← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 139

Sashe 127

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace meer yazo gaban yana binsa da wani irin matsiyacin kallo sannan yace kawo number mutumin da yake kiran ka, dan Meer akwai karantar mutum yagama karantar sa kuma ya yarda da duk abun da yafaɗa shiyasa ma baiƙara kai masa mazgaba,

kai mutumin ya girgiza yace watar tana can gidana na abuja basu bari nataho da ita ba,

sam yace "mundauko ta ai tana office, saidai aje can aɗauko yanzu,

Papa da tun ɗazu yakasa magana sa yanzu ya samu damar cewa "basai kunje yanzu ba kubari agama komai zuwa anjima sai kuje, da "to" sam ya amsa tare da samun guri yazauna,

shiru gurin ya ɗauka kafin daga baya papa yace za a iya mayar da su inda aka ɗauko su sannan suje suyi sallar la'asr,

kamar baban sumayya zaiyi kuka haka ya durƙusa aƙasa yace dan Allah tund dai banda laifi kutai maka ku barni intafi gida dan Allah kusake ni intafi yayi maganar sada kansa ƙasa hana addu'ar Allah yasa su barsa ya matsu yaje yaga ƴar sa,

buɗar bakin papa kam yace ba matsala zaka iya tafiya amma koda yaushe idan wani abun yafaru da ya shafeshi zai iya jin kira ya zauna cikin shiri,

cike da murna da farin ciki yace "ya amince koda yaushe ake buƙatar sa zaizo,

saida aka ƙara gargaɗin sa da ja masa kunne haɗi da ƴar ƙaramar nashiha akan yaguji abun duniya komai zaiyi ya tsaya iya gaskiyar sa yanzu gashi yajawo kansa duka da kwana wani wajen batare da sanin iyalan saba ya kiyayi cin hanci ko nan gaba domin hakan ba inda zaikaisa saidai ya kaisa yabaro sa,

sosai jikinsa yayi sanyj yayi da nasani daman tun ba yauba tun ranar da sam ya dake sa agaban ƴar sa yake nadama, dan haka yayi masu godiya yayi wa kowa sallama harda wanda aka kamosu tare da yake ji kamar ya bisa, bayan yayi musu sallama sannan ya miƙe tsaye yajuya zai fita har yakai bakin ƙofar zai buɗe sai kawai yaji ance RABI'U......cak yaja yatsaye sakamakon jin muryar wanda bai taɓa tunanin jintaba a irin wannan loƙacin batare da ya juyo ba yafara ko kwanton anya kuwa muryar da yaji daidai kunnuwan sa suka jiyo masa amma kuma yana da tabbacin ko amafarki yajita yasan ta wace dan bazai taɓa mance taba,

ahankali yashiga juyowa har yagama juyiwa gaba ɗaya yanda ya zuba musu ido haka suma ƴan ciki suke kallon sa,

ɗaya bayan ɗaya yafara binsu da kallo dan yaga ta inda mai muryar zai fito yaji muryar sa amma kuma gashi baigan sa,

Abu ne ya miƙe tsaye sannan yafara takowa ahankali har zuwa gaban sa yakafe sa da ido kallon kallo suka shiga yiwa juna,

saura kaɗan baban sumayya ya faɗi ƙasa yayi saurin dafa bango yana zaro ido tsawon minti biyar yakasa magana shima kuma abu bai masa magana,

sai da ƙyar baban sumayya ya iya ɗaga hannun sa ya shiga nuna sa da yatsa yana mamar mamar da baki yanaso yayi magana amma yakasa da ƙyar dai ya daure bakin nasa ya buɗu yace "umaru ru......,

na'am Abu ya amsa masa yana kallon sa tare da harɗe hannun sa aka ƙirjin sa, yana sake ƙare masa kallo,

abun mamaki sai kawai hawaye suka fara sauka daga idon sa cikin hawaye yace "daman kana duniya daman zan sake ganin ka arayuwa ta babu irin neman da banmaka ba umaru nayi neman har nagaji har garin Lagos naje bansame kaba daga ƙar she nahaƙura ashe da rabon sake haɗuwar mu aduniya ashe bazan mutu da zunubin ka ba dan Allah ka yafe min abubuwan da nayi maka abaya da abun da mahaifiyata tayi maka na roƙeka ka yafe mata dan ta cutar dakai arayuwa yaƙara sa maganar yana zubewa aƙasa yana dafa ƙafar Abu hawayen sa har yana ɗiga kan ƙafar sa,

Abu baisan loƙacin da shima yaji hawaye na zubowa da sauri yasaka hannu ya share hawayen tare da tsugunna yasa hannu biyu yaɗan bubbuga kafaɗun sa sannan ya ɗagosa ya miƙar dashi tsaye tare da rungume sa rungume juna sukayi,

kowadai na falon sun zuba ido suna mamakin wannan sanayyar da tasu a ina suka san juna haka, har da su kuma,

