← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 139

Sashe 129

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dadda ce ta fito daga ɗaki tana cewa wallahi kiyi saurin kiransa kar ya kashe min jika dan bazan yarda ba sai nayi shari'a da mutum idan wani abu yasamar min shalelena wannan yaron da ba imanine dashi ba komai ma zai iya yi mata wallahi,

maama tayi dariya tace to meye ai ita tafara tsokanar sa ni nama fasa kiran suci kansu tafara girmama sa daman na fuskanci ta rainasa gwanda ma ya koya mata hankali, tayi maganar cike da tsokanar dadda,

dadda tace "da kwa ankwashi ƴan kallo agidan nan dankwa kowa sai abun ya shafeshi idan kuna son zaman lafiya to kar abari wani abu ya shafi shalele na ehe idan ba hakaba kuma kowa ya kuka da kansa bazamuga kowa da gashi zamu yage masa rigar mutunci ba,

haka sukaci gaba da hirar su cikin raha daga ƙarshe dai su Amra sukaje suka sanar da ummy saƙon maama amma da takira wayar sa tana ta ringing ba aɗaga ba sai daga baya aka ganta a falo ashe baima fita da itaba, haka duk kowa yayi tagumi ana jiran dawowarsu......, da addu'ar Allah yasa kar yayi mata komai............,

        **********************
tunda suka fita yake kwarara gudu, Ameesha ta rakuɓe agefe ita kuma sai faman raira masa kuka take zuwa yanzu ta fara fita hayyacin ta kuka take kamar ranta zai fita,

duk kukan datake akan kunnen sa yanajin ta amma bai fasa gudun da yake ba, saida suka zo wajen danja da aka dakatar dasu sai loƙacin yasamu ya taka burki ya tsaya nadan ransa yaso ba,

jin kukan nata ya isheshi yasashi juyo ya kalle ta tare da daka mata tsawa,yace  "ki rufewa min baki kafin in karkar yaki agunanna ubanki namiki na taɓaki da zakizo kina cikamin kunne da wata ƙatuwar muryar ki yakama ki adana kukan ki saboda gaba zai miki amfani ba yanzu ne loƙacin da yakamata kiyi saba kibari mu sauka saikiyi me dalili, wallahi naƙara jin muryar ki saina canza miki kamanni agunnan nonsense yafada tare da buka wani tsaki ya mayar da kansa bakin titi yana ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa,

ɗif tayi bata ƙara bari sautin kukan nata ya fito ba hannu kawai tasaka ta toshi bakin ta tana yi ƙasa ƙasa jikin ta kuma sai faman ɓari yake ji tayi wata irin tsanar sa ta darar mata a zuciyar tsanama wacce inajin tunda take bata taɓa ji tayiwa wani ba haka takejin ta yanzu loƙaci ɗaya,

ana basu hannu yaƙara kwasar motar kamar yanda yake yi yacigaba da gudu, dan gudun ma kamar yafi na farko,

har wani ama"amai take ji na taso mata saboda gaba ɗaya hanjin cikin ta yagama kaɗawa cikinta ya ruɗe duk tabi ta furgita gashi kuma ya hanata kuka, duk yanda taso ta daure kar kukan yafito amma ina yafi ƙarfin ta saida yafito fili harda su tari da ya sarƙeta,

da ƙarfi yataka burki da saida kanta ya bugu da kujera taƙara yin baya, ba ƙaramin faɗuwa gabanta yayi ba dan tayi tunanin ma motar ce take juyawa,

bata gama tantance wannan azabarba yasa hannu yajawo gashin kanta daman mayafine ajikinta shima iya kai ko ɗan kwali babu,

