← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 139

Sashe 128

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameesha dake gefe ita dasu Amra sunyi shiru saboda dakatar dasu ɗin da yayi yace ko suyi shiru ko su fita da har zasu fita Amra tace dan Allah su tsaya ita tanaso tai ta kallon sa dan haka suka zauna basu fita Amra na ta aikin kallon sa kamar ta samu tv idan taga zai ɗago sai tayi sauri ta kawar da kanta su Hamra suna yi mata dariya ƙasa ƙasa Azeema ma kam tafi so su zauan ɗin dan jirgi ɗayane ya ɗebo sa da Amra,

Ummy ce ta shigo falon da sallamar gaba ɗayan su suka amsa mata,

tana ƙarasa shigowa ta ƙaraso ta kalli Meer tace "hayatee gurin ka nazo dan Allah ka tashi kaje gidan can kadai ji abun da Abu yace ba sai na ƙara nanata maka ba dan haka tashi zakayi kaje ka kwaso min kayan da na bari aɗakina duk masu amfani ne, yanzu ma inada abun danake buƙata kayi sauri kaje,

maama tace "gaskiya dai noma kashiga ɗakina ka duba idan da abun da namanta kataho min dasu,

bashi da yanda ya iya tunda maama tasaka baki dole yaje dan baice komai ba ya miƙe tsaye tare da nufar hanyar ɗakin sa dan ɗauko key ɗin motar, yana shiga ya kuma fitowa ɗauke da key ɗin ahannun sa,

yana fitowa maama tace bakaji ba juyowa yayi yana kallon ta,

"ga ƙannen ka kuje tare mana su rakaka yanzufa ka kashigo cikin dangi dole ka canza Wannan ɗabi'ar taka ka sauko karinga magana da kowa,

tsaye yana kallon ta kamar yasamu TV sannan daga baya yace suyi zaman su yana faɗar haka yaɗaga ƙafa zai tafi Ameesha tace "nima ka taho min da kayana suna nan ajakar ɗazu,

wani irin kallo ya watsa mata tasan za arina dan haka tana faɗa takawar da kanta gefe bata yarda ma sun haɗa ido ba bare taga abun da zai mata girgiza kai yayi aransa yace zanyi maganin ki,

ahankali yace "su taho yana faɗa yayi gaba,

maama ta ɗanyi murmushi tace ko kaifa to kutashi kuje Amra ce tafara miƙewa sannan sauran ma suka tashi Ameesha ganin da sune yasa bataji wani tsoron saba ta tashi suka fita tare suna zuwa suka gansa har yaje wajen motar da zasu fita,,

ƙarasawa sukayi sai duk suka tsaya suna jiran sa ya shiga sannan su shiga yana shiga kam suka buɗe baya gudan kar ace Ameesha ta shiga gaba yasa tafara shiga canbaya sannan Azeema sai sauran ma suka shiga,

tsayawa yayi bayan sungama shiga sai yaƙi jan motar, sunkai wajen minti bakwai agun sai kawai suka ga ya buɗe motar ya fito sannan ya buɗe tasu Amra ce afarko yana buɗe yace fito tayi zaton ko gaba zata shiga duk da tana tsoransa amma da sauri ta fito saidai kuma tana fitowa yace da Hamra itama tafito ba musu kuwa dolen ta ta fito,

suna jiran jin mai zaice sai yacewa ya nuna Azeema da hannu itama yace mata fito da sauri kam ta fito jikinta har yana ɓari dan hakan nan take tsoron sa bayama idan ta tuna da marin da yayi wa fulani take tsoron sa,

ganin Azeema ta fita yasa Ameesha tun kan yace ta fito ma tayi saurn matsowa zata fito tana daf da zuwa wajen ƙofar yayi saurin datse ta ya rufe ta aciki sannan ya koma gaba ya shiga yana shiga yayi wa motar key duk da mamaki suka shiga bin motar suna ƙwalalo ido Ameesha kam tuni cikin ta ya ɗuri ruwa take ji take kamar ta saki fitsari a wando tagane sarai yana sane yayi mata haka dan yarama abubuwan da tayi masa,

haƙuri ta fara bashi da magiya amma ko kallon ta baiyi ba ya tayar da motar tare da janta da mugun gudu ya ƙaraso gurin gate sarauka aka buɗe masa yaƙara kwasar aguje ya fice kamar zai tashi sama guri ɗata ta haɗe ta matse jikinta ta fara sakin kuma dan tun a iya nan ma tagama tsorata dashi tasan shikenan ƙamshinta ya bushe tunda tazo hannun sa ta kaɗe har ganyen ta bata da maitaimakon ta yau sai ta Allah wataƙil ma yau kwanan ta ta ƙare dan yasan idan yasaka hannun ajikin ta da niyar duka saidai ahaifi wata dan mutuwa zatayiii..............✍️✍️✍️

                     💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innoc
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 98

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

_Na haɗe har wancen page ɗin danayi last posting saboda baida yawa kuma daman banbawa number ba shiyasa na haɗe su a wannan page ɗin ina fatan kun gane, wanda ya   karan ta sai ya wuce zuwa inda ya tsaya wanda kuma bai karanta ba sai ya ɗora kawai,_

     "yanda yaja motar yatafi yabar su Amra agun har yanzu suna gurin sun kasa motsawa sunyi carko carko agun kamar nonuwan maza ko mamaki yagama cikasa da yakasa yiwa ɗan uwansa magana,

Hamra ce tafara dawowa daidai da mamakin yagama sakin ta sannan tace to me muke jira sai kuzo mu kwashi ƴan matan ƙafar mu muƙara gaba daman ni basan zuwa nake ba dan wannan daman kana ganin sa kasan baza ayi abun arziƙi dashi ba,

saida ta taɓasu sannan Amra da ba haka taso ba ta taɓe baki kamar zatayi kuka tace "to wai mema yake nufi da hakan kodan ita kaɗaice ƴar uwarsa shine zai tafi da ita yabar mu dan ƴan ubanci,

da sauri Azeema ta dafata tace "haba Amra ba haka bane ba abun da kike tunani bane bazai taɓa yin hakan ba wai dan ƴar uwar sace kinga shi ba me son mutane bane wataƙil abun da yasa yatafi da ita dan ta ɗebo nata kayan itama da ta bari saboda bazai ɗebo mata ba shiyasa ya