Abu ne yaraba su sannan ya kamo hannu sa suka dawo ciki, ba tare da ya zauna ba yakalli su Abu da suka tsare su da ido suna jiran ƙarin bayani,

kallon su yayi sannan yace "wannan bawan Allahn da kuke gani ƙani nane koma ince kusan sa'ani muke dashi agidan da nafara tasowa na tsinci kaina kafin daga bisani kuma muka rabu sai yau Allah ya haɗa mu,

bayan yagama gaya musu kafin ma yayi magana ya maida dubansa ga baban sumy sannan yace "Rabi'u ai kaman ta da komai yafiya kuma babu abun da kukayi min nima na daɗe ina cigiyar ku bansa meku ba tunda natafi da na dawo akacemin kun tashi haka na koma naci gaba da rayuwa ta ni kaɗai nakama kasuwan cina har Allah yayi min arziƙi nama bar ƙasar naje nayi aure har bayan na dawo ma na kuma bada cigiyar ku gidan radio amma shiru tun ina neman ku har na haƙura zan cen da nake maka yanzu haka bandaɗe da sanin ma ba mahaifin mu ɗaya ba dakai sai kwana biyu da suka wuce nasan hakan, sakamakon haɗuwa da mahaifiyata ta gaskiya da mahaifina ga kuma dangina babu abun da zance sai godiya ga mahallici na,

yanzu waɗan nan dakake gani iyayena ne wannan itace mahaifiyata wannan kuma mahaifina ga ɗana kuma wanda kuma ake tuhumar ku akan ɓatansa kuma shima ɗan uwana ne ƙanine agare ni,

dan haka ni banda wata damuwa yanzu daman damuwata ɗaya ce ta inda zan sameku dan innuna farin cikin riƙe nin da mahaifinka yayi sai gaka kuma Allah ya haɗa mu nayi murnar ganin ka sosai, domin ko mai kukayi min arayuwa bazan taɓa mantawa dakuba saboda kun gama yimin komai ko ince mahaifin ka yagama yimin komai arayuwa tunda har ya ɗauke ni aloƙacin da bansan kowaba banda komai har ya raineni na mallaki have ankalin kaina kafin ƙaddara tazo ta rabamu, idan ban yafewa iyalen aba ai bancika ɗan halak ba banyiwa kaina adalciba zan kasance ɗata daga cikin masu yin butulci nikuma ba butulu bane....ɗan dakatawa yayi da maganar sannan yaɗan yi murmushi tare da kara kamo hannun sa yace "Rabi'u ina so kamanta da komai kabar tuna baya kasa ma kamar babu wani abu da yataɓa faruwa tsakanina da kai na rashin jituwa da makaman cinsu komai ya wuce yanzu ka zauna anan idan muka gama komai zamu je dakai kaini wajen baffa inganshi harma da Inne itama inason ganin ta da sauran ƙanne na ina fatan duk kowa yana nan lafiya da ransa da lafiyar sa dai ko? yaƙarasa maganar tare da faɗaɗa fara'ar fuskar sa,

shiru Rabi'u yayi yakasa cewa komai saboda abun al'ajabin da yagama kasheshi wai wanda suke ɗauka abanza suke wulaƙan tawa da cin mutuncin sa da zarafi ashe yafi su matsayi shiɗin wani ne yafisu zaiso kwa haɗuwar sa da mahaifiyar sa da har yanzu tana nan yanda take taƙi canza hali yasan idan tagansa zuciyar ta sai ta kusan bugawa, sosai ya tsunduma kogin tunanin saida Abu ya taɓosa sannan ya dawo daga duniyar tunanin da ya luluƙa,

cike da raunin murya yace "saidai kayi haƙuri amma baffa tun bayan barinka gida ba jimawa Allah yayi masa rasuwa su Khadijah kuma duk suna nan ƙalau kowacce tayi aure da ƴaƴan ta,

Allah sarki baffa Allah yajiƙan sa yayi masa rahama Allah yasa ya huta, da "Ameen" gaba ɗaya falon ya amsa Abu yaji mutuwar nan sosai mutuwar ta dake sa ba haka yaso ba yaso yasameshi da ransa dan ya rama masa halaccin da yayi masa amma haka Allah ya tsara dan haka yayi ƙudirin taimakawa ƴaƴansa daga yanzu bazasu sake shiga damu ko ƙunci ba zai taimaka musu fiye da tunanin me tunani,

haka suka gama jimamin mutuwar sa akayi masa addu'a da gaba ɗaya mutanen dake ciki tun agurin baban sumy yafara kiran wasu yagaya musu bayyanar amma baigayawa mahaifiyar suba so yake ta gansa kawai,

har wajen magariba suna tare basu rabu ba kuma tun aloƙacin Abu yace masa ya shirya gobe yaje gidan da suka siya idan yayi masa sai ya zauna yabashi kyauta inma wani zaibawa yabawa dan yagama dashi sosai yayi masa godiya sannan yatafi gida ransa tas cike da farin ciki da murnar ganin Abu da kuma yafe masa da yayi jinsa yake yau kamar a aljanna,

mutumin da suka kamo kuma mayar dashi sukayi inda suka ɗauko su sanan kowa yakama gaban sa saboda dare yafara kusantowa,

ana tashi daga gurin sam da hankalin sa gaba ɗaya yayi kan sumy da ya ɗauko yakaita wani wajen bai ƙara bibbiyar taba duk da yasan baban ta yatafi gida kuma zai tarar bata nan hakan bai damesa ba kuma baijin zai mayar da ita yanzu sai yagama garasu sannan zai nemi mahaifin nata yaji wai wane irin zama take agidan kuma ina mahaifiyar ta take sai yaji labarin kafin ya yanke hukunci ya mayar musu da ita,

suna tashi kuwa ko takan su shettima baibi ba yaja Hamza suka fice daga cikin masarautar batare da su bossay sun lura da hakan ba,

duk suna zaune afalon maama ta kalli Meer dake zaune yana cin kayan ciye ciyen sa da yasaba, ta kalle sa tace "ɗan gidan gwaggo wai baka gajiyane da waɗannan kayan zaƙin baza ka zauna kaci abinciba saidai kaita cika cikin ka da kayan banza wallahi ka canza wannan halin inbahaka ba zaka zama lusarin namiji kadai jini ko,

ko kallon ta baiyi ba kuma bai daina cin abun saba,
Chapter 127 · 0% Book details