da ƙarfi yaja gashin tare da ɗagota dashi ahaka yajawo ta daga baya ta dawo gaba ya wurgata kan kujerar gefen sa, sai ya buɗe wani guri ajikin motar ya zaro wata ƴar ƙaramar wuƙa, yasaitata akan wuyan ta yace "wallahi idan baki min shiru ba sai yanka ki da ita, kiƙara cewa uffan kiga yanda zan gunduwa gunduwa da namanki acikin motar nan, inkashe ki na kashe banza dan ubanki mai kama da miyagu, atai miki magana ke bakijin magana kin raina mutane so kike ki fasa min kunne, to ni kafin kiyi min illa bari ni inmiki yana faɗar haka yadanna wuƙar awuyan ta kamar zai yanka ta sannan ya ɗauke,

saura kaɗan Ameesha ta sume agun dan bata taɓa tunanin wannan muguntar tashi takai haka ba bata taɓa tunanin zai iya kisan kai ba ashe bayan dukan mutane da yake har kashesu yakeyi daman tare take da makashi bata sani ba,

ai ba ƙaramin tsorata tayi ba ko kallon inda yake bata ƙara yiba ta matsa gefe ta rakuɓe jikin ta na kerma yake ga kanta da yafara yi mata wani irin ciwon azaba,

tayar da motar yayi yaci gaba da tafiya har suka ƙarasa gidan,

saida yazo dab da gate ďin sannan yayi parking ďin motar yafita ya zuge gate ďin ta sannan ya dawo ya kuma budewa ya shiga motar sannan yaja yashiga ciki. yana gama daidaita parking ya buďe ya fito baibi ta kanta ya koma ya rufe gate ďin, har yaje ya dawo bata fito ba,

wajen motar ya koma ya buďe da kansa yana buďe wa tayi baya zata koma baya ya jawo ta ya fincikota ya fito da ita waje,

gefen rigarta ya riqe ya fara janta ita kuma tana kwacewa da tagadai da gaske ciki zai kaita tafara basa haquri amma yaqe sauraron ta,

ta manta da laifin da tayi masa tunfarko ta qara kai baki zata cijesa aikwa ya riqo bakin ha matse kamar zai fasa mata shi haka ya matse mata shi, tana kuka tasaka hannu tana qoqarin kwatar bakin  ya kuma  riqe ďayan hannun  nata ga murďe shi har sai yayi  qara sannan ya sake  ta yaci gaba da janta har yakaita cikin falon yana shiga ya jefata ciki ta faďi qasa saura kaďan kanta ya bugu da center table  dake tsakiyar falon Allah ya tsagaita mata wahala ya kareta bata kai ga buguwa ba yasa ka hannu ta dafesa,

loqacin da suka shigo anfara kiraye kirayen sallahr isha'i  dan haka sai babi ta kanta ba ya juya zai fita har ya kai bakin qofa sai kuma ya tsaya haďe da juyowa ya wurga mata wani banzan kallo sannan yace "ko da wasa kikayi kuskuren fitowa na lahira sai yafiki jin daďi yana kaiwa nan yayi fice abunsa,

ko kallon sa batayi ba saida ta tabbatar da yafita tayi saurin tashi zaune tinanin yanda zata samu mafita ta shiga yi yanda zata kare kanta daga haďuwa dashi,

jitayi kamar tafiya tayi tunanin ko shine ya dawo aguje ta miqe har ra doshi ďakin da ta kwana tana zuwa tajisa arufe arikice ta juyo ta qara nufar ďayar kofar nanma takasa buďewa babu qofar da  bata gwada buďewa ba amma duk sunqi buďuwa,

qofar shigowar taqara kalla tajidai har yanzu bai shigowa sai kai tayi sauri taqarasa gurin qofar taci sa'a kuwa kye ďin yana jikin qofar,

sai kawai tayi sauri ta rufe qofar ta kulle harda su zira saqata ajiki sannan tabar muqullin ajiki saboda koda ya zira wani bazai buďu ba,

duk da atsorace take da zaman itakaďai amma ta gwammace ta zauna ita kaďai akandai yadawo yasameta aciki, dan tunanin tama kawai wuqar ya tafi ya ďauko kasheta zaiyi shiyasa ta rufe ta koma kan kujera ta zauna cike da tsoro da fargaba jikin ta sai rawar sanyi yake abunne ma yahaďar mata biyu ga tsoro ga sanyin garin shiyasa take rawar ďari,

