← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 139

Sashe 4

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read

kuka nafashe dashi ina roqon sa yanzu ba wani taimakon dazai iyayi min insamu ganinsa koda sau dayane yataimaka min sai yace wallahi bazai iyayin komai akai ba saboda ko bagaren da aka qullesa ma baza abarshi yaje ba saidai kawai inyi hakuri in koma gida inci gaba da addu'a Allah yakawo sauyi har zai tafi nayi saurin daka tar dashi sai nace ya suffan tamin kamannin mutumin kuma da mota yake zuwa ko aqafa yace wlh besani ba bema taba ganin saba sai nace dan Allah to kayi min wannan taimakon kasaka min ido akan mutumin duk ranar da yazo yatambayeni ko ina zargin wanine wanda nasani nace masa a'a da banyi niyar gaya masa ba amma sai kawai nagaya masa tunanin da nayi nace masa inaso inde be fini jikiba ko kuma banfishi ba inaso inyi shiga irin tashi inje inganda zaro ido yayi jin abun da nace sannan yace baiwar Allah wannan wane irin ganganci kikeso kiyi kinsan halin da zaki jefa kanki kuwa idan aka kamaki nace masa nide zan iya in sha Allah ba abun da zai faru dani yace gaskiya to shi bazai iyaba badashi bazan jefasa a wata masifar ba sosai nakama yimasa kuka ina roqonsa yataimaka min da yagade da gaske nake sai yace to inyi shiru zai taimake ni amma bata wannan hanyar ba injira duk yanda zaiyi yagano inda yake zaiyi inyaso sai ya samomin kayan ma aikatan gidan insaka hakan sai yafi akan inyishigar wancan mutumin da dole ma akamani tunda ba kamannin mu daya ba amma idan nai shigar ma aikata  ba lalle akamani ba saboda akwai ma aikata da yawa bakowa yasan kowa ba nace masa hakan ma yayi sai yace yanzu inbashi number wayata inyaso idan yagama shirya komai sai yakirani duk yanda ake ciki zai sanar dani da sauri na zaro salulata nabashi number sannan nayi masa godiya mukayi sallama,
shiru shiru be kiraba harna cire rai da zai kirani sai ga kiransa amma sai yace in qara hakuri haryanzu besamu damar ganowa ba amma yana nan yana kokartawa nace masa ba damuwa Allah yabashi daman ganowa mukayi sallama atakaicede mufu tsawon wata shida be samu damaba saida kyar yagano yasanar dani aranar da yasanar dani naje da yamma nasame shi yabani kayan maza nashiga wani daki nasaka tare da rufe fuskata da face mask nasaka hula na dora wata qatuwar rigar sanyi akai nasaka takalmin maza wadan da duk shi yahada min su sai kwanon abincin da zan kai masa saboda damai kai abinci suka hada baji shima yataimaka min yabashi kayan sa yakawo min nasaka saida aka idar da sallar magrib sannan muka fito daga inda muka shiga haka na fito kamar namiji ba wanda zai ce macace addu'a nayi sosai gaba na na dukan uku uku haka nuka shiga ciki nida shi daman ya kwantan tamin inda zanbi dan haka muna zuwa shi sai ya tsaya daga baya yanda idan wani ya taho zaiyi sauri ya kirani awaya,
a haka na doshi wajen nikadai ina ta jero addu'o'i ina tafiya  duk addu'ar da tazo bakina yi nake  har naje bakin wajen kuma Allah cikin ikon sa ba wanda na hadu dashi a hanya saboda wasuma basu dawo daga masallaci ba har naqarasa bakin gurin da yake ina tafiya naji hawaye na tahomin da narasa na meye na farin cikin zan ganshine ko na bakinciki kuka ne yaci karfina wanda nama kasa magana saida na tsaya agefe nayi me isata sannan na qarasa bakin dakunan dasuke ajere naje daidai kan inda yace zanga ansaka number 43 nanne dakin da yake ciki qaraswa nayi ina leqawa nagano sa a tsugunne ya kifa