← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 139

Sashe 40

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  "daga mata kai tayi tace eh naga alamar itace babba duk wanda yace shine to bashi bane kemeyasa kike son shekaru haka,
  "Amra tace au hakama zakice to shikenan ba ruwana dake tunda kema ƙaryata ni zaki tafada tana ƙoƙarin miƙewa daga gurinbarin wajen kamota Ameesha tayi tace yi hakuri na yarda kece babba ni inkina soma sai inƙara miki da nawa shekarun dan murmushi Amra tayi sannan tace Allah ya taimake ki kinyarda amma da nikadai nasan zaman dazanyi dake saboda ƙaryatanin da kikayi to ai shikenan yanzude komai ya wuce tunda nayarda,
hamra dake jinsu tana saka kaya bata yanka musuba ta juyo tace ƙawata kema kirabu da ita kike kiyi wankan kafin akawo mana abincin ba musu ta ce to tare da miƙewa daga gurin Amra ce tayi saurin tashi tace zo kikarbi towel tafada tana nufar inda suke a sakale ɗaukowa tayi ta bata tana karba bata cire kayan agun ba ta tashiga ahaka da kayan jikinta bata daɗe ba tafito bayan tayi wankan sai ta maida kayan jikin ta tan fito duk suka bita da kallo Amra tace naga kin mayar da kayan da kika cire kinga fa waɗanda na ɗauko miki kallon kayan Ameesha tayi sannan ta qara kallon ta tace "a'a Nagode wannan is ok ai dazan fito nasaka dan hade rai tayi tace Allah sai kinsaka su,
hamra ce ta karaso wajen da take itama ɗauke da kaya ahannun ta tace dallacan ko zata sakama naki zata saka to nawa zata saka ungo dan Allah kicire waɗannan kisaka wannan Amra ce ta fusge kayan tace Allah nawa zata saka inbanda neman fada ma bani nafara bata nawa ba itama hamra tace nata za asaka itade ta zuba musu ido sunatayi kowa yaqi hakura suna cikin haka momma tashigo dakin tsayawa tayi tana kallon abun da sukeyi Amra ce tafara ganinta sai tace yauwa momma gwara da kika shigo kizo kiyiwa hamra magana tabari tasaka kayana mifa nafara bata nawa shine itama wai saidai tasaka nata kuma wallahi momma na rigata qaraaowa tayi sai ta karbi kayan gaba daya sai ta dauki ɗaya tabawa Ameesha tace saka wannan kuyi sauri nace baza akawo muku nan ba kufita muci gaba dayan mu,
  "gwalo Amra tayiwa hamra saboda kayanta momma ta karba tabawa Ameesha,
ita kuma Hamra haushi taji ta hade rai daman tasan hakan zata faru tunda taga shigowar momma tasan shikenan momma na Amra zata bata,
Momma da ta lura da fushin da hamra take da harzata shareta sai kuma tafasa kawai sai tace ke kiyi hakuri tunda kece babba kuma ba ga ta nanba sai inroqi abarta tunda gobe ba makaranta sai ku zauna kinga kema sai tasaka naki gobe ba shikenan anraba ba,
sakin fuskarta tayi harda dan murmushin ta tace to shikenan momma dama abarta muyi weekend dinnan tare wallahi naji dadin haduwa da ita,
momma tace to saidai yayan naku yadawo sai ku tambashi da kanku ko ku tambayi yayanta danagansu tare kuma sunce tare zasu dawo cike da murna gaba ɗayan su suka hada baki wajen cewa Allah yasa abarta momma, tace Ameen,
"bayan Ameesha tagama saka kayan sai momma ta tura su suka fita daga dakin zuwa falon dan cin lunch,
agurin cin abincin ma saida suka kusa fada sude fada baya musu wuya komai ma nafadane haka ake fama dasu Hamra son girma da kuma tsokana ita kuma Amra rashin hakuri da indai tai mata sai ta rama ta wani bangaren Amra tafi hakuri kuma tafiya sauqin kai da saurin fahimtar abu saboda ita sai ka tabota kuma akwai yawan wasa dan ita sai taimaka magana wanjen goma amma bata gaskiya aciki kawai tayine awasa kuma koda kayi mata laifin da yabata mata rai to data rama anwuce wajen zata manta dashi saɓanin hamra da ita bata san wasa ba gashi wataran ita zata fara tsokanarta da fadan amma kuma ita idan tayi mata sainata ran yabaci ga riqo akwaita da riqo indai kayi mata abu ko bata ramaba to yana nan aranta dan badan Amra bata biye mata da tuni sunfara 'yar gaba saboda abu kadan yahadasu sai tafara daina mata magana itakuma Amra sai ta kurata to bayanda zatayi dole ta sauko shiyasa suke yawan samun saɓani saboda halinsu baizo ɗaya ba kuma kowa bazai barwa kowa ba idan rigimar ta tashi ahakama dan anayawan tsawatar musu akan kuma hana fadan dokeke acikin gidan shiyasa komai zasuyi iyakacin su na fatar baki,

