Sashe 107
Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"zaune suke ita da ƙawayen ta wajen susu biyar ita ta shida ko wacce taci uwar kwalliya sun saka kaya ɗamammu mayafai akafaɗa ga ɗaurin ɗan kwali ko wacce da kalar nata saikace masu zuwa gidan biki saɓanin Rasheeda da take sanye da doguwar riga kawai ta ɗan ɗora mayafin kanta tare da ɗan zamashi kaɗan gashin ta yafito ba laifi itama fa kyakkyawa ce son kowa ƙin wanda ya rasa,suna cikin wani restaurants ko wacce gaban ta cike da abinci me rai da lafiya da sukayi order awajen bakajin bakin kowa saboda cin abincin da sukeyi kowa hankalin sa nakan kwanansa banda Rasheeda da tayi zaune tana kallon su saboda ita bata cin abincin sukaɗai ta siyawa ita banda ita ake ci tanaso sugama su tashi daga gurin dan ji take zaman gurin ya isheta dandai sun takura matane shiyasa suka fito adaren nan suɗin ƙawayen tane da suka fara zuwa tunyanzu ace warsu gwara suzo ayi komai dasu daman kuma ita takirasu suzo afara shirye shiryen biki saboda sai anyi kwana goma cif ana kwasar sabada dan haka dole sai anfara shiri sa wuri, duk yau sukazo daga gida jensu suka sauka agindasu bayan sungama hutawane suka sakata agaba sai takawo restaurant dan anan suke sha'awar suci abinci yau saida tace dasu ma zata saka ayo musu order amma sukace su sunfi so suje da kansu dan haka bayanda ta iya dole ta kwasosu amota suka fito bayan sun fito ɗin ma zata kaisu wani waje ɗaya daga cikin su tagaya mata ai ga gurin da suke son zuwa wajen babban restaurant aduk cikin kano babu restaurant irin sa yafi kowanne tsaruwa da tsada da komai da komai saboda ko baƙi akai daga wasu ƙasashen ko kuma masu kuɗin garin da ƴan ƙarya duk nan suke zuwa gurin yayi fice ako ina da ina kowa yasanshi sunan gurin(XEEMAT RESTAURANT) ga masu son zuwa sai su gaggauta zuwa dan bawa idon su abinci suga tsaruwar gurin😜😜,
ɗaya daga cikin sune tafara gamawa ta ɗau tissue ta goge bakinta sannan tace nagama saura ku wata tace nima na kusa gamawa ai bajimawa mutum biyu suka ƙara gamawa yarage saura mutum biyu su gama suma kuma sun kusa gamawa dan ma yanga suka tsaya da tuni sun gama,
cikin zaro ido ɗaya daga cikin su ta furta "wow!! oh my gosh tafaɗa tana yarfa hannu,
duk ɗagowa sukayi suna kallon ta ɗaya ta taɓota tace zee yadai me kika gano saboda sunjuya inda sukaga tana kalla basuga komai ba shiyasa ɗaya tayi saurin tambayar ta,
saboda tsabar ruɗewar da tayi tama kasa bata amsa sauran saida suka shiga tambayar ta kafin ma ta basu amsa ta ƙara ganin sa gurin ta ƙara kalla tace nashiga uku ku kalla wayyo Allah na gaba ɗayan su suka maida dubansu gun datake kalla ai sai suka nemi su fita haukacewar,
Rasheeda ita harda miƙewa ma wajen kallon sa bakinta yama kasa motsawa haka suka zubawa masa ido har ya fice daga gurin,
sannan wata tace "daman akwai irin waɗannan mazan agaske?