tana zaune agun har tsawan loqaci bataji dawowar saba wani tunanin ne yafaďo mata kodai tafiya yayi yabar ta ita kaďai tunanin hakan yasa ta tashi da sauri ta taje wajen  window ta yaye labulen ta leqa waje sai ta hango motar agun ajiyar zuciya ta sauke ganin bai tafi ba tana niyar barin wajen kenan ta hango shigowar sa da sauri ta saki labulen ta koma inda tame ta zauna gabanta na qara faďuwa tafara addu'ar Allah kawo mata ďauki Allah yasa dadda tazo ta taimaketa..........,

bugun zuciyar ta ne ya ƙaro loƙacin da tajisa kusa da ƙofar yana murɗawa alamar zai buɗe ƙara ƙanƙame jikinta tayi ajikin kujera jikin ta nacigaba da ɓari,

ba ƙaramin mamaki yayi ba ganin ƙofar arufe da alama rufeta akayi ransa yaji yaƙara ɓaci ga sauran muƙullan suna cikin falon har muƙullin motar yana ciki ya ajiyesu loƙacin da zaiyi alwala,

buga ƙofar ya shigayi da ƙarfi kamar zai ɓalle ta,

cikin ɗaga murya yace "ki buɗe ƙofar nan wallahi kika bari na shigo sai ranki yayi mummunan ɓaci ki buɗe,

tana jinsa amma ki motsawa batayi ba  haka yai ta bugun ƙofar nan taƙi buɗewa, haƙura yayi ya nufi wajen motar sa yajata ko zata buɗu amma yajita arufendai da yabar ta taƙaicine ya isheshi yarasa samun mafita,

dawowa yaƙara gurin yaƙara bugawa bata buɗe ya koma wajen window ɗin suma arufe suke ta ciki tashin hankali wanda ba asamishi rana yau wannan ƴar kucililiyar yarinyar ce ta rufe masa ƙofa rainin har yakai yana mata magana tanajin sa tayi masa banza idan kwa yakamata ta shiga uku sai ya kusan karya ta wallahi abun da baiyi niyar yi mata ba tajawa kanta sai yayi mata abun da bata taɓa tunani ba aidai dole ta buɗe tunda ba aciki zata kwana ba,

samun wani ɗan guri yayi ya zauna yana jiran buɗewar ta acewar sa idan tagaji da zama ita kaɗai zata buɗe,

gugugu gari yaɗauki kukan hadari loƙaci ɗaya ya turniƙe da haɗowar wani gagarumin hadari,

zunbur ya miƙe daga gurin cike da tashin hankali da fargaba da ruwan samane kawai yake haddasa masa tsoro da fargaba saboda ko ɗigon ruwa ba ya bari ya taɓasa indai ya taɓasa har suma yana iyayi baya son ruwan sama ya taɓasa saboda akwaisa da jin sanyin aɗan ƙanƙanan loƙaci sanyi yakesawa ya fita daga hayyacin sa inda kagansa hankali kwance ana ruwa to yana ɗaki aduƙunƙume aciki bargo yana bacci shine kaɗai kwanciyar hankalin sa,

asukwane yaƙara zuwa kusa da ƙofar yayi mata wani irin mahaukacin bugu wai ko zataji tsoro ta buɗe amma taƙi buɗewa,

cike da raunin murya da yasan bashida wata hanya da ta wuce wannan yace "pls ki buɗe I promise you bazan miki komai ba kibuɗe hadarine agarin kar ruwa ya sauko,

kamar tana gabansa ta maƙe kafaɗa alamar bazata buɗe ba haka yayi tayi mata daɗin baki ta buɗe amma taƙi buɗewa acewar ta wayo zaiyi mata shiyasa yabiyo ta wannan hanyar dan ta buɗe yasamu damar cin uwar ta,
Chapter 129 · 0% Book details