Sashe 113
Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Azeema dake gefen ta ta kalla da har zatace a'a sai kuma kawai tace ba damuwa tana fadar haka kuma ta fice daga falon,
Azeema tsaye tayi agurin takasa gaba ta kasa baya daya daga cikin matasane tayi mata magana da ta dawo kan kujera ta zauna jiki babu dadi duk atakure take jinta haka ta dawo zata zauna akan wata kujera sarki yace mata " dawo nan yafada yana nuna mata gefen sa da hannun duk kallon sa suka shigayi saboda su basu san me yake faruwa ba kuma sunga yana cewa wai tazo ta zauna kusa dashi shi da ko su da suke amatsayin matansa ba kasafai yake sakar musu fuska ba bare har yace suzo su zauna akusa dashi haka yaransa ma baifiya jansu ajiki ba, sai yaga dama ko kuma idan yan mulkin basa kusa shine zakaga wataran yadan yi musu wasa,
kamar yanda yace haka taje ta zauna kusa dashi kallon yake sosai yakai wajen minti biyar yana kallon yakasa magana saidaga bisani sannan yace "tashi ki kunce min wannan abun kannawa ba musu kam ta tashi tashiga ware masa rawanin kansa saida ta kunce masa gaba daya sannan ta nannadai abun ta ajiye gefe sudai matan sa suna zaune suna kallon ikon Allah da abun mamaki,
saida ta kunce masa ta kara ganin kamannin sa da saleem sosai suke kama kamar yan biyu saidai kawai bambancin su manyan ta kuma wannan yama fi kama da mama akan saleem bayan kamar da yake da saleem kana ganin sa zakaga kamannin mama afuskar sa,
kura masa ido tayi shima ita yake kallo yana so yayi mata magana amma yakasa sai kallo kawai ji yayi son yarinyar na shigar sa dukan sa akayi mata dazu yafara tunawa da sauri ya rufe idon sa ji yayi bama yason tunawa gaba daya yanzu idan hakan ta kasance da wane ido zai ringa kallon su dan ya cuci mahaifinsa duk da ba asanin sa yayi hakan ba kuma ba laifin sa bane dorashi akayi akai dan idan yayi tunanin abubuwan da yayi sai yaji ya tsani kansa, duk son yayi mata magana amma yakasa sai kawai ya mike tsaye ya nuna dayar matar sa yace akaita ta kwanta sannan shima ya nufi dakin da zai kwanta yana shiga ya cire duka kayan jikin sa da niyar ban kwana da su dan bazai kara sakawa ba yasan da hakan kuma idan magana zama gaskiya daga gobe bazai kara zaman gidan ba dan jin sa yake gaba daya kamar akan kaya yake duk zaman gidan ya isheshi kuma ya tsani kowa dake gidan so yake gobe tayi kawai yabar gidan matar sace ta shigo dakin cikin lallami da kulawa take tambayar sa abun dake faruwa amma sai yace mata ba komai duk yanda taso ta shawo kansa abun ya gagara haka taita fama da shi daga karshe dai da ta gaji ta rabu dashi ko abinci ma kin ci yayi aranar, rana daya duk yabi ya canza yana abu kamar ba shi ba,
Azeema tunda aka kaita wani daki takasa sakin jikinta haka tayi kwance agadon da aka nuna mata ta hau tayi shiru tana tunane tunane,
aɓangaren fulani kam suna shiga falon ta kaiwa hajiya sarah shaƙa ta haɗa ta da bango tana zazzare ido tare da cewa ni zaki cuta ni zaki ciwa amana duk irin yarjejeniyar da mukayi dake akan sirrin nan shine yau zaki tona min asiri me yasa zaki min haka haka mukayi da ke to kafin kowa yagama sani bari in kasheki kowa ya huta sai inga ta yanda zaki bada sheda gobe wallahi da nasan haka zaki min da tuni na san yanda zanyi dake tun wuri ban taɓa tunanin haka daga gare kiba kin cucune wallahi nima bazan barki ba sai kin ɗanɗani kuɗar ki tana maganar taba zazzaro mata idanuwa,
idanun hajiya sarah sunyi ja sun kaɗa gashi sun firfito waje saboda tsabar zafin shaƙar da take ji saida tabari ta gama tata maganar sannan ta buɗi baki da ƙyar tace to kikashe ni mana sai mai nace kikashe ni mana idan kin cika ƴar halak angaya miki idan kika kashe ni kin tsira kisani idan kika kasheni ne ma zaki jefa kanki cikin babban hatsari domin asirin ki yariga da yagama tonuwa kuma kin manta da shadar da na basa ko bana raye zai gani bare ma kuma daman kinsan boka yace daga ranar da akafaɗi maganar kowa yaji shine makarin asirin ki babu wanda zai ƙara yarda dake dan haka kikashe ni kiƙara jawowa kanki babbar masifa ni kin hutar dani ma bala'in da zan shiga kinga saiki haɗa da nawa laifin a hukun taki tun anan duniya kuma a hukuntaki alahira ki kwashe min duka zunu baina kinga naci riba biyu ke kuma kin tashi da tutar babu dan haka sai kiyi abun da kikayi niya kar ki fasa kiyi kishiga wutar jahannama,
