yaji labarin munsan wannan qarya yake ai dole su qara canza wani daban kawai bets solution shine mutafi dashi inyaso sai mugano inda wancen yake takan wayar nan yafada yana nuna wayar hannun sa,
Shiru shettima yayi yana tunanin ta yanda za suyi sufita dashi daga gurin nan batare da kowa ya gansuba dan nufasawa yayi sannan yace kai yanzu to wacce shawarar ka yanke taya kake ganin zamu fita dashi batare da kowa yagani ba,

bai basa amsaba kawai suka ga yanufi hanyar fita saida yakai bakin qofa sannan yace musu kujirani ina zuwa bayan fitarsa da kamar minti hudu yadawo hannun sa roqi da wata baqar leda ajiyeta yayi agabansu sannan yadauki audiga ya gogewa wancen jinin da yadan bata masa fuska sannan wani abu aroba me kamar turare sai ya fesa masa shi afuska sannan ya zaro face mask yasaka masa sannan ya miqe yace ku kamo sa yatashi tsaye haka suka tasheshi tsaye kuma yatsaya da qafarsa idonsa abude yake amma kuma babu abun da yakeji kawaidai asama sama yakejin sa baisan ko shi waye ba komai zaiyi komai yakeyi shi mutum ne ko aljani oho,
Sam yace kusake shi zai iya zuwa da kansa kawai mubi bayansa kafin nan da minti biyu mu isa cikin mota in bahakaba kuma zai iya faduwa ahanya muyi sauri lokacin mu na tafiya dan tattare furin sukayi yanda baza agane anyi wani abuba sannan suka dauko wayar sa tare da kashe komai na office din na wuta sannan suka fita suka jawo office din tare da saka masa key suka cire key din suka tafi dashi,

suna fitowa mutanen dake waje suka fara binsu da kallo daya daga cikin su yace yallabai jiranka fa ake tundazu naga kuma zaka fita bossay ne yayi saurin bashi amsa dacewa yanzu zai dawo ba fita zaiyi ba ok dayan yace kawai dan baidamu da rashin amsawar yallabai din ba saboda baikawo komai aransaba tunda duk wanda yagan sa ba wanda zaice bashi bane ko kuma da abun da yake damunsa baya cikin hayyacin sa tunda ga fuskarsa nml idon sa abude gashi yana tafiya da qafarsa suna tafiya sam yana duba lokaci ahankali yace saura 59 second muyi sauri dan dudubawa sukayi suga ko ba mutane da sai suriqe hannun sa sujashi yanda zasu fiyin sauri amma suna juyawa sai suka ga idon yawancin mutanen akansu kamar ansan basu da gaskia,
Chapter 41 · 0% Book details