← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 139

Sashe 73

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ɗagowa yayi yana niyar barin wajen kawai sai idon sa ya sauka akan wata inuwa da tayi saurin giftawa wani lungu da sauri ya juya gurin amma sai yaga ba kowa da har ya basar amma sai wata zuciyar take ingizashi akan yaje yaga komenen ya wuce yana gama ayyana hakan ya nufi wajen saidai yana zuwa yaga wayam ba kowa ƙarewa ma hanyace miƙaƙƙiya awajen hanyar yaci gaba da bi dake gurin da haske dan haka yana ganin komai kawai yaci gaba da bin wajen saida de yaga kamar ma idan yabi ƙarshen sa dajine ba wani kwana ko kuma ɗaki awajen dan baka kawai sai ya juyo yadawo yana cikin tafiya kamar amce masa ya kalli ƙasan sa idon sa na sauka ya sauka akan wani abun hannu da sauri ya tsugunna yana tunanin a inda yasanshi saurin miƙewa yayi daga gurin tunawa da inda yasanshi a fili ya furta tabbas natane wallahi na gansa a hannunta ji da muna mota loƙacin da ya riƙo hannun ta yaganshi....

damƙe abun hannun yayi yanajin kewarta tabbas wannan abun hannun tane to me ya kawo shi nan to sunzo wajen tayardashi wata zuciyar kuma tace masa to kode nan tashigo ta ɓata agun takasa komawa gida saka abun hannun yayi a aljihu yashiga dudduba gurin har inda yabaro ya koma amma baiganta ba da sauri yabaro wajen ya nufi inda part ɗin da yabaro wajen su sam,

da sauri yake tafiya dan har yana harɗewa wajen tafiya da haka ya ƙarasa part ɗin kamar daga sama suka gansa ya turo ƙufar da ƙarfi dukan su suka zuba masa idanu suna tunanin kuma me yadawo dashi dan atunanin su ya daɗe da tafiya ma,

ƙarasawa yayi inda suke tare da zaro abun hannun ta yana nuna musu batare da yace komai ba da sauri shettima ya miƙe yace a ina kasamoshi ko ka ganta ne naga abun hannun ta agunka, yaƙarasa maganar tare da karɓar abun hannu yana kalla yace ai jiya jiyanannan nasiya mata loƙacin da muka fito tanuna tanaso nasiya mata a ina ka ganshi?

"awani guri na tsince shi acikin nan basu labarin abun da yafaru har yaje gurin daga nan kuma yagansa ya kawo musu,

da sauri Sameer ya miƙe tsaye shima ya karɓi abun hannun yana mamakin jin inda aka gansa to me yakai abun hannun ta gurin gurin da ba kowa bane yake zuwa dan yana da tabbacin babu abun da zaisa su Hamra zuwa gurin barai ace garin zuwa ta jefar dashi bata sani ba....
to yake shirin faruwa abun hannun ta acikin masarauta bayan kuma ba anan aka sace taba,....

                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[6/26, 9:53 PM] #momyn twins#: ,  ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️69&70

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

   to me yake shirin faruwa abun  hannun ta acikin masarauta bayan kuma ba anan aka sace taba,....

 shettima ne ya karɓi abun hannun daga hannun sameer yana ƙara nazarin abun acikin ransa shima abun da sam yayi tunani shima ai yayi tunani maida duban sa yayi ga sam sannan yace sameer ina twins suke yakamata muji ta bakin su ko iya zuwan ta sunje wajen idan kwa bataje wajen ba tofa akwai matsala yakamata musan wani abun game da ganin wannan abun hannun ace inda aka ɗauketa daban kuma a tsinci abun hannun ta acikin nan to taya hakan tafaru anya ka tabbatar ma kuwa acan waje aka ɗauke ta kode Sundawo tare ne daga nan kuma tayi wani wajen,

"ba anan ta ɓata ba momma ta tabbatar min da hakan tace sukaɗai suka shigo suna kuka tundaga can suka rasata amma fa abun ya ɗaure min kai to me yakawo abun hannun ta shi tsoran sama kar ayi zargin familyn ɗinsa daman ɗazu bossay yagama faɗar abun da yaga dama yanuna shi baiyarda ba gashi kuma yaje ya nemo abun hannun ta hakan kuwa zaisa yaƙara zargin wani abu yaƙi yarda da cewa ba anan gidan aka ɗauke ta ba,

"bossay ne yace wai kuna nufin ba acikin gidan nan ta ɓatan ba a ina ta ɓata ko ince a ina aka sace ta??

   shettima ne ya kalle sa da sannan yayi masa bayanin yanda ɓatan nata yakasan ce kamar yanda sam yabashi

dafe kansa yayi yana ambaton sunan Allah dan shi yanzu bama shi da bakin magana bayaso ya ƙara sakasu cikin damuwa amma bakin sa taf yake da maganganu amma faɗarsu zai iya sawa su samu matsala dan haka kawai yaja bakin sa yayi shiru tare da koma ya zauna yana kallon su yana jiran jin hukuncin da zasu yanke game da wannan lamarin me ɗaure kai,

   "yanzu meye mafita?
sameer yafaɗa yana kallon su gaba ɗaya,

  "shettima yace mafita ai guda ɗayace kamar yanda na faɗa maka ɗazu dole bari zamuyi zuwa gobe sai mu koma inda sukaje ɗin aduba mana ina ganin hakan shikaɗaine best solution amma ku ya kuke ganin taku shawarar,

