← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 139

Sashe 38

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hakannan yaji matar ta kwanta masa arai yaji yana sonta kuma yanaso yaga ta tashi lafiya qalau burinsa kenan kullum yana wajen ta bacci ne kawai yake rabasa da ita shima kuma saboda ummyn sa na hanasa amma da anan zai ringa kwana zuwa lokacin kuwa kowa yafara samun freedom saboda befiya bi takan lamuran suba ita kadai ce agabansa aikin ma yanzu ba sosai yake gudanar dashi ba indai kaga yayi maka fada to kataba tane ko kataba abun da ya shafi lafiyar ta nanne zaka ga bacin ransa inma takama da duka yayi maka,

"ahaka yaci gaba da kula da ita tundaga wannan lokacin harzuwa yanzu da yakama shekara kusan biyar kenan yana abu daya akanta,

Wannan kenan ina fatan kun fahimta inma baku fahimta ba zakufi fahimta nan gaba........✍️✍️✍️
[5/24, 9:35 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

        💅 💅💅💅💅💅
💅SARKI SAMEER......💅
             (wasa farin girki)
             💅💅💅💅💅💅💅💅💅

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿35&36

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

*cikin masarauta*

     "yanda sukayi mata runfa bayan hasken yadawo baqin yagama daukewa suka fara matsawa daga gurin ta,

"sameer ne ya dauketa batare da yace komai ba yayi gaba sukuma suka rufa masa baya yana tafiya suna binsa abaya part din momma dinsa ya nufa da ita har suka qarasa ko nocking beyi ba ya tura qofar ya shiga kai tsaye ya kaita kan kujera ya kwantar da ita tare da cewa mikon ruwa,
"shettima ya nufi kan dinning yadalo ruwa marar sanyi ya kawo masa karba yayi ya yayyafa mata ajiyar zuciya ta sauke tana bude idon ta abun da yafaru yafado mata atai da sauri tajawo hannun sa  tare da qamqameshi duk tabi ta fita hayyacin ta can kuma tasaki kuka kawai tsayawa yayi yana kallon ta batare da yace ko uffan ba,

"bossay ne yamatso kusa da ita yace ke kikwantar da hankalin ki babu komai jin muryar bossay yasa tayi saurin sakin sameer ta koma kansa tace mutafi dan Allah mutafi wallahi bazan zauna ba nidai mutafi gida mutafi gida nidai gurin dadda ta zani kaini gurin ta dan Allah ka kaini tana magana tana kuka gashi tabi ta ririqeshi qoqari yake yarabata da jikin sa amma yakasa cikin sigar rarrashi yace ya isa haka to kiyi shiru ki sakeni sai mutafi kinji sakeni nace mutafi makale kafada tayi ita sai yatashi suntafi sai wani kukan take saki,

sameer da yaji ta isheshi ya daka mata tsawa dacewa dalla malama kiyiwa mutane shiru ki nutsu yafada yana kai hannun sa kanta zai cireta daga jikin bossay din,
momma dake saukowa daga step din stairs tun shigowarsu tana kallon su saboda itama tana falon abun da yafarune yasata tashi ta koma daki ba shiri yanzu kuma da taji komai yayi shiru yasata fitowa dan tambayar yan waje abun dake faruwa sai kuma tace karo dasu,

Qarasowa tayi  tace rabu daita ya isa haka tafada tana kamo hannun ta tace zonan "yata rabu dasu daina kukan sai amaida ke gidan ko kai tadaga tare da dagowa tana kallon matar hakan nan taji bazata iyayiwa matar musuba sabosa kwarjinin da tayi mata sakin bossay tayi tare da komawa kusa da momma kamota momma tayi da kyau ta rungume ta lokaci guda Ameesha ta sauke ajiyar zuciya tare da tsayar da kukan da take bakajin kukanta saidai 'yar shashsheqar da takeyi kadan kadan momma bata saketaba har saida taji tayi lufff ajikin sannan ta dagota tana kallon ta yarinyar taji hakannan ta kwanta mata arai sai take ganin ta kamar su Amra,

"goge mata hawayen da suka bata mata fuska tayi sannan ta dawo da ita gefen ta tana kallon ta batayi mata magana ba sai ta maida dubanta ga su sam da duk sun tsaya suna kallon ikon Allah,

"wannan abunne ya tsora tata ko shettima ne yace eh wlh har suma ma tayi cike da alamun damuwa afuskarta tace ai dole ta suma wannan abu da babu dadin ji ai nima kaina nakusan suman dan na tsorata da wannan abun,
"Shettima yace momma ai inaga dama ba kya waje awaje yafi qara muna fitowa daga mota fa mukaji abun mamakin ma kiga yanda wajen yayi baki gaba daya abun abun maamaki wallahi,

"Momma tace nagani mana ai duhun gaba dayane dan har daki watakil ko gaba daya duniyar ce al amarin ubangiji kuma shikadai yabarwa kansa sanin manufar wannan abun,
"sam ne yace momma wanna fa a bun alamar tambaya dan iya cikin masarauta ne babu awaje yanzu na tambaya mukadai ne hakan tafaru damu,
da mamaki momma take kallon sa tace iya nan kuma? cike da tabbatarwa yace mata eh amma momma hakan be taba faruwa ba ko abaya cen? tace bai taba wallahi yau nafara jinsa amma bari intambayi papa inji ko hakan ya taba faruwa atarihin masarautar nan dan abun abun adubane,