kansa akan cinyoyin sa naji dadin ganin sa ashede zan qara sakashi acikin idona kafin inbar duniya saida nagama qare masa kallo naga ya rame ya canza sosai shagala nayi da kallon sa dan harma na manta a  inda nake saida naja lokaci kafin indawo hayyacina dan bubbuga qofar nayi amma shiru be dago ba cigaba nayi da bubbugawar amma yaqi motsawa saida yajide baza adena ba sanna yace bazan ciba ka koma da abincinka saboda atunanin sa me kawo masa abincine banyi magana ba na qara buga qofar sai lokacin yadago lokaci guda muka hada ido dashi sai ya kawar da nasa gefe ahankali nace dan albarka juyowa yayi da mamaki qarara a fuskar sa sai kuma yamayar dan atunanin sa ko kunnuwan sane suka jiyo masa muryar wadda baya tunani zatazo qara kiran sa nayi nace dan albarka ko in komane baka son ganina yanzu kam saida yayi wata iriyar zabura da har saida yakusan bani dariya da gudu yazo wajen sai kuma ya tsaya yace bawan Allah kamar muryar mace naji anan ko ninake jin haka dan Allah bude idon nayi na kalle sa da kyau yacanza gaba daya ga gashi da ba gyarashi yake ba duk ya cika masa fuska inbaka sanshi bama sosai baza ka taba ganesaba gashi yayi duhu sosai ga wata uawar rama da yayi kana ganin sa kansan yana cikin mawuyacin hali,
saida nagama qare masa kallo shima kuma ni yake kallo kana  nace masa  wai kana nufin baka gane niba nice ba nafada tare da dan bude fusakata kadan yanda zai ganni aikwa yana gani yayi suman tsaye yayi da qyar ya iya bude bakinsa yana in ina yace umm..um..ummin mu kice da gaske ko gizau din da nasaba yine kice min ba mafarki nake ba ummi ummin kece agabana ya akayi ki ka shigo daman kuna raye ina baba ina Ameesha duk suma suna raye basu cutar dakuba ummi taya akayi kika gano inda nake ina ne nan wane garin suka kawoni duk yabi ya kidime sai faman tambayoyi da yake jeromin sai da na bari yagama sannan nace dan albarka wacce tambayar zan fara baka yanzude duk ba wannan ba bani da lokaci kasande shigowa nan ba tadadin rai na shigoba kuma nanason azo a riske ni anan atakaicede yarka tana nan lafiyarta qalau malam kuma tun washe garin ranar da muka bar wajen ka nafita unguwa kafin indawo sukazo suka tafi dashi bansani ba ko sun kasheshi ko yana raye Allah masani ammade suna zuwa inda nake sunce kuma inde ban basu abun dasuke nema ba sai sun kasheshi amma basu san Ameesha na raye ba nace musu ta mutu tare da mahaifiyar ta shiyasa ma inajin take araye haryanzu kuma duk sanda zasuzo basa samunta agidan ni kuma bazasu kasheni ba sai nabasu takaddun ka da komai naka ni kuma na hanasu amma yanzu abun dasuka fi damuwa dashi shine su fara sanin inda kake saboda kasaka musu hannu nikuma nace musu suje can garin su nemeka idan 'yan can kuma suma da nasu shirin akanka shiyasa basu fada musuba inda kake saidai ni suke ta bibiya duk inda naje sai sunbini sun gano inda nake shiyasa ma tun ina guduwa har na dena saboda koma ina naje sai sun nemoni shiyasa na rabu dasu tunda na fahimci baza su kasheni ba,
