← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 139

Sashe 48

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

janye hannun sa sam yayi daga dafan sa dayayi sannan ya miqe tare da juyowa yana fuskantar su da kyau sosai maganganun shettima sukayi tasiri a zuciyarsa sai yanemi duk wani bacin ran ma yarasa, saima wani irin kwarin gwaiwa da yaji yazo masa,
maganar ka gaskiya ne yanzu tunda ancire sim din sannan wayar ta fashe dan haka jefar da ita zamuyi sannan yanzu mu koma gurin shi ayau sai yagaya mana inda yake,
Shettima yace " kana ganin zai gaya maka batare da anyi masa baranar dangin saba yakamata muafara bincike akansa mugano wani wanda yafi kusa dashi wanda idan aka tabasa zaiji aransa da har zaisakashi yagaya mana gaskiya, kawai muyi binciken yau inyaso sai mukoma gurin nasa koda zuwa gobe ne ina ganin hakan sai yafimana sauqi amma bana tunanin hakan nan zai fada mana dole sai munbi ta shawarar da ka kawomana tun dazu,
Shiru yayi bece masa komai ba sai kuma yace hakan zamuyi yafada cike da qarfin gwaiwa sannan ya koma kan kujerar yazauna tare da miqa hannu ya karbi sim din dake hannun shettima,
a flash yasaka sim din ya zura ajikin system din sannan yafara aikin sa bai wani dauki lokaci me tsawo ba ya tashi tsaye tare da cewa yess yafada da qarfi yana kallon su cike da jin dadin abun da yace da kuma ganin yanayin sa da ya tabbatar musu da anyi nasara kenan,
bani wayar ka yafada yana kallon bossay da sauri bossay ya miqa masa copying din wata number yayi aciki sannan yace ka ajiye mana wannan number kayi saving dinta bayan yabasa ya karbi ta shettima ma itama wata number yayi copy ya miqa masa yace shima yayi saving sannan ya qara dauko tashi wayar yayi copy,
  number suwa kagano? shettima ya tambayeshhi ,

  "naduba naga numbers din  da yafi yawan  waya da su  naga  ansaka my wife  itace nabawa bossay yafada yana nuna bossay,

tabiyu kuma ta mahaifiyar sa ce ita nabaka,      "ni kuma ta daughter din sa nadauka  kuma ina kyautata zaton duk sune dan haka yanzu su zamubi didigi mugano inda suke da zama  amma zamu rabune saboda naga kamar  duk ba aguri daya suke zaune ba,

bossay " yace amma aganina ai bama sai anbi diddigiba kawai kiran su zamuyi awaya? yafada yana kallon,
harar sa shettima yayi yace idan ka kirasu din kana da abun da zakace musu da zaisa suyi maka kwatancen inda suke ne ae dole sai munbi mungano da kanmu,
dan nufasawa yayi sannan yace zamu iya sani wallahi amma basu zamu fara nema ba iyarinyar zamu fara nema ko ba budurwa bace yafada yana kallon sameer,
dage kafada sameer yayi alamun shima baisani ba,
hakan kuma yayi maganar ka abun dubawa ce nasan ma dole budurwace amma de sai nake ganin tunda batare suke ba ai kamar bazamu iya snin inda sauran suke ba, bossay yace to ai ko ita muka kama shikenan zamu iya yimasa barazana da ita amma ya kuke gani,
  "aa bazamu bi ta wannan hanyar ba kawaidai yanzu abar batun sauran yanzu muje tare har inda yarinyar take sai mubi location inyaso idan yaganta kuma yaqi saduda sai mukamo sauran,
duk sunyu ns'am da shawarar tasa dan haka ba bata lokaci suka tattara inasu insau suka fita daga office parking sapace suka zo kamar yanda sukazo dazu yanzuma haka sukayi bossay ne zaija motar, bayan sungama shiga gabadayan su yaja motar da gudu me gadi ya bude musu gate din ya kwasheta aguje suka fita daga hospital din,
wayar yadauko ya kunna location din number nan yafara nuna musu hanya tun yanacewa bossay ga inda zaiyi daga qarshe kuma sai kawai ya miqa masa wayar gabansa bayan sunzo unguwar da take(unguwar sharada) wani layi suka shiga sannan suka qara yin kwana adaidai wani gida suka tsaya inda abun ya nuna musu parking sukayj abakin gidan sannan bossay yace "to ya za ayi kiranra za ayi awayar ko kuma turawa za ayi akirata?
  "shettima yace habade saidai akirata awayar kawai sai yafi,
   kana da abun da zakace mata idan kakirata din har inama kana dashi to idan tafito baizama lalle tayarda damuba saboda batasan muba bata taba ganin muba kawai yanzu wani acikin ku  yafita yaje yasa me gadi yakirata,
ko kai bossay kaje saika san yanda zakayi ka jawo hankalin ta har ta yarda tashiga mota,    mukuma fita zamuyi daga motar mujiraku abakin kwanar cen idan kun fito sai ka dauke mu mutafi,

