← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 139

Sashe 54

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   " kamar wadanda ake juyawa atare yanzu ma atare suka juya wajen gate din ahangame suka gansa,
"Bossay ne yace wai tafiya yayi?
  Shettima "yace ga zahiri kana gani kuwa,
  "to ina yatafi?
ni ina zansani bayan munaa tare dakai rashin mutunci ne kawai nufin sa muhau motar haya,
tab gaskiya yagama damu to meyasa zaiyi mana haka "duk borin kunya ne nasan yasa shiyimana haka cewar shettima,
amma bari in kirasa inji wayarsa ya dauko ya kirasa saida baidaga ba wani kiran yaqara yimasa sai da takusan tsinkewa sannan yadaga shina kuma yana dagawa yace musu muhadu agida kawai ya kashe wayar,
wayar suka shiga bi da kallo kamar shi suka gani ajikin wayar,
bayanda suka iya dole suka hakura bayanda zasuyi dashi suka fita daga gidan suka rufe gate din sannan suka nufi titi aqasa shi kansa titin kafin suje aikine saboda nisan sa,
suna tafiya suna jan tsaki da hirar abun da zasuyi masa zsai sun rama abun da yayi musu ko ta hanyar tsokanar sane wallahi idan suka sakashi agaba sai ya tsani kansa dan kowa sai yasani, ahaka suna surutansu har suka ƙaraso bakin titin napepe suka tara direct suka wuce masarautar abakin gate aka ajiye su suka biyashi kuɗin sa suka shiga ciki masallaci suka shige saboda harma antayar da sallar magariba'
bayan sunyi sallar suka suka nufi can cikin masarautar inda part part suke, part din momma suka fara nufa dan sunsan bazai wuce can dinba dole nan zai fara zuwa, amma ga mamakin su suna shigowa suka duba parking space basuga motar da yataho da ita ba alamar de baidawo gida ba part din momma suka shiga,,
basu tarar da kowa ba a falon sai kawai suka zauna akan kujerar suna zama momma ta fito daga kitchen hannun ta dauke da try tana ganin su tasaki murmushi tare da cewa sai yanzu kuka dawo tunɗazu nake zuba ido ganinku, taƙarasa maganar loƙacin da taƙarasa gaban dinning ɗin ta ajiye sannan tadawo wajen su tasamu waje ta zauna tana fuskantar su,"shettima shima yana dan murmushin yace ayya momma wallahi wani aikine ya riƙemu bamusamu damar gamawa ba sai yanzu,
to ai shikenan tundade yanzu kundawo sai kuzo kuyi dinner tunɗazu daman nasa aka haɗa muku ku kadai yake jira ina me sunan baba naga kun shigo kukaɗai ko ya wuce part ɗinsa?
"shiru duk sukayi sun rasa me zasuce mata,
da har shettima zai fadi gaskiya sai kuma yayi saurin bugar bakinsa sannan yace a'a momma yana nan ƙarasowa yadan biya wani wajen ne yace mutaho yanzu zai shigo,
tace to shikenan zaku jirasa ɗin ne ko zakuci?
"a'a zamu jirasa ai yanzu zai shigo,
"tace to bari inje in kungama kwamin magana tafaɗa tana miƙewa daga gurin ta hau upstairs tabar su agun,
"hira sukaitayi abunsu suna jiran shigowar sa amma shiru har wajen ƙarfe tara bai dawo ba...

aɓangaren sam kam tunda yafita da ita tasakar masa wani sabon kukan tana cewa ya sauke, shikuma bai kulata ba, dade yagaji da kukan nata saikawai yasamu bakin titi yayi parking tare da zuba mata idanu yana kallon ta shifa yarasa yanda zaiyi da yarinyar, kai ta kifa akan gwaiwarta tana ta faman raira kuka amma jin ya tsaya yasata ɗagowa titin tashiga bi da kallo ganin ba gida bane yasata tajuyo ta kalle sa haɗa ido sukayi tayi saurin jefa masa harara sannan ta kawar da kanta,
ahankali yace dan Allah badan niba kitaimaka kiyi min shiru wallahi tun da muka hadu kike sakamin ciwon kai naji ban kyauta miki ba amma ai na baki haƙuri yakamata ki fahimceni kitaimaki rayuwata kidena wannan kukan wallahi banason kuka na tsani kuka badan nasan ninayimiki ba daidai ba wallahi da tuni na saitaki amma yanzuma bata ɓaci ba ina roƙonki da Allah da Annabi kiyi shiru wallahi karki kaini ƙarshe dan zan iyayi miki abun da baki tunani kibini ahankali, ɗagowa tayi ta kallesa ganin yanda ya hade fuska tana mamaki ace wai mutum yana magana cikin sanyin murya amma kuma har yakoma faɗa saboda tsabar yasaba da masifa wannan wane irin mutum ne haka da baƙin hali bashida tausayi,
jin tayi shiru yasa yaci gaba da tafiyar sa atunanin sa shikenan ai ya tsoratar da ita bazata ƙara damun saba, kamar kwa yanda yayi tunanin kwa hakance ta kasance bata ƙara kukan ba har suka ƙaraso gidan,
agaban gate din yayi parking tare da cire louck din motar ko kallon barinta baiyi ba yace mata fitar min amota,
yanda kasan yayi magana da dutse haka ta mayar dashi ko motsawa batayi ba jin shirun ta yasa yaƙara cewa kifitar min nace miki ko bajiki ba nan ma shiru bata motsa ba,
"afusace ya juyo zai balbaleta da faɗa sai kawai yaja stop yana binta da kallo hannu yakai saitin fuskarta da take arufe yadan hada hannun sa guri guda yabada ɗas ɗas yayi sau biyu amma bata bude idon taba,
"bacci? yafaɗa a fili rabuwa yayi da ita ya koma ya kwantar da kansa shima yayi ajikin kujera tare da lumshe idanu yana jiran farkawar ta(Tabb😬)
jin abu yayi akafadarsa ahankali yashiga bude idon sa akanta yasauke su datake kwance akan kafaɗar sa,
maimakon ya tasheta sai kawai yadan ƙara gyara zaman sa yanda zatafi jin daɗi kwanciyar ahaka ya yakomar da kansa kan kujera ya ƙara lumshe ido,
bazato ba tsammani shima baishirya ba bacci yayi awon gaba da shi ahaka sukayi bacci gaba dayan su tana kwance akansa...........

💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(mrs bmb)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

[6/8, 6:28 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️51&52

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

___________*Abuja*

     "tunda ta kwanta ta bata farka ba sai bayan sallar la'asr,
    tun suna leƙanta suna jiran farkawar ta da wuri harde suka haƙura suka tashi daga falon amma jim kadan dai wani yazo ya duba ta,
   bayan sun idar da sallar la'asr ne suka ƙara zama awajen ta gaba ɗayan su,
   basu daɗe da zama ba suka ga tafara motsi dukkan su miƙeya sukayi suka koma kusa da kujerar ta suka zuba mata idanuwa,
   ahankali ta shiga buɗe idanun ta tun tana ganin dishi dishi harta ƙarasa bude su tar ta sauke su akan su  ƙara mayar dasu tayi ta rufe sai kuma tasake budesu jitayi jikin ta gaba daya yana yi mata ciwo ahankali ta yunƙura zata miƙe zaune amma taji takasa,
  'da sauri meer yakai hannu sa ya daugota da taimakon sa tasamu ta zauna' " jigina kan kanta tayi da jikin kujera tana dan dafe kanta saboda bata danji dadin sa jitayi yana danyi mata
ciwo amma ba sosai ba,
   Ummy ce tafara cewa sannu sannan Abu ma yayi mata sannun,

       'meer kuma gefen ta yasamu yazauna  sannan yayi mata sannun,
"bata amsa sannun kowa ba saidai duk wanda yayi mata sai ta bishi da kallo batare da amsawa musu ba,

"falon ta shiga bi da kallo tana mamaki aranta inane nan,
  ba inda yake miki ciwo?
   "Abu yakatse mata tunanin ta,
  juyowa tayi tana kallon sa tare da kafesa da ido kamar zata ciro wani abun ajikin sa saida tagama ƙara masa kallo sannan takawar da kanta mayar dashi tayi kan meer shima haka tayi masa,
   "saida ta dauki loƙaci me tsawo batare da ta iya budar baki ba tayi magana,
    duk sun ƙosa da suji tayi magana amma taƙi yi,

  A ina nake nan, nan gidan waye?
  sukaji ta jefo musu tambaya bayan kuma kafin ta kwanta sungama magana da ita amma yanzu taƙara tambayar su ko da yake bai kamata ma suyi wannan tunanin tunda yanzu tadawo hayyacin ta watakil ta manta tattauna warsu,
' Ummu ce ta zauna adayen gefen nata tare da riko hannun bata wani dau lokaci ba kawai tayi mata bayanin yanda komai yafaru bata rage mata komai ba har zuwa yau da akayi mata ruƙeya komai Saida taba ta labari,

"kuka tasakar musu jin yanda rayuwar ta takoma tsawon wasu shekaru sosai take kuka abun ba ƙaramin ciwo yayi mata ba ace tana gidan sarauta da iyayen da daginta da ƴan uwanta da mijin ta ga ɗan ta da tahaifa babude abun da ta rasa amma ace rayuwar ta taso ahaka kuma batare da kowa ya neme ta ba wannan wacce irin ƙaddara ce ta same ta wane irin zunubi ta aikata musu da har zasuyi watsi da ita haka shin wai nema yafito da ita daga cikin gidan tamabayar da tafi tsaya mata arai kenan,

"cikin kukan tayi musu godiya da irin dawainiyar da sukayi da ita har ta samu lafiya,
nan suma suka nuna mata ai bakomai ayi yiwa kaine har suna nunamata rashin jin dadin yawan godiyar datake tayi musu dan su har kunyama suke ji,

' da ƙyar suka samu tayi shiru da kukan da takeyi sannan, Ummy ta gyara zama tare da cewa Abu ka zauna mana, kujera yasamu yazauna sanshi yama manta atsaye saboda gaba ɗaya hankali sa yana kan ta,
shiru falon yadauka na wasu yan daƙiƙu ,kafin daga bisani ummy ta katse shirun nasu, dacewa baiwar Allah inba damuwa ko zamu iya sanin ko ke wacece kuma daga ina kika fito dan inafatan yanzu kin tuna komai, ko ba hakaba ?
Chapter 54 · 0% Book details