adan takaicede nabashi labarin komai harda kukansa jinyanda naked ta garari nikadai yace alokacin kuma na tambayesa wai ance wani mutum yana zuwa wajen sa shikadai ake bari yagansa waye mutumin shine yace shimade ba alkhairi bane yake kawosa  ba shima duk akan maganar ne aikosa akayi amma be bashi amsar komai ba yace kuma inde banbashi ba bazan taba barin gidan nan ba har abada ni kuma nace yayi duk abun dazaiyi amma bazaiji komai daga gare niba saboda nasan kona basu ba barina zasuyi ba gwara in hanasun ma gabadaya,nace masa yayi tunani awajen aikinsa ba wanda suka taba samun sabani ko yayi masa laifi da zaisa suyi masa wannan sharrin ko akwai wanda yake jin haushin shi yace min shidai bai taba fada da kowa ba inma akwai wanda yakejin haushin sa to besani ba ammade dole akwai hannu mutane da yawa akansa ba iya dauke wayar ne yasa akayi abun da akai ba saida sa hannun masanin bankin sannan kuma wadan can mutanen ma suma daban ba bakinsu dayaba nace masa hakane nande muka dan tattauna game da yanda zamu bullowa lamarin ta yanda zamu gano ko suwaye amma sai mun hada hujjoji sosai sannan zan shigar da qara awata kotun ko Allah zaisa adace mugano meye musababbin bibiyar tashi da akeyi me ya aikata ko me mahaifiyarsa ta aikata amma dole sai munsamu tsayyayen lauya me gaskiya in bahakaba yanda sukayi mana awacen qarar da akayi yanzu ma haka zasuyi zasu siye alakalanne gaba daya yanda baza ataba bamu gaskiya ba daga qarshe ma za a iya hadamu gabadaya a qulle mu saboda ba imanine da suba basu da tausayi akan abun da suke so kodan kar asirin su ya tonu zasu iya yin komai daga qarshe reshe ya juye da mujiya  shiyasa sai munbi komai a hankali  inda so samune na musamu lauya na kusa damu sosai yanda baze iya cutar muba, alokacinne kawai yazo min da wata shawara yace me zai hana insaka Ameesha makarantar privet yanda zata samu karatu me kyau ta shiga jami'a tayi karatu me zurfi inyaso sai ta karanci bangaren law wannan ce kawai hanya mafi sauki yanda zata tsaya musu amma in ba haka ba duniyar nan bata da tabbas mutane ba abun yarda bane yanzu kowa yafi bawa kudi mahimmanci anfidaukar kudi fiye da komai inde za abawa mutum kudi to zai iyayi maka komai zai dannai gaskiya ya dau rashin gaskiya yanzu rayuwar ta zama haka saidai fatan shiriya (Allah yasa mu cika da imani Allah ya kawar da kanmu akan abun duniya ameen)
kiran da yashigo wayatane yasa mu katse hirar da muke ashe har lokaci yaja haka lalle mutumin nan ya taimakamin ina dagawa yace inyi sauri infito ga shinan za azo wajen da sauri mukayi sallama yace ingaishe masa da Ameesha sannan dan Allah kar intaba sanar da ita labarin komai har sai ta mallaki hankalin kanta,
daga nan mukayi sallama badan musoba muka rabu ina daf da fitowa naji ance Rabi'u zo ka kamamin wannan tun dazu nake neman ka ina kashiga ne gabananen yafadi nakasa juyowa ina tunani ta inda zan fara yin magana kawai na qarajin wata murya ance laa ai da kabarshi ma kawo inkaima ka zan iya to to gashi shikenan ma ngd ai bangama jin maganar tasu ba nayi saurin barin wajen,
lokacin da muka fito har anidar da sallar isha mutane sun fara shigowa muna shiga dakin nayi sauri nacire kayan na maida nawa nasaka nayi masa godiya sosai sannan na taho gida,
tundaga wannan lokacin inde ina son ganin sa ina zuwa mutumin nan yana taimaka min kuma inajin dadin hakan dan nadena ma yawan damuwa hankalina kwance naci gaba da rayuwata kuma mutanan ma daga baya sai nadena ganin su kwata kwata suka dena zuwa,
Abun mamaki da nakasa ganewa ranar da naje ina son ganin sa saikawai na nemi mutumin da yake taimaka min na rasa wayarsa ma ta dena shiga da na tambaya sai akace min yadena aiki agun baji dadin labarin ba shikenan  yanzu na dena ganin sa tundaga lokacin inde naje bana samun mafita tun ina zuwa ko zan samu wata hanyar da zanshiga bana samu har na hakura na fawwalawa Allah nadena zuwa,
Chapter 4 · 0% Book details