    "Bayan sundaidai ta parking agaban gidan prison din suka fito gaba dayan su tare da nufa ciki bayan sun shiga suka sanar da wanda sukazo nema akayi musu iso har zuwa office dinsa suka shiga su suka bayan sun suke qara sanar dashi daga inda suke da kuma abun da yakawo su duk da yariga da yasani amma saida suka qara yimasa bayani,

ba bata lokaci yafara yi musu nasa bayanin,

  kamar yanda nagayawa mahaifin ka gaskiya lokacin da abun yafaru banine anan ba saida yanzu zamuje daku kuduba ko ina idan kun ganshi to sai afara binciken inda file dinsa yake inyaso ku kuma sai shigar da qarar,
sam yace idan kuma ba anganshiba kana nufin baza mugansa ba shikenan ko ko me kake nufi,
da mamakin maganar mutumin yake kallon sa ganin shi ko ajikinsa maganar da yayi tunawa da ko shi waye sai kawai ya kawar da mamakin sa, yadanyi murmushi sannan yace bawai haka nake nufi ba ai ganin nasane zaifi sawa mugano bayanen sa da wuri amma idan baya nan kaga abun zai bamu wahalar gano inda yake kamar yanda kukayi min bayanin cewa tun alokacin bayan an hamada haduwa da kowa kaga kwa mai yiyuwa ne ace suncanza masa guri tunda har basa so azo wajen sa,
yanzude abudaya zamuyi muje afara bincikawar idan babu shi zanduba cikin sunayen da suka yi aiki anan inayaso sai muduba na shekarar da yayi aiki anan koda yanzu baya nan sai muneme shi ko ya kace nidai inaganin wannan ce hanyar da Yakamata mubi dan inada tabbaci kaf cikin gurin nan ma baifi kasamu mutum biyarba waɗanda suna nan tunwancen lokacin har zuwa yanzu wasu dayawa sunbar nan wasu anyi musu transfer wasu kuma sunyi ritaya tunda gaskiya andade,

shiru yayi yana kallon su danjin bun da zasuce game da bayanin da yayi musu, Shiru sukayi gaba dayansu saida ga bisani Shettima yace hakan yayi dole abi ta wannan hanyar yanzu kamata yayi aje aduba din gashi ma kuma matar tagaya masa inda dakin yake kaga shiga kawai zamuyi inba ya nan sai ko tambayane muyi dan nima bana tunanin zasu barsa anan haryanzu,
sam ne yaja dogon numfashi tare da furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya miƙe yana zagaya office din tare da saqale hannun sa abayan sa batare da yace komai ba saida yayi yan mintina sannan ya juyo yana kallon sa da shima shi yake kallo aransa yana mamakinsa,

ba dubawar da zamuyi yanzu abun da za ayi shine kawai ka dauko mana record din naku aduba sunan mutumin da yakarbi case din ta kansa zamu fara ai bama yacikin prison dinan dole sunfita dashi mutumin zamu fara nema kafin muyi komai shizamu fara kamawa zai fadi inda yakaishi kafin ya sauka,

shiru mutumin yayi yana nazarin maganar sa kafin yace masa gaskiya yanzu baida alhakin da zai iya basu wani abun dole shima sai yayi magana da manyan sa kafin yabasu
Shettima yace kamar nanda yaushe zakai magana da sudin yace musu subashi nan da gobe ma sai sudawo,
nande ba wanda yaqara cewa komai banda kallo da sam ke binsa dashi babu abun da yake wanda kallon nasa har saida yasa mutumin yadan fara tsarguwa da kallon da irin kallon da yake masa,
baide kulasaba har suka miqe tsaye su shettima sukayi masa godiya sannan suka fita daga ofishin,

yana ganin fitar su hannun sa har rawa yake wajen saurin dauko wayar sa yadannawa wata number kira ana daga ya sheqe da dariya sannan yace ka kwantar da hankalin ka har na tsarasu sunma tafi yanzu haka ma inajin sun shiga mota nace gobe su dawo nikuma kafin goben baza su qara ganina ba duk sanda sukazo zance musu bana nan mahaifin nasama zanyi blocking din number sa ta yanda bazai qara samu naba duk wata hanya da zata hadamu dasu Bazan bari su ganni ba bare hartakai ga na basu sunanka daga can bangaren aka bashi amsa da cewa yauwa aikin ka na kyau zansa aqara maka salary wannan watan zaka samu kaso me tsoka kaide Kaci gaba da abun da nasaka inbahaka ba kuma kasan halina koda wasa karka kuskura kagaya musu inda nake kajini yana washe baki yace angama baza sutaba sani ai kasanni da iya aiki daga cen mutumin yace ai saboda haka na ɗoraka akai nasan zaka iya fiye da hakama jin anyabeshi yasa shi qara washe baki yana yimasa godiya daga nan sukayi sallama ajiye wayar sa kenan yamaida kansa jikin kujera yanajin dadin qarin kudin da za ayi masa,
kawai yaji anturo qofa kallon qofar yayi dan ganin me shigowa zunbur yayi ya miqe yana binsa da kallo baigama kallon sa saiga sauran nan sun shigo suma wani qarin abu yahadiye da ya tsaya masa amaqogaro da tunanin me kuma yadawo dasu bayan sun tafi karde ace sunji maganar da yayi wata zuciyar tace taya za ayi sujika bayan qofar arufe take kuma na waje bai isa yaji na ciki ba sauke ajiyar zuciya yayi duk alokaci guda yayi wannan tunanin tare da dan basarwa harda qaqaro murmushin dole tare da cewa a'a kundawo ku kunyi matuqa ne yafada yana qara binsu da kallo tare da komawa kan kujerar yayi zamansa hankalin sa kwance,

Shettima mane yace eh munyi mantuwa abun da muka manta shine baka fada mana sunan wanda ya sauka ba kafin ka hau tunda dole daga shi saikai kaga dole zakasan sunan shi,
wanidan qayataccen murmushi yasaki tare da cewa taya zanyi insani dana sani ai da tun dazu nagaya muku ai shiyasa nace kubari sai zuwa gobe sannan na binciko ko waye,
Chapter 40 · 0% Book details