da ƙarfi fulani ta sake ta tare da turata gefe saida ta bugu da bango aikwa tana jin zafi tayo kanta itama cike da masifa da kuma jin zafin abun da tayi mata ta fara zazzagin ta ta uwa ta uba harda su gorin haihuwar da bata taɓa yiba tun abaya yanzu saida ta tuna mata tayi mata tass itama bata barta ta fara mayar mata da ai gwanda ita tayi auren ma ita da take yawon ta zubar fa tana zaman karuwan ci ba uwa ba uba ba dangi sai yawon bari kanci daga nan sai can tazo duniya abanza zata koma abanza jin hakan da hajiya sarah tayi bata san loƙacin da ta daddage ba ta kwashe fulani da maruka har guda uku sannan ta nunata da yatsa tace wallahi ki iya bakin ki san maganar da zaki ringa ni kike cewa karuwa kin taɓa ganina kwance gado ɗaya da ubanki idan ma karuwancinne to da ubanki nayi ubanki nake ɗaga ƙafa ya shiga ai bari in baki labari idan baki saniba agadon uwarki muke aikata zina da ubanki tunda uwarki tayi masa kaɗan ai dole ya haɗa da mai maiƙo irin mu kinga kwa karuwar ma tana da rana tunda ta taimakawa ubanki abun da uwarki takasa basa, ke idan karuwancinne ma har kyayi magana bayan ga babban kwartooo ubanki ubanki ai shine ɗan iskan me yawon ta zuba ba wani ba tunda dashi nake yawon ta zubar ɗin shi kuma ya kwasa da.......
bata ƙarasa maganar da take son yiba fulani tayi wani kukan kura tayi kanta zata shaƙo ta taji anyi saurin riƙeta gaba ɗayan ta anyi baya da ita,
hajiya sarah tace rabu da ita idan ita ta isa ƴar halak tazo ta taɓa ni wallahi sai na koya mata hankali,
itama fulani murya cikin kuka tace kasake ni kasake ni nace wallahi yau sai tagaya min uban da yake karuwaci da ita kirasa wanda zaki gar min sai ubana da yake ƙarƙashin ƙasa duk abun da zakiyi meyasa bazakiyi shi tsakanin dake ba meyasa zaki saka mahaifina aciki da yariga da yabar duniya me yayi miki laifi bani nayi miki meyasa zaki huce akan sa ME YASA...!!! ta ƙarasa maganar da ƙarfi tare da fashewa da wani irin matsanan cin kuka wanda kana jinsa kasan daga ƙasan zuciyar ra yake fitowa dan maganar hajiya sarah ba ƙaramin ƙona mata rai tayi ba ta sosa mata rai matuƙa duk acikin abubuwan da suka faru babu wanda yafi ƙona mata rai irin maganganun ta na yanzu,
kuka take sosai duk wanda yaganta awannan loƙacin sai ya tausaya mata dan kuka ne dake fitowa daga can ƙasan zuciya kana jin kasan ba ƙaramin abune zai saka mutum irin wannan kukan ba,
Sam dake riƙe da ita shi kansa baiji daɗin zagin da hajiya sarah tayi mata ba duk da yaji wasu maganganun da tayi mata itama amma bai kamata ta rama ta wannan hanyar ba tun shigowar su ciki yake tsaye yana kallon su sai yanzu da yaji suna neman wuce gona da iri shiyasa ya ƙaraso wajen dan dakatar da su daga abun dasukeyi kar suje suyiwa kansu illa,
janta yafara yi zuwa ɗaki zai kai ta ɗakin ita kuma tana fusfusgewa tana cewa yasaketa amma yaƙi sakin ta gashi kuma ya riƙeta ƙam ba yanda za ayi ta iya ƙwacewa daga hannun sa haka yajata saida yakaita har kan gadon ta ya ajiye ta sannan yafuto tare da ƙulleta aɗakin ta waje sannan yadawo falon itama hajiya sarah ya nuna mata wani ɗaki kuma ya gargaɗeta kar tasake ta fito komai zataji daga har safiya kar ta fito sannan itam saboda gudun matsala ya ƙulleta aɗakin sannan yafita daga part ɗin gaba ɗaya ma part ɗin Ammah ya nufa yana shiga yaga bata falo dan haka ɗaki ya nufa direct yana zuwa yayi nocking Ammah "tace waye?
yace "nine
jin muryar sace amma sai kawai tace "kai wa?
ba ƙaramin mamaki yayi ba jin tambayar da tayi masa bai taɓa jin haka daga gare ta ba yasan dai tasan muryar sa kuma ya tabbatar ba bacci take ba bare tace bata gane muryar saba saboda da baccin da takeyi, da kamar bazai bata amsaba amma sai kawai ta daure yace "sameer Abdallah sameer,
yana faɗar haka ga mamakin sai ji yayi tace "ya akai mai kake nema me za abaka?