wata ta karɓeta da cewa "nima dai abun da nake tunani kenan kowacce da abun da take faɗa,
buɗar bakin Rasheeda sai cewa tayi 'ina son sa gayen yayi min banason in rasa wannan daman kutashi mubi bayansa dan wallahi bazan bari ya kuɓuce min ba sai nayi masa magana kutashi mutafi ta faɗa tana miƙewa daga gurin,
Wacce tafara ganin sa tayi saurin miƙewa tace haba baby Rash ke da aka kusa bikin ki me zakiyi da wani ai mu yakamata kibari mu yaƙeshi kedai kuyi haƙuri da wanda kika samu ko ya kukace biyu daga cikinsu suka ce zancen ki babu ƙarya aciki baby Rash hakan yakamata ayi,
wata mahaukaciyar harara ta maka musu tace ku kun isa ina ruwana da bikina da aka kusa ai ko ranar ɗaurin aure ne nayi tozali da wannan guy ɗin zance nafasa ne bare kuma bikin ko zuwa baiyi ba ina gayawa dady na nasan zai yarda afasa wannan ba matsala bane, dan haka kada wacce ta sake magana akai inma da wacce take sonsa ta haƙura zan biyaku ko nawa kuke so ku tayani farautar kar wacce kuma ta ƙara yimin maganar wancen kumanta dashi,
ihu sukayi jin zata biyasu daman sunsan tafi ƙarfin su ita zata iya gogawa dashi su daman basu ɗorawa kansu ba dan haka rabuwa dashi abune me sauƙi,
Suna murna suna cewa wallahi munbarmiki indai zaki biyamu bamu da matsala da hakan muje kawai kar ma yayi mana nisa dannaga yanda yake tafiya ba wani sauri yake ba,
zee tace "daman yana kalar madara taya zai iya yin wani sauri gayen fa ta ko ina yayi ba ƙarya daga gani kuma mugun me kuɗi ne wallahi Allah dandai hajiyar mu ta ƙyasane amma da ko ba boka ba malami da kisisi na sai nayi wuff dashi,
Rasheeda ta harare ta tace "basai kiyi mugani ba ni dan Allah ku muje kun tsaya kuna ta surutu har sun juya zasu tafi sai Rasheeda ta tsaya tare da juyowa ta kalli wata daga cikinsu da take zaune agun bata da niyar motsawa kuma tunda suka fara surutun su babu wanda yaji bakin ta batace ko A ba azancen nasu,
kafin ta buɗi baki rayuwa ɗayar magana zee ta ƙara cewa yadawo yadawo kunganshi kunganshi duk rikicewa suka ƙarayi suna sunbatu akansa ta gefen su yazo yaƙara wucewa basudaina kallon saba saida kaga ya shige wani waje sannan suka fara dawowa cikin hayyacinsu,
cigaba sukayi da kuruntashi suna yabon irin zubinshi da halittar su da irin kyaun da Allah yayi masa kamar shi yayi kansa,
Zee tace ƙawata idan kika samu wannan guy wallahi kinyi wa sauran mata fintinkau dan ba wacce zata kai ki ke ko ƙafarkima baza akamokiba har na haskoko wallahi baƙaramin dacewa kukayi ba kingani kuwa,
fari Rasheeda tashiga yi da ido tare da sakin wani kayataccen murmushi tana jin wani farin ciki da sonsa na ratsata jitayi da yazo wucewa kamar take ta rungume shi kallo ɗaya yagama tafiya da imanin ta dan har tanaji aranta idan bata sameshiba zata iya shiga mawuyacin hali daman irin mijin datake mafarki kenan kuma gashi yau Allah ya haɗata dashi dan haka dole tabi hanyar da zata sameshi dan ganin bai kuɓuce mata ba bata son tayi wasa da wannan damar da tasamu yanzu ita kaɗai yasan abubuwan datake ƙissimawa aranta idan suka fara haɗuwa dashi sai ta rikikkishi da nata salon saitasa kallo ɗayan da zai fara yi mata yaMana yagama susucewa kanta loƙaci ɗaya zatasaka masa sonta aransa,
