← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 139

Sashe 114

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ƙofar ɗakin ya shiga bi da kallo kamar tana gurin kansa ya ƙulle yama rasa amsar da zai bata tunda take da ita hakan bata taɓa faruwa ba ba ƙaramin mamaki yayi ba yau abun da baitaɓa gani ba bai taɓajiba ko amafarki akace Ammah zatayi masa wannan tambayar dan yazo gurin ta bazai taɓa yarda ba, yama rasa me zaice mata dan haka sai kawai yafara ƙoƙarin barin wajen dan baisan me zaice mata ba saidai yana juyawa zai bar wajen aka buɗe ƙofar tsayawa yayi tare sa saurin juyawa yana kallon fuskar ta yaga alamun ba lafiya ba dan baitaɓa ganin hakan daga gare taba to me yake faruwa takawa yafara yi har yaje gaban ta tun kan ya buɗi bakima yayi mata magana ta dakatar dashi tare da cewa kayi haƙuri koma me zakace kabari sai gobe yanzu banda loƙacin yin wata magana duk ka adana tambayoyin ka sai kayi su gobe, gobe da safe zamu haɗu a fada kaji duk abun dake faruwa ina fatan ka gane, kai kawai ya kada mata alamar ya gane,,

tana gama faɗa masa haka daman bata jira cewar saba ta juya ta koma ɗakin tare maida ƙofar ta rufe,

ƙofar yaƙara kalla yadaɗai agurin tsaye mamaki yagama cikasa saida ga baya sannan jiki babu ƙwari ya juya ya fita daga part ɗin ransa duk babu ɗaɗi kansa neman yi masa bunduga yake yau me yake faruwa dashine daga wannan sai wancan abubuwan da suke faruwa dashi suna neman sufi ƙarfin tunanin sa suna neman tarwatsa masa tunani tafita kawai yake shi kansa baisan inda yake ɗora ƙafarsa tafiya kawai yake ahaka har ya ƙarasa part ɗin fulani ya wuce ɗakin sa yana shiga ya faɗa kan gado tare da kifa kansa yayi ruf da ciki shikaɗai hasan halin da yake ciki yarasa wane irin tunani zaiyi yaji daɗi abubuwa sunyi masa yawa yakasa samun mafitar tunanin sa daga yafafa wannan tunanin sai wani ya faɗo masa haka yayi tayi yana faman juyi akan gadon kansa sai sara masa yake kamar zai tsage gida biyu da ƙyar ga iya tashi ya ɗauko maganin ciwon kai da na bacci ya ɓalla ya sha sannan ya koma kan gadon ya kwanta bai jima da kwanciya ba sosai ba bacci ya ɗauke sa......

***********************

______*Rasheeda & Meer*

tana ƙarasawa gabansa tasamu kujera kusa dashi tare da zama tana wani karkaɗa ƙafafu tana jiran ya ɗago, amma baiɗago ba ko gefen tama bai kalla ba,

aɓangaren sa kam tunda ta taho yake kule da ita har ta ƙaraso yasan da da ƙarasowar ta har zamanta duk yana sane da ita saidai baiɗago ya kalli taba dan ko kalar kayan jikin ta baisan waɗanda tasaka ba yadai san dole macece tazo wajen ba namiji ba yadai tsaya kawai yaga iya gudun ruwan ta koma wacece,

cikin kasalalliyar murya me kashe jikin duk wani namiji me rai da lafiya tayi ƙasa da ita cike da kisisina da iya barikan ci da kuma ƙwaraiwa ta ɗaga hannun ta tare da ɗora sa akan gefen fuskarsa ta shafo gefe tana cewa Hyyy the beautiful of the world and nice to meet you baby tayi maganar tana wani kashe ido tare da ƙanƙantar dasu suka koma sexy tana kallon fuskar sa tana so ya ɗago ya kalle ta, yaci gaba da danna wayar sa da yakeyi gama cin abincin sa kenan yana shirin barin wajen sai kuma ya ɗauko wayar sa yana dannawa dalilin da yahana sa fita tun ɗazu kenan har tazo ta tarar dashi agun, amma da tuni ya tafi,

ganin yaƙi ɗagowa ya kalle fa yasa tasaka ɗayan hannuta ta ɗora ta ɗayan ɓarin tana shirin juyo da fuskar sa gareta yanda zata samu damar kallon sa da kyau,

saidai da juyo da fuskar tasa da ɗaga hannun sa duk atare tana juyo da fuskar shikuma ya wanke ta da wani ƙyaƙƙyawan mari saboda tsabar jin zafi da tsorata saida ta faɗi daga kan kujerar da take kai azaune,

baijira wata wata ba daman zuciyar sa akusa take a zafafe yayi kanta kamar mayunwacin zaki haka yayo kanta gadan gadan hannu ɗaya yasa ya ɗagota tare da kaiwa fuskar ta naushi take adaidai kan hancin ta bata gama tantancewa ba ya ƙara kaimata wani awajen bakin ta take bakin yafashe yafara fidda jini ihun da tasaki ne yafara jawo hankalin wasu mutanen dake gurin suka fara kallon su ƙawayen ta da duk abun da yafaru akan idon su suka fara ƴar kallon kallo a tsakanin su kowa yakasa magana sai su kalli juna sai suci gaba da kallon yanda ake jibgar ƙawarsu sun kasa zuwa su taimake ta,

saida suka ga yazaro belt yafara zuba mata ita ajiki tana ihu sannan suka tafi zasu taimaka mata daman gurin ba wasu mutane da yawa agun kuma daman gurin na ƴanji da kansune kowa yana ganin yafi ƙarfin zuwa wajen su yatambayi ba'asi dan haka kawai sai kowa yabasar dasu yaci gaba da abun da yakawo sa wasuma jin ƙarar ta ishesu yasa suka tashi daga gurin suka fitama gaba ɗaya,

ƙawayen ta na ƙarasawa suka fara ƙoƙarin shiga tsakiyar su zee ce tafara shiga rai aɓace tace malam dakata bafa jaka kasamu ba kazo kana dukan ta sai kace an aiko ka, uban me tayi maka,

baibata amsar baki ba sai ta duka kanta yakoma itama yafara zuba mata ai sauran basu jira sunce wani abun ba suka kwashi ƙafafunsu suka kwasa da gudu zasu bar wajen gurin dan sunga alamar mutumin baida hankali wataƙil, dan sunma manta da batun da momy tayi musu kashedi suka ƙi ji,

ai basukai ga bakin ƙofar ba ya jefo musu belt ɗin tashiga gaban su suka harɗe duk sansu dake karsu faɗi amma saida suka faɗi ƙasa suna ƙoƙarin miƙewa kenan yariga su zuwa wajen da hannu yafara dukan su kafin daga baya ya ɗauki belt ɗin suma ya zane su da hannu ya jawo su ya haɗe su guri ɗaya kamar wanda ya sha maganin ƙarfi haka ya ringa dukan su sai yayi tunanin ya rabu dasu sai kuma yaƙarajin wani haushin nasu da kuma ƙarfi sai kawai yaci gaba da dukan su.....

wacce ta taɓasa Rasheeda kenan ita yafi duka da ƙyar ta samu baki tafara basa haƙuri amma yaƙi rabuwa da ita,

yana cikin dukan nata yaji an riƙe masa bulalar ta baya afusace ya juyo dan ganin me gigin da tsautsayi yasa yariƙe masa abun duka,

yana juyowa idon sa yasauka akanta haɗe rai yayi tare da zaro mata idanu zai ƙwace belt ɗin dan itama ya sauke mata nata rabon ƙin saki tayi tasa hannu biyu ta riƙe sosai tana girgiza masa kai mamaki ta bashi sosai cikin kara jin haushi yaja belt ɗin da ƙarfin gaske ya kwace ta daga hannun ta ya ɗaga zai sauke mata abaya tayi saurin haɗawa da bulalar ta faɗa jikin sa ta tariƙe belt ɗin a hannun ta ɗayan hannun kuma tariƙeshi ƙam tare da fashewa da kuka tana cewa dan Allah kayi haƙuri kayi haƙuri.......!!!!!✍️✍️

_plss kuyi haƙuri da jina kwana biyu shiru wayata ce ta samu matsala ta lalace saida nakai aka gyara duk da ƴan group ɗin WhatsApp sun riga da sun sani nasa ansanar daku tun loƙacin da ta samu matsalar amma nasan ƴan Facebook basu sani ba todai da wanda yasani da wanda baisani ba duk ina ƙara bada haƙuri,_🙏🏻

*sannan kuma naji daɗin kulawar wasu ina godiya da ƙoƙarin taimakon da kukayi nacewa ahaɗa kuɗi aturo min duk da ba aturo ba ina godiya da hakan Allah yasaka muku da Alkhairi nasamu kuɗi na gyara yanzu zamu cigaba daga inda muka tsaya*

_ina ƙara baku haƙuri dai nima bada son raina hakan ta faruba har nakai tsawon wannan loƙacin bangyara ta ba sai yanzu ina fatan zaku fahimce ni nagodai.......🙏🏻,_

                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 92

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

  "Sosai ta riƙesa ƙam yakasa motsawa saida sukai wajen minti biyu ahaka jin bai motsaba yasa ta ɗago da jikin ta daga nasa batare da ta kalle saba ta ƙara cewa dan Allah kayi hakuri ka rabu dasu kazo mu tafi Ummy na kiranka tayi maganar tare da ƙara sunkuyar da kai dan tana ɗan tsoron kar taji saukar duka yanda kasan tayi magana da gini haka yayi ko motsawa baiyi ba kuma baida na kallon taba,

ɗan ɗagowa tayi takalle sa aikwa caraf suka haɗa ido dashi da sauri ta sunkuyar da kai gaban ta na dukan uku uku ganin yanda idon sa yayi ja kamar gwarashin wuta,

Su Rasheeda ta shiga kalla yanda suke malelekuwa aƙasa da ɗaya bayan ɗaya tashiga kallon su har ta saukesu akan Rasheeda kallo ɗaya ta gane ta zaro ido tayi cike da mamakin ganin ta tayi saurin zuwa gurin ta tana cewa aunty aunty ta faɗa tana ƙarasa tsugunnawa agaban ta tana ƙara kiranta duk ganin ta yasa tabi ta rikice sai ƙoƙarin ɗagota takeyi,

duk da halin da Rasheeda take ciki hakan bai hanata gane Ameesha ba tayi mamakin ganin ta amma ba halin yin magana ko ta tambaye ta wani abun azabar jikin tama kaɗai ta isheta so take ta zaro wayar ta ajaka ta kira dadyn ta azo aɗauke ta amma ta kasa ganin Ameesha yasa ta buɗi baki da ƙyar tace ɗauko min wayata ajaka,
Chapter 114 · 0% Book details