"a'a wallahi bani yakamata naje ba kai yafi kamata nasan dole intaganka zaka iyayi mata kwarjini kuma sai tafi yarda dakai bazata iyayi maka musu ba tana ganin ka handsome din nan ai da gudu zata amince dakai bai rufe baki ba shettima ma yace gaskiya ne wallahi kai zakaje bazata taba bijere maka ba kawai kaje ayi awuce gurin dan nasan kafin ma kace ta shiga zata shiga saboda qaramin  tafiya da imanin ta zakayi ba bare ma taji kana sanbado mata kalamai tuni zata mace maka yaqarasa maganar yana kunshe dariyar da take son kwace masa dan yasan baqaramin abu suka daukowa kansu da wuya sam ya amince shida bama ya magana da wata macen amma shine yau za ace yayi magana da wata kuma harda kalamai tirqashi abun da kamar wuya,
wata uwar harara ya watsa musu gaba dayan su tare da nuna kansa da yatsan hannun sa cikin hade rai da bata fuska alamar ba wasa din nan yace"ni ni zanje wajen mace mai kuka daukeni ta ba inda zani ni sa'ankune danma kunga ina kulaku shine zaku wani ce inje wai harda cewa inyimata kalamai saidai uwar kalamai zanmata nibanda mace taimin laifi indauki mataki akanta me na iya kai ai kasan halina ba wani abu zan iyace mata ba dan haka kawai ku ajiye wannan maganar saboda ba abune me yiyuwa ba bazan taba zuwa ince inason maceba harkuma inyi mata kalamai kai nifa kama rainamin hankali yafada yana kaiwa shettima bugu akafada kalmar kalaman nan da yafada ba qaramin tsaya masa tayi araiba,
Wallahi ka kiyayeni kana mun abubuwa da yawa ina rabuwa dakai ko to bazanje ba shidinma yafasa zuwa kai zakaje,
gaba dayansu dariya suka saka mishi sanna shettima yace kasan Allah ba maganar wasa ba kai yakamata kaje indai bawai kanason ka bata mana shiri ba kagade layin nasu da mutane bare ace za ayi mata taqarfi tana fitowa mu dannata amota dole sai dai mushigo da ita tacikin sauqi inbahaka ba kuwa tofa aikin mu bazai tafi yanda muke so ba zamu iya samun matsala dan haka malam kawai kafita kaje,
still de kin amince musu yayi saida suka sake wani cecekucen kafin daga baya da kyar da kyar suka shawo kansa tare da yimasa dabara sannan ya amin ce da yaga ba yanda zaiyi,
murna sukayi sosai tare da yi masa godiya sannan suka fita daga motar gabadayan su key din motar bossay yabashi sannan sukace to yafara tafiya sugani sannan ya su sutafi tare da yimasa fatan samun nasara,
ko kulasu baiyi ba saboda haushin su yaje ji yayi gaba abun sa taku baifi biyu yayi ba,
shettima yakira sunan sa dan dakatawa yayi batare da ya juyo ba,
shettima tace fatan nasara fa mukayi maka bazakace Ameen ba ko duk zumudi ne yau za afara zuwa zance wajen budurwa to adai yimata ahankali kar akasheta da kalamai sanna kuma kar ashanyamu muyi tajiranku,
dannasan za ayi wucewa da soyayyar gaske amanta damu dan Allah muna roqode kar ayimana haka romio tuzuru dan nasan ba asaba ba kuma wall.........
beqarasa ba sam yayo kansa afusace,
kafin yaqaraso sukuma sukayi saurin barin wajen suna mishi dariya,
kwafa yayi ya tsaya yana binsu da kallo jiyake kamar ya fasa zuwan ma da haryayi tunanin binsu sai kuma yafasa kawai yayi kwafa tare da juyawa ya nufi qofar gidan,
yana qarasawa sai ya tsaya  abakin gate din,
ya kai wajen 2 minutes agun yakasa kwankwasa gate din wani tunanin ne yaqara fado masa yanzu idan ya buga aka bude wa zaice yana nema sai yanzu ya tuna ashe duk tsare tsaren nasu sun manta basu san sunan taba sosai ya shiga tunanin abun da zaice,
wata dabarace ta fado masa da sauri ya zaro wayar sa dake aljihu sai ya bude ta ya shiga WhatsApp dinsa number ta ya lalubo sannaan yayi mata sallama da niyarsa idan yayi mata magana sai ya goge number ta ta daga kan wayar sa inyaso sai yakoma WhatsApp ya duba sunan da take amfani dashi tanan kawai zai iya gano sunan ta idan tasaka,
bayan yayi mata sai ya fita yake contact din ya goge number ta sannan ya kuma shiga WhatsApp din ga mamakin sa yana shiga dak kawai yaga anbude sallamar da yayi mata alamun tana ma online da sauri ya bude tare da duba sunan da take amfani dashi ba SUMY yaga ansaka ajiki hamdalah yayi tare da sauke ajiyar zuciya,
sannan ya duba yaga har tayi masa reply da hello
" sai kawai yace sumy yakk?
  "ba jimawa ta amsa masa da lfy pls waye?
bangane me magana ba?
"bazaki gane ba daman amma fito waje ina qofar gidan ku sai kiga ko waye...
sticker zaro ido ta turo masa sanna tace aqofar gidan nufa kace anya kuma ni kake nema?
  "of course yabata amsa,
gani awajen amma banga kowa ba ta maido masa da amsa,
duba qofar gidan yafara yi yana laliben ta inda zai ganta amma baiga kowa ba,
  "baki fito ba yamayar mata da amsa,

     "kaga malam nifa bazan fitoba saboda bansan ka ba wai waye ma yabaka number ta?

  shiru yayi ya rasa amsar dazai bata shifa harga Allah yagaji saira kadan takaishi qarshe tun dazu sai wasu tambayoyi take masa,
   daurewa yayi yacije yakai zuciyar sa nesa,
    sannan yayi mata reply da
   " idan kanason abu ai duk wani hanya dazakabi dan ganin ka mallakeshi bazai maka wuya ba dan haka samun number abune me sauki awajena dan haka kima daina mamakin inda nasamu number ki ki ajiye wannan maganar  kitaimaka kifito inga kyakkyawar fuskarki ni masoyin kine na gaskiya( duk wanda  ya tuba dan wuya ba lada ashede ka iya masoyin gaskiya 😂 lol),
Chapter 48 · 0% Book details