← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 139

Sashe 56

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abune yadafa su gaba ɗayan su yashiga rarrashin su sannan ya kamo hannusu yamaida su kan kujera ya zaunar dasu saidai yana zaunar dasu ma'ana(sabreena) ta ƙara miƙewa tsaye tare da cewa nifa bazan ƙara zama ako ina ba ayau nake so zuwa kano duk dare agarin Kano nake son kwana dan inbagani acan ba zuciya ta bazata taɓa samun kwanciyar hankali ba dan haka kawai kubarni intafi nagode da kulawar da kuka bani da kuma irin taimakon da kukayi min bazan taba mantawa daku ba Allah yabiyaku da mafificin alkhairi nasan kungama yimin komai badan kuba da tuni wani zance ake ba wannan da tuni ina nan akwance kamar yanda sukeso su taganin na ahaka,
dan haka dan Allah kurabudani in tafi ko nasamu sauƙin abun da nakeji idan naje a aiwatar da ƙudurina,
yanzu zan tafi Allah yabar yabiyaku idan komai ya tafi yanda nake so har nan zan kawo muku ƴaƴana kugansu zan kawo muku ziyara dan bazan taɓa mantawa daku ba acikin rayuwata kuɗin na musamman ne agareni nabaku wani gurbi acikin raina domin kuntaka muhimmiyar rawa acikin rayuwata duk godiyar da zanyi muku bazan taɓa biyanku taimakon da kukayi min,
ni zan wuce Allah yaƙaddara saduwar mu tafaɗa tana ƙara miƙewa tsaye da sauri ummy tayi saurin dafa kafaɗunta ta tace dan Allah kaikitafi kibarmu kibari mutafi tare muma bamason kiyi mana nisa duk inda zaki munata tare dake zamu biki tayi maganar ta ƙokarin ganin ta zauna amma bata zauna ba taci gaba datsayiyuwa batare da ta tafi ba......✍️

                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(mrs bmb)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

[6/9, 10:08 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️53&54

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

    "Abu ne ya fara yi mata magana cikin  sanyin murya yafara cewa baiwar Allah kiyi haƙuri banga lafinki ba nahakan amma de zakai kiyi haƙuri abi komai asannu baikamata kije ahakaba kibari sai mun fara bincike kafin kije cikin gidan tunda kikaga haka tofa ba ƙaramin abune me sauƙi gurin gano koma waya yi miki haka Yakamata mufara zama ayi nazari akan  waɗanda kuke mu'amala dasu da kuma abun da yataɓata shiga tsakanin ku na saɓani ko makaman ci haka ko kuma faɗa dade sauran abun da ba arasa na zamantakewar yau da kullum wannan ce hanya me sauƙi kawai wajen gano wanda ya aikata miki hakan amma garaje da sauri duk bana mubane sai munbi komai asannu amma dan Allah ki ajiye batun tafiya ke kadai kibari tare zamu tafi sai mufara binciken ko ya kikace shiru yayi yana jiran jin amsarta

" shiru tayi tana nazarin maganganun sa kafin daga bisani ta kalle sa sannan tace naji bayanin ka kuma hakan yakamata ayi banyi Wannan tunani kwata kwata idona ya rufe tabbas bincike yakamata infarayi kafin su san da inaraye dan nasan yanzu gaba ɗayan su babu wanda baiyi tunanin na mutu ba mugaye kawai wallahi inna tuna abun da sukayi min sai naji kamar yanzu inganni agaban su in caccaka musu wuƙa musamman ma idan na tuna raba ni da ƴaƴana da sukayi tsakanina dasu saidai Allah ya isa Allah ya tona asirin su, "Ameen duk suka amsa mata dashi"   bayan tayi shiru ta cigaba da cewa  ammade kuyi hakuri bazan iya zaman nan ba zantafi kano acan zan zauna inyaso duk abun da zanyi nayi acan,
  "ummy tace ai ba matsala duk sai mukoma can din amma to idan munje a ina zamu sauka?
   Abu yaya saurin tarar numfashin ta kafin maama tayi magana yace habade gurin zama ai bazai mana wahala ba akwai wani abokina acan sai insakashi ya samo mana gida asaka duk abun da ake buƙata sai kawai mukoma gabaɗayan mu,
    "Nifa yau nake son tafiya maama taƙara gaya musu,

   "Abu ne ya bata amsa da cewa maama yanzu fa babu loƙaci kinga la'asr ta wuce magariba ake shirin yi kafin muce munje ai dare zaiyi mana kuma kinga ko gidan da zamu zauna ba asamu ba idan munje ina zamu sauka acikin dare, kiyi haƙuri kibari ko nan da jibi ko gata sai mutafi San  anshirya komai atsanake,

   batare da ta tanka masa ba ta juyar dakai tayi irin alamun nifa ko me zakuce bazan yarda ba,

  jin shirun nata yasa Ummy ƙara bata baki akan tabari din sa tafi nan da jibin ko gata, amma itama tace a'a itafa bataso ta kwana ako ina inba Kano ba batason ta ƙara kwana awani wajen sai acan garin,

duk yanda zasuyi mata bayani ta fahimta tabari din amma taƙi aminta tace ko ita kaɗai ce su rabu da ita ta tafi idan yaso su sako duk sanda suka shirya,