juyawar da zatayi idonta ya sauka akan ɗaya daga cikin ƙawayen nata dake zaune akan tabur ɗin bata tashi ba tun ɗazu yanzu kuma sai suka ga ta kifa kwanta da tabur ɗin ta ɓoye fuskarta,
gabanta Rasheeda ta ƙarasa tare da ɗan buga tabur ɗin, tana ɗagowa suka haɗa ido da ita sai ƙawar tayi saurin janye idonta tana shirin ƙara mayar da kanta ta kwanta,
Rasheeda tayi saurin dakatar da ita tare da cewa "ke kuma baƙin ciki kike munne da kikayi zaune baki da niyar tashi zee tace nifa tun ɗazuma nake lure da ita batayi magana ba kuma dai nasan halin momy da son maza masu kyau da surutun tsiya amma banji tace komai ba anya lafiya kuwa kodai wani abun kike shiryawa daban,
da ƙyar ta tattaro sauran yawun da baigama bushewa ba abakin sannan ta ɗan samu damar miƙewa jikin ta har karkarwa yake ta matso kusa dasu sannan ta kalli Rasheeda tace bana miki biƙin ciki tunanin zakice hakanne ya hanani magana tun wuri amma nidai shawarata agare ki da zan baki shine duk inda tunanin ki yake kiyi gaggawar dawo dashi cikin jikinki kidaina furucin da kike ki koma gurin wanda kike so yake sonki gun da za ariƙe ki da mutunci domin wannan mutumin da kike gani ba alkhairi ne agare kiba karkiyi kuskuren shiga hanyar sa kijawowa kanki bala'in da baki taɓa gani ba, domin wannan da kike kira da gaye ba gayen arziƙi bane yafi ƙarfin ajinki da tunanin ki,
cike da zafin rai da masifa Rasheeda kamar ta rufe ta da duka tace ta daka mata tsawa da cewa momy ya isa haka nace ya isheki haka afaɗin garin nan ke harkina da bakin cewa wani yafi ƙarfin ajina ki kalle ni da kyau meye bani da shi da akesonshi ajikin mace wanda bani dashi idan kuɗi kike magana kekinsan ko ni wacece basai angaya miki ba dan haka wallahi naƙara jin kinfaɗi kalmar da bata dace ba sai nayi ƙasa ƙasa dake agunnan nidaman nasan baƙin ciki ne da hassada ne suka hanaki magana tunɗazu sai yanzu da kika kasa riƙewa hassadar tafi ƙarfinki kinkasa jurewa sai yanzu zaki bayyana ta daman ana gayamin kina min zagon ƙasa bana yarda sai yau da kika nuna min halinki a fili nagane hakan to zansan zaman da zanyi dake daga yau,
murmushin ta ƙaice momy tasaki sannan tace kinsan ai da halina ne hassada da tuni kin sani waɗanda suke zuwa suce miki ina miki zagon ƙasa saidai idan su suke miki amma bani ba ni bana mufurci bana yin zancen wani abayan idon sa kana min ba daidai ba zan gaya maka kayi min ba daidai ba danni banga abunda wani ya isa yamin ba wanda Allah baiyi min ba shiyasa banajin tsoron mutum da zan kasa cewa wani abu gaban sa ba indai kinga nayi zancen wani abayan idon to na tabbatar zan iya yi agaban sa koma na riga nafara gaya masa kafin inje wani wajen inyi dan haka ki adana kalamanki ba akain yakama kiyi suba kije kiyi a inda ake munafurtar taki amma ba waje naba, ɗan dakatawa tayi sannan ta juga ta kalli sauran ƙawayen tace Inma acikin kune wasu suke faɗa mata haka to kuci gaba kunriga da kunsan halina wallahi duk wacce nakama tana min munafurcin abun da banyi ba to ta kuka dakanta dan ba wacce zan ɗagawa ƙafa kunfi kowa sanin halina kunsan kuma ko ni wacece dan haka muzuba mugani wata ta buɗi baki zatai magana Rasheeda tayi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannun,