← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 139

Sashe 109

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita kuma matar da tashigo da sauri taje wajen baba tana girgiza shi tanacewa kar ka mutu yanzu ba lokacin mutuwar ka bane ina bukatar ka araye kar ka mutu katashi juyowa tayi taba kallon sarki da shi mamaki ma yahanasa magana yabari sauran sugama nasu ya yanke nasa hukuncin me gaba daya dan ya riga ya kistimawa randa babu ma kara kwana da ransa ayau dinnan sai yasa ankashe kowa da su har matar da takawo kanta tunda yake babu wanda yataba yi masa makamanicin abun da sukayi masa jin zuciyar sa yake kamar zata fashe saboda tsabar bacin ran da yakike cinsa,

cike da daga murya ta kalli sarkin tace kaidai ba halinka mugunta ba to daga yau baza ka karayiwa wani ba kuma wannan abun da kayi kayi na farko kayi nakarshe dan sai kayi da nasani arayuwar ka kuma har abada baza kadaina ba wannan abun sai yazamar maka tabo acinki zuciyar ka tabo ma kuma wanda bazai taba gogewa ba har abada sai nasa ka tsani kanka sai kayi da nasanin da baka taba yiba arayuwar ka,

tunda tafara magana sarki yake kallon ta kawai ko kiftawa bayayi ya kafeta da ido har saida ta gama sannan ya dauke idon sa daga kanta ya mayar dashi kan hamza dake rike ds wuyan mutumin nan har yanzu yaki saki ga sauran suna ta kokarin rabasu amma sun kasa nan ma dauke idon sa yayi yamayar kan Azeema dake kwace kamar matacciya amma idon ta abude yake kawai tsabar azabace yasa takasa motsawa duk da hankalin ta yana kana babanta da matar kuma datake masa magana tana cewa kar ya mutu,

cike da kasaita sarki yafafa zagaya su yana kara binsu da kallo daya bayan daya, sannan yakira wani daga cikin su yana zuwa ya rada masa abu akunne da sauri yafita daga cikin fadar,,

da kyar aka iya raba hamza da wanda ya shakesa ana rabasu kuma suka cigaba da dukan hamza basu dade suna dukansaba sarki yadakatar dasu tare da cewa azubawa tsohon cen ruwa atake suka kwarawa baba ruwa me yawa,

da sauri baba yasauke numfashi me karfi cikin mawuyacin hali lokaci guda duk yatuna abun dake faruwa baisan lokacin da yafara zubar da hawaye ba wannan wacce irin masiface ta sameshi tunda yataso daga yaro har kuruciyar sa bai taba fadawa irin wannan makamancin halin ba baitaba ganin bala'i irin wannan ba amma sai gashi yanzu da tsufa yazo masa wannan masifar ta sameshi shida baisani ba ko Allah yayi laifi ya jarabcesa da wannan masifar ta mutanen nan,

da sauri matar ta kara tashi daga wajen baba ta koma wajen hamza rungumo shi tayi tana cewa kayi hakuri nasan duk ni najefa ka cikin irin wannan halin nacuci rayuwar ka da naturo ka nan amma kayi hakuri nima bada son rainaba bani da zabin da ya wuce inyi hakan hakan shikadai ne mafita agare ni kayi hakuri,
cikin sanyin murya yace umma nasani ya isa haka kiyi hakuri kidaina wannan maganar dan Allah,

Azeema ganin baban ta ya farfado yasata rarrafa da kyar taje wajen sa tana so ta tashi amma takasa, shikuma baba har yanzu baiganta ba,

ganin hakan yasa hamza raba jikinsa da na mahaifiyar sa yayi wajen su Azeema duk da yayi mamakin ganin yanda Azeema ta damu da baba amma yanzu ba wannan lokacinne dashiba yafi barin abun akan kawai ta tausaya masane amatsayin sa tsoho shiyasa tafi tausaya masa,

yana zuwa wajen ya dagota da kyar ta samu ta iya zama da mazaunan ta,

kuka ta fashe da shi tare da dora hannun ta akan sa tace baba da kyar baba ya iya juyo da kansa yasauke idon sa akan da sauri ya mayar da idon ya rufe tare da kara budesu dan ya tabbatar wa dana kansa abun da yagani,

ba karamin mamaki yayi ganin dai dagaske itadin ce,

Ahanakali ya yaɗaga hannun sa zai taɓata tayi saurin riƙe hannun tana ƙara fashewa da kuka tana cewa baba baba katashi karka mutu dan Allah katashi mutafi gida...

ahankali baba ya ƙoƙarta tashi tare da taimakon hamza yaƙarasa zama shima yana zama Azeema ta faɗa jikin shi ta rungume shi sosai tana kuka shima saida ta zubar da kwalar tausayin ta daman mutumin da suka aika yazo yagaya musu yace yarinyar sa tace zatazo cikin gidan nemansa amma yasanar dasu ya dakatar da ita yace kar tazo ya gargaɗe ta kar abarta tazo shiyasa baba bai taɓa tunanin zatazo ɗin ba ashe kwa sai da tazo yanzu gashi za ayi biyu ba ko ɗaya ita bata fita shi baifita ba daman abun da wancen mutumin yayi musu gudu kenan kuma gashide saida hakan ta faru,

da mamaki Hamza yake kallon su Saida yabari suka ɗan tsagaita da kukan kenan sannan ya dubi baba yace baba "kasanta ne daman?

kai baba ya ɗaga masa tare da cewa "ƴata ce zaro ido Hamza yayi ba ƙaramin mamaki yayiba jin wai ƴarsace daman ƴar sa yake so duk loƙacin da ya haɗu da ita basu taɓa haɗuwa da baba sai yau yauɗin ma cikin mawuyacin hali irin wannan da ba damar farin ciki saidai ma baƙin ciki gaskiya baiso ta wannan hanayar suka haɗuba da yasan hakane ai da tuni ya haɗasu kash rashin sani yafi dare duhu,

itama matar gurin ta tsugunna tunda yanzu kamar sarki yabasu damar su tattauna ne dan ita atunanin tama ko angama yimusu hukuncin ya rabudasu shiyasa ya dakatar da sauran ga dukan su,

zama tana zama tace Alahamdulillah naji daɗe da ka farfaɗo da Allah yasa baka mutu ba, kallon ta ta mayar ga Azeema tace sannu yarinya wannan mahaifin kine ko kai Azeema ta ɗaga mata,  sannan ta ƙara cewa amma me yakawoki gidan nan, shiru tayi bata bata amsaba tana tunanin ya za'ayi ta gaya mata agaban sarki ta karawa kanta laifi shiyasa tayi mata shiru,

Hamza zaiyi magana kenan saiga wannan mutumin da yafita yadawo da sauri ya shigo yana haki yace ranka yadaɗe angama shirya komai fitar su kawai ake jira,

bayan ya shigo sai ga wasu mutanen wajen guda shida manyan maza dan su ko uniform ma irin na bayi babu ajikin su suna shigowa sarki ya umarcesu da su ɗauke su baba afita dasu inda yace,

mutum ɗaiɗai aka fara ɗaukan su baba aka fara ɗauka Azeema nata kuka tana rirriƙeshi taƙi saki daga ƙarshema saida tasamu tuƙwicin mari zafafa guda biyu sannan tasakeshi aka fita dashi itama wasu suka ɗauketa suka fita da ita sai matar da ta shigo tana tayi musu masifa su sauketa wallahi zata ɓata musu rai amma basu saurare ta suka fita da ita, sunzo ɗaukan hamza, Hamza yace musu dalla malamai kar ku taɓani zan fita dakaina wanine yabiyo ta bayan sa gabuga masa katako akai yace kai akomai saika nuna taurin kai ko to bari muga iya ƙarshen taurin kannaka dafe kansa yayi take yaji yana yimasa wani irin ciwo bibbiyu yafara gani yana niyar faɗuwa wani yajawosa ya miƙar dashi ya tsaya da ƙafafun sa sannna suka shiga tura ƙyayar sa suna dukan sa suna turasa ahaka suka fita dashi daga fadar,

bayan fitar su sarki da masu rufa masa baya suka bi bayansu suma suka fita,

afarfajiyar masarautar aka jeresu da ƙuƙƙule musu hannuwa da ƙafafu,

ƙarasowar sarki kawai ake jira afara zartar da hukuncin da yace ayi musu gefe guda kuma wasu mugayen wuƙaƙene masu kaifin gaske wanda ana ɗora ma ita zata iya yanka ka,

guri har yafara taruwa da mutane sunzo kallo,

sarki na ƙarasowa gurin yasa aje akirawo fulani dan tazo a yanke hukuncin agabanta,

kowa na gurin sai mamaki me suka aikata haka za a yanke musu hukuncin kisa dan andaɗe ba ayi hukuncin kisaba Saida ahukun ta mutum ta wani fannin daban amma banda kisa yau kuma gashi za ayi daga gani to ba ƙaramin laifi suka aikata ba wasu kuma sunsan laifin da sukayi wasu su tausaya musu masu jin haushin Hamza kuma nayi masa Allah yaƙara duk dade sun tausayawa masa saboda duk wanda yaga halin da yake ciki sai ya tausaya masa basu kaidai bama har sauran gaba ɗaya abun a tausaya musu ne domin sunji jiki ba kaɗan ba gashi kuma za aƙara musu da kisa.....

magana har ta fara karaɗe masarauta yau za ayi hukun kisa har mutum huɗu tofa kowa fitowa yake yaga suwaye haka kuma wane irin laifi suka aikata,

ana cikin haka saiga motar sam nan ta shigo tundaga nesa yake kallon gurin taron da mutane suka cika amma dai baidamuba saboda inda sabo yasaba ganin yasan bazai wuce halin nasu suke ba na cutar bayin Allah tsaki yaja tare da cewa gobe inyanzu wani zancen aike ba wannan ba kuyi na ƙarshe ku gama yaune ranar ku ta ƙarshe cike da taƙaicin halayen su na masarautar ya ƙarasa parking lot shidaman arayuwar sa ya tsani wannan mulkin da sukeyi da bashida wani amfani dan baiga amfanin sa saboda ba abun da akeyi asauran masarautu suke ba su nasu na mahaukata suke bana mutane ba abu kwata kwata babu tsari ba a san me yakamata ayiba da abun da bai kamata ba yamaji daɗin  zuwan waɗannan bayin Allah, haka yai ta saƙe saƙen sa shikaɗai, saboda shikaɗai ya shigo, ya ajiye shettima agida,

fitowa yayi daga motar ya nufi part ɗin fulani jikin sa duk akasalan ce babu daɗi so yake kawai yaji sa akwance yana buƙatar hutu sosai kwakwalwar sa ta huta..,

akan hanya sukayi karo da fulani ta fito afusace cikin fushi ko takansa bata biba ta wucesa fuuu kamar zata tashi sama,

binta yayi da kallo kawai tare da girgiza kai yayi wucewar sa ciki,

kamar anjefota gaha fulani tashiga wajen taron tunda tashiga kanta yana kan hamza ganin sa cikin mawuyacin hali irin wannan hakan ba karamin dadi yayi mata ba,
Chapter 109 · 0% Book details