← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 139

Sashe 78

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda safe su sameer suka haɗa kansu alahamdullillh jikin bossay da sauƙi yana tashi yajishi garau saidai kuma tunda safe Sameer yace ya kashe wayarsa shima kuma daman tunanin hakan yake dan yasan dole akira shi daga gida kuma yasan halin dadda tunda tace sai anhaɗa ta da Ameesha tofa yau saita Allah dan haka gwara ta kira layin sa taji akashe ammade bata ɗaga musu hankali ba kuma batasan inda suke ba dan haka dole tayi haƙuri tabari har sai ya koma gida hakan sai ya fiye masa kwanciyar hankali,

Wajen ƙarfe goma da rabi suka fita daga gidan gaba ɗayan su harsu hamra da Ammar,

acikin mota hamra ta ƙara basu labarin motar da tagani ɗazu da safe gaba ɗayan su sunyi mamaki amma wasu daga cikinsu basu yarda ba,

Sameer ne yace amma meyasa baki faɗa mana ba tun kan mufito daga gida shiru tayi bata basu amsa ba,

shettima ne ke tuƙi dan haka daman basuyi nisa da fitowa ba sameer ya kalle sa yace mu koma gida,

shettima ya kalle sa yace mukoma fa kace yaza ayi mukoma bayan mun kusa ƙarasawa ai ni ina ganin gwara mufara zuwa can kar su rigamu zuwa suje suyi wani ƙulla ƙulan nasu mukasa samun wata sheda ko ɗaya inyaso wanann me sauƙi ne idan mun dawo gida mayi duk abun da zayi saboda mutum ɗaya zamu riƙa me gadi tunda ya buɗe musu ƙofa suka shigo kuma suka fita ai dole yasan ko suwaye suka fita nidai ina ganin gwara mufara zuwa ɗin tunda wannan bama mu da tabbas kasande halin Amra da shiriri ta wataƙil ma wata motar ta gani ta zata waccen ce amma in ba hakaba me zai kawo motar cikin gidan nan batare da sanin kowa ba indai har ta shigo koma waye ya shigo ai ansan dashigowar sa,

gaskiya ne maganar ka hakan yakamata mufara yi kaga idan mugano wani abun sai nufi tabbatar wa saboda muna da hujja a hannun cewar bossay da haka suka yarda kowa yayi na'am da maganar akan sai sun dawo sai kuma a tambayi me gadi....

        **********************

tunda asuba dadda take nacin sai ankira mata bossay amma ankira wayar taƙi shiga dan haka tasakasu agaba sai anfito mata da jikarta dan Wallahi baza ta yarda ba idan ba da rashin gaskiya ba a al'amarin me yasa zai kashe wayar sa saboda yaji tace sai taga jikarta yau shine yaƙi dawowa kuma ya kashe wayar sa saboda yasan basu da gaskiya,

Sude su Ammi sun rasa yanda zasuyi da ita sunyi iya bakin ƙoƙarin su wajen sun ganar da ita amma ta rufe ido taƙi sauraron kowa dan haka kuwa kowa yarabu da ita kowa yaci gaba da sabgar gaban sa,

dadda da taga haka sai ta koma ɗaki ta ɗauko mayafin ta da ɗan canjin da take dasu ta fito falo tana shirin fita daga gidan Ammi ta fita daga kitchen da sauri ta ƙaraso wajen tana cewa dadda yanzu fisabilillahi bazakiji maganar da muke miki ba meyasa kikeyin haka waɗan nan mutanen ba mayaudara bane bazasu taɓa cutar da Ameesha ba amma kinƙi sauraron kowa yanzu dakike niyar fita kinsan inda take ne ina zakije,

Kinga Aminatu nifa wallahi babu wanda ya isa ya rabani da jikata wallahi sai naje sun fito min da ita idan kuma sun kasheta ne saidai hukuma ta rabani da su idan ku kun kasa ni zanje da kaina bade ance ɗan sarkin garin nan bane to ai matambayi baya ɓata zanje har gidan sarkin insanar dashi abun dake faruwa asan yanda za ayi a fito min da jikata dan bazan juri rashin ta ba wallahi bazan taɓa lamin taba akan duk wanda ya taɓamin jika yarinya marainiyar Allah amma anbi an takurawa rayuwar ta anrabata da iyayen ta shine itama sai anga bayan ta so na kuɓuta daga sharrin waɗan cen su basu kasheta sai sune zasuzo har gida su ci amanata ingama basu labarin ta amma memakon su tausayawa rayuwar baiwar Allah amma sai sunemi suci zarafin ta su kasheta to duk ma wanda ya aikata mata hakan wallahi idan mafarkin nan ya zama gaskiya sai inda ƙarfina ya ƙare ko zan rasa komai arayuwata sai na ƙwatar mata ƴanci sai wallahi sai duniya tasan abun da akayi mata dan haka koyi haƙuri kibarni dan bazan taɓa sauraron duk abun da zakice min ba nasan ke mutuniyar kirkice amma daman ance ka haifi ɗa baka haifi halin saba bazan iya yabon ɗanki ba akan basa hannun sa aciki ba tunda har dashi nagani amafarki kuma ga alama nagani da yaƙi dawowa kuma yakashe wayar sa kinga kwa dole inyi zarginsa kiyi haƙuri idan kinji haushina akan zargin da nayi masa saduwar alkhari nagode da mutuncin da kiakyi min bazan taɓa matawa dake ba arayuwata kingama yimin komai kuma nayarda dake dan haka natafi kuma ba lalle indawo cikin gidan nan ba koda ace naganta to zan ɗauketa ne muyi nesa da garin nan shiyasa daman tunfarko bana son inhaɗa mu amala da kowa saboda gudun matsala irin wannan tana gama faɗar haka ta share hawayen da ya zubo mata tare da rungume Ammi sannan ta ra jikin ta da nata sannan tayi saurin juyawa ta fice daga gidan tana share hawayen ta,

mutuwar tsaye Ammi tayi bata taɓa tunanin dadda zatayi mata haka ba yanzu tana nufin ta tafi kenan baza ta dawo cikin gidan ba me yasa dadda zatayi mata haka me yasa dadda bata jin magana,

jiri taji yana niyar ɗinbanta da sauri tayi saurin dafe bang,

tunanjn me ya hana bossay dawowa gida da kuma kashe wayar da tayine ya tsaya mata arai ga kuna abubuwan da dadda ta fada tana cikin tunane tunanen naji zubar hawaye akan kumatun ta hannu tasa ta share tana me jin quna acikin zuciyar ta wani abune yazo ya tokare mata arai jitake kamar ta dora hannun akai ta kurma ihu haka take ji,

jitayi andafata da sauri ta dago duk atunanin ta ko dadda ce tadawo hada ido sukayi da farouk cikin sanyin murya yace Ammmi me yafaru naga kina kuka kasa bashi amsa tayi saboda wani kukan da taji yana shirin tahomata,

rungumeta yayi yana bata hakuri da kyar ta iya cewa farouk dadda ta tafi ta tafi ta barmu tace bazata dawo ba, ta qarasa maganar cikin matsanaciyar damuwa,

da sauri ya raba jikin sa da nata shima cikin damuwa kamar zaiyi kuka yace Ammi me yasa kika barta ta tafi Ammi zata iya fadawa wani halin fa tun yaushe ta tafi Ammi kikara kiran yaya ko zai dauka kiji ina yake kinji Ammi duk yabi ya rikice sai faman jero mata tambaya yake jero mata,

riqo hannun sa tayi tace kwantar da hankin ka in sha Allah babu abun da zai sameta kuma in Allah ya yarda zatadawo kar kasaka kanka adamuwa Allah sarki uwa ganin yafita shiga damuwa yasa itama kwantar da damuwarta dan taga ta cire shi daga damuwa haka taita rarrashin sa har yasauko amma gaba dayansu ba sukuni agaresu kowa yayi jigum jigum abun duniya ya ishesu......,

************************

Su sam suna karasawa wajen mall din suka fito gaba dayan su suka shiga ciki inda suka nemi ayi musu iso ga managen gurin ba bata lokaci kuwa aka kaisu har office din sa sameer da bossay ne da shettima kadai suka shiga sukuma suka tsaya daga bakin kofar,

bayan sun shiga sun gaggaisa da managen suke sanar dashi abun da ya kawo su atake shima hankalinsa ya tashi yashiga basu hakuri sannan akace aduba cctv camera din na jiya ko za aga wata alama nan ya shiga duba computer din dake gabansa bincike ya shigayi da ido sameer yayi wa bossay alamar yaje ya duba shima bossay ya zagaya ta bayan sa yana ganin dubawara da yake yi daga bayama gaba dayan sune sukaje suka tsaya suna kallon videon tundaga safe har zuwa yamma aka nuno lokacin da suka shigo gurin aikam suna tsayawa da motar su sai ga wata motar ta tsaya daga bayan su,

anan sam yasa aka saka pause sannan akace su Ammar su shigo suna shogowa aka nunawa Amra akace itace motar da sauri tace eh wallahi itace kuma itace dazu ta fito daga gida wallahi nagane ta itace,

play aka saka videon da suke kalla yaci gaba da tafiya saida babu wanda yafito daga motar...

cigaba da kalla sukayi har lokacin da su hamra suka fito tabbas tare suka fito saidai kuma abun mamakin suna fitowa kuma sai camera din ta dauke gaba daya ashe tundafa lokacin ma bata kara aiki ba har sai washe gari taci gaba da aiki,

gaba dayan su dagowa sukayi aka shiga kallon kallo gaba dayan su sun kasa magana,

managen gurin ne yayi karfin halin cewa to kungade abun da yafaru ni kaina ma bansan da hakan ba bansan ya akai hakan ta faru ba amma de kuyi hakuri kuje zuwa gobe insha Allah zan bincika ahankali har ingano inda aka samu matsar bazai yiyi muyi yanzu ba saboda idan nace za ayi to za aja hankalin customers kuma baza asamu ma'aikata ba dole sai zuwa dare zan tara su gaba daya sai aduba daga ina matsar take kuyi hakuri amma in Allah ya yarda kar kudamu zanyi kokarin gano muku zan kira wani abokina shi zaifi dubamin abun dake faruwa dan zai iya sawa ma gurin haske aga koma menen awajen kar kudamu da wannan,

Sai yanzu duk suka samu bakin magana kowa na tofa albarkacin bakin sa game lamarin amma basu tashi hankalin suba tunawa da inda Amra tace taga motar sunsan bazasu sha wahalar bainceke ba da zarar sunje gida suna ganin komai ya daidaita,

dan haka ba bata lokaci suka kara kwasar jiki suka nufi hanyar gida suna tafiya suna hirar jefi jefi ahaka har suka karasa unguwar suka nufi masarauta suna shiga gate na farko da yake abude koda yaushe sun nufi gate nabiyu da zai sadaka da cikin masarautar bossay dake tuke yayi saurin taka burki da mamaki duk suke kallon sa shettima yace ya akai lafiya de ko da hannun yayi musu alamar bakin gate din masarautar kallon sa yayi yace me fa yafada cike da rashin fahimta,
Chapter 78 · 0% Book details