    "meer ne yasaka baki shima ya gwada sa'arsa yace dan Allah kekwa kibari mana ko zuwa gobe amma yanzu kafin kije dare zaiyi sosai ga hanya bata da kyau sai kinke ansace ki  ahanya kinga ba ke ba daukar fansa kuma bazaki ga ƴaƴan naki dakikeso kigani ba,
amma inbaki yarda ba   ga hanya nan inkinfi so a kwamishi ki sai ki tafi saidai muce ki gaida waɗanda suka kwamishe ki dan ba inda zamu,

    "zazzara ido ta shiga ys tana tunanin maganar sa to kode da gaske yake kai kumafa hakan zata iya faruwa asace tadin koma aje idan ansace ta din aje akasheta ma gaba ɗaya kai inaa tafasa tafiya saboda maganar gaskiya ta yarda da maganar sa kuma tana tsoron hakan,

   "dan murmushi Abu yasaki irin nasu na manya, yana ɗan satar kallon ganin yanda tayi zuru zuru da ita alamar tsoro, fakar idon ta yayi ya kalli meer tare da daga masa gira sannan yayi masa alama da hannu da yacigaba da abun da yake ma'ana yaci gaba da tsoratar da ita ɗin,
  dan ya fahimci wannan tsohuwar taurin kai zatai baza a iya lankwasa ta  sauƙin rai ba dole sai da dabara,

  "Meer yacigaba da cewa Ni wallahi ma kitaso in rakaki ki hau mota amma mu fara yin sallamar bankwana dan nasan bazamu ƙara haɗuwa ba saidai muce Allah ya jiƙanki dan kamar sunan ki gawa suna daukarki zasuje suyi romon ki abawa dodo jinin ki ya shanye shikenan ke kuma saidai idan munzauan muce Allah sarki baiwar Allah nan da muka taɓa haɗuwa da ita ansace ta akan hanyar ta ta tafiya daukar fansa da take ƙudirin yi,

  "dan Allah yaro wai da gaske kake tafaɗa cikin nuna tsoron ta afili kai yaɗaga mata tare da cewa gasu Ummy ki tambaye su kiji idanni kin ƙarya ta ni idan kikaji daga bakin su sai kifi yarda tunda ni kin maidani maƙarya ci yanzu.... kaga ni rufe min baki da jawowa mutane bala'i fayaƙu khairan au liyasmut(kafaɗi alkhairi ko kai shiru),

   da haka suka ci gaba da tsoratar da ita gaba ɗayan su babu wanda bai faɗi albarkacin bakin sa ba wajen tsoratar da ita ɗin aikam kuma sun ci nasara dan ta tsorata kam ba ƙarya amma fa duk da haka bata ce musu tayarda zata zauna ɗin ba,

saida suka sha wahala kafin ta amince musu shima kuma zuwa gobe da safe suka ce mata sun yarda da hakan,

bayan da suka iya dole suka fara shirye shiryen tafiya kano gobe,
  tun aloƙacin batare da kowa ya tafi ba Abu yakira abokin nasa yasanar masa buƙatar sa ya kuma tabbatar masa da zuwa gobe yake son komai ya kammala, abokin nasa ya amsa masa da angama bashida matsala za'asamu ko yau yake so zaiyi ƙoƙari yasa asamomu su,   nande yayi masa godiya sannan sukayi sallama,
anan sukaci gaba da zama har aka kira sallar magariba sannan suka tashi Abu da meer suka ta tashi suka tafi masallaci ita kuma Ummy ta kai maama dakin da ta kaita ɗazu tana nuna mata de komai sannan ta fita itama dan gabatar da tata sallar,

                *Kano*
*___S&S__ sam&sumy

    "kiran sallar magariba ne ya farkar dashi daga baccin da ya daukeshi ba shiri,
  ahankali ya shiga buɗe idonsa bai tun yana ganin dishi dishi har ya ware su amma baigama tantance a inda yake ba, dan yana budesu yaƙara rufesu tare da ɗaga hannayensa zaiyi  miƙa dan yama manta a inda yake yana ɗaga hannu sai ya bude idon sa basu sauka ako ina ba  sai suka sauka akanta da take kwance kan cinyar sa bacci yasa daga kan kafaɗar sa ta dawo kan cinyar sa baccin ta take hankali ta kwance kamar tana ɗakin uwarta..
Chapter 56 · 0% Book details