"sam yace hakan yakamata muyi amma suma mufara tambayar su tunda suka fita ba wanda suka lura da yana binsu abaya ko kuma sunga wani kusa dasu da yanuna alamun rashin gaskiya danni fa tunanina yafi bani tun fitar su ake bibiyar bayan su har suka cika ƙudirin su akanta,

"shettima yace nima nayi wannan tunani wannan abun dole yana buƙatar mu gaggauta bincike akai yaƙarasa maganar yana mayar da sunansa kan bossay sannan yace "Aliyu baka ce komai ba kasamu waje ka zauna"'

   "to mezan ce ai kune manya sai abun da kukace duk shawarar dakuka yanke daidai ne,

  kawai kallon sa shettima yake batare da ya yarda da maganar da yayi masa ba yasan dole akwai magana abokin sa saidai kawai bazai faɗaba,

  "Shima guri yasamu ya zauna tare da cewa sameer shima yazauna gaba ɗayan su azaune suke sam da shettima suka cigaba da tattaunawa akan lamarin amma banda bossay tunda suka fara bai tanka musu ba,

  daga ƙarshe de suka yanke shawarar sukwana atare inyaso gobe asubar fari su nufi gurin da mall ɗin,

suna zaune suna ƙara tattaunawa sukaji sallamar Ammar ya shigo ciki amsawa sukayi ciki yaƙaro so kusa dasu ya zauna tare sa lanƙwashe ƙafafun sa ya durƙusa agaban sameer zuciyar sa na dukan uku uku tunda momma tace yaje yana neman sa hankalin sa yaƙara tashi dan ba laifi yana tsoron sa har cikin ransa koda ba abun da yayi masa bare kuma ace gashi yau ya aikata babban laifi yasan da ƙyar in jikin sa bazaiyi tsami ba.....

  "yaya gani yafaɗa cikin sanyin murya da fargaba,

sameer dake kishin hiɗe ajikin kujerar duniya tayi masa zafi ya ɗago ya kalle sa kallo ɗaya ya fahimci halin da yake ciki dan haka kawai sai yace masa daman ba wani abu bane kaje kawai amma gobe da safe kashirya zamuje inda kukaje ɗin kade tabbatar agun aka sace ta kuma kana da tabbacin kun fito tare da ita daga gurin?

   Ammar baisan loƙacin da ya sauke wata sanyayyiyar ajiyar zuciya da har saida sam yajishi sannan ya gyara zama yace" eh wallahi tare muka fito da ita,

  Sameer zaiyi magana kenan bossay yarigashi da cewa zaka iya tunawa tunda kuka tafi baku lura da kowa na binku ba abaya ko kuma loƙacin da kukaje wani wajen babu wanda ka lura dashi da yanuna rashin gaskiya akusa daku ko kuma a shopping mall ɗin da kukaje kayi tunani da kyau babu,

  "shiru Ammar yayi alamar yana tunani duk zuba masa ido sukayi sunajiran suji me zaice,

   can de yace gaskiya babu amma bari inkira twins ko su sun lura da wani abun amma nidai gaskiya ba luraba saboda hankalina yana kanta itakadai nake kallo (inji nifa ba inji shiba)

   No rabu dasu kawai nasan yanzu sun kwanta,

   yaya bamu kwanta ba tsulum sukaji muryar Amra tafaɗa tana danno kai ciki gaba ɗayan su suka juya suna kallon ta ƙarasowa ciki tayi Hamra abayan nabinta ashe tare suka taho da Ammar ɗin sai yace su jirasa awaje,

akusa da Ammar suka zauna suma suna fuskantar yayan nasu,

  Bossay ne ya tashi daga inda yake yadawo kusa da su shima a ƙasa ya zauna inda suke sannan ya kalli ɗaya daga cikin su yaƙara maimaita musu tambayar da yayiwa Ammar,
Suma tunanin sukashigayi da sauri Amra tace wallahi loƙacin da muka zazu restaurant naga wata mota ta tsaya abayan mu amma de banga wanda ya fito daga ciki ba muka shiga da muka fito ma kuma muna tafiya a hanya wallahi naga motar abayan mu amma daga nan ban ƙara bi takan taba bansan de ina tayi ba ko taci gaba da binmu ko wani gurin tayi wallahi bansani ba,

mtsww sam yaja tsaki yace ke matsalata dake kinfiya shirir ta to meye nagaya mana wannan abun baki tantance ba,

bossay yace a'a ba wani shiririta tunda har taga motar itama alamar tambaya ce bai kamata ace tayi shirya ba tunda tace loƙacin da suka tsaya sannan kuma me motar baibar gurin ba har saida suka fito kaga kwa shima dole da alamar tambaya akan sa zai iya yiyuwa yaci gaba da bin nasu ita kuma hankalin ta ba abun yake ba ba yanda bazai iya kasan cewa ba,
ke yanzu idan kika ga motar zaki iya gane ta da sauri tace baƙa ce amma idan naganta zan ganeta saboda tana da ɗan tudu,

  good bossay yace sannan ya kuma cewa gobe kema zamu tafi dake saboda idan anduba CCTV camera za agani indai har ya biyo ku za aga motar sa inma aƙafa ne za agani nasan bazamuyi wahalar ganowa ba,
Chapter 73 · 0% Book details