"Sam yace gaskiya momma wanna fa babbar matsalace ni tunda nake bantaba jin irin wannan qarar ba qarin mamakin kuma ace gari da haske amma cikin nan yakoma duhu daga baya kuma yayi haske,

shettima ma yace nimade gaakiya abun ya tsorata ni harmafa da kururuwa kamar mutane kamar a horow film dannidai anan nataba jina makamancin irin wannan  sai gashi kuma yafaru a gaske a gasken ma acikin gidan nana gaskiya da wani abun da yafaru acikin masarautar nan yakamata abincika,

momma tace maganar ka gaskiyace amma ai nasan tunda bamu kadai muka jiba nasan dole za ayi zama akan hakan tunda wannan ba abune da kasaba jiba gashi kuma kunce a iya nanne ni wallahi duk azatona gaba daya duniyar ce tayi haka,
hakade suka cigaba da tattaunawa akan wannan babban ala'amarin da yafaru dasu,
"Bossay  dai baisaka musu baki ba tunda wannan abune na family be kanata ya tsoma musu baki ba duk da daman shi ransa fal yake da tambayoyin ganin wannan abun da baitaba gani ba yazata ko su sunsaba ko kuma sunsan dashi amma jin tattaunawar su yasamu amsar tambayoyin su saikawai yaja bakin sa yayi shiru bashida tacewa kawaidai yana mamakin hakan,
Ameesha ma bata saka nata ba amma de har yanzu a tsorace take jikin ta sai bari takeyi taciki so take ta tashi taje gurin bossay tace masa su tafi amma momma ta hanata damar hakan saboda suk maganar dasuke hannuta riqe yake da nata shiyasa baza ta iya tashiba kodan kwarjinin matar,

"bayan sungama maganar ne momma taqara dubansu "tace wanna fa daga ina tafada tana kallon ko qanwar wannance duk da shima de yau nafara ganinsa bansan ku tare ba taqarasa maganar  tana nuna bossay sai lokacin bossay yadan sunkuyar dakai tare sa gaida ita amsawa tayi tare da cewa munhau wata hirar bamu gaisaba ko dan murmushi yayi kawai batare da yace komai ba,

"duk shiru sukayi saboda basusan ta inda zasu fara yimata bayani ba,
"saida taqara nanata musu tambayar sannan sam yace momma not enough time in mundawo  zan miki bayani yanzu zata zauna daku zuwa dare zaizo su tafi tare,
"tace to shikenan Allah ya kaimu ai yanzuma su sweetheart zasu dawo  daga makaranta taqarasa fada tana juyawa ta kalli Ameesha dake ta faman rarraba ido duk jinta take atakure takasa sakin jikin ta amma yanzu ta dena jin rawar da jikin ta yake mata,

tanaji tana gani sukayi sallama da momma suka fita jitake kamar ta bisu amma ba halin dole ta hakura ta zauna,

lokacin da suka fita,"cikin masarauta an cika dam da mutane kowa yafito Dan jin me yafaru yau amasarauta duk inda ka kalla mutanene a cure suna maida yanda akayi kowa nafadar albarka cin bakinsa,

ahaka suka ratsa ta suka shige mota duk da mutane sai kallon su suke suna Jira suji ko zasuce musu wani abun amma shiru har suka shiga motarsu suka fice suka barsu," sukuma suka cigaba daga inda suka tsaya,

"duk yanda momma taso Ameesha tasake da ita amma taqi saima qara nannadewa datakeyi ita kadai taqi sakin jiki da ita ko kallon tama batayi,
datagaji da ita taga bazata sake ba sai tayi tunanin ko saboda itane yasa taqi sakewa sai kawai tace ta tashi ba musu kwa tayi saurin tashi tsaye itma tashi tayi tare da kama hannun suka hau sama ta kaita dakin su amra again ta watakil tafi sakewa idan taga ita kadaice shiyasa ta kaita tare da cemata ta zauna bari akawo mata abun da zataci kafin su dawo kada mata kai kawai taga mata batare da tace komai ba guri tasamu ta zauna aqasan carpet dinsu bayan fitar momma tashi bin dakin da kallo dakin ya burgeta sosai ba wani tarkace Kuma wai Ahaka dakin Yara ne dama ace nata ne da tafi kowa farin ciki gadon su ta kalla sai ta tuna nasu dakin da katifar na kamar carpet din dakin nasu amma su ga qatuwar katifa gashi kuma harda gado tunawa tayi itakan tunds take inba gadon asibiti ba sai kuma ranar da ta kwana akan agidan su shettima dan jiyama qin kwana tayi akan gadon hajiya sai aqasa ta kwanta wai bazata iya kwana da itaba gado daya bayan ba ayi da itaba amma taqi haka aka rabu da ita ta kwana aqasa to bayan haka bata taba kwana akan gado ba Koda na qarfe ne hannun ta daga ta shafa gadon sai kawai ta saki murmushi komai ta tuna oho daya bayan daya taringa kallon komai na dakin tana cikin hakane wata tashigo dakin da try din abinci ahannuta tare da sakin fuska ta qaraso inda take tare da zama akusa da ita, kwanukan ta shiga budewa sannan ta tura mata gabanta kayan fruit ne aciki anyanyan ka mata su tace maza kici ba musu kwa domin kayan marmarin sun burgeta shiyasa ta ci Saida ta cinyesu tas sannan ta ture kwanan, kallon tayi cike da mamakin cinyewar da tayi,
Chapter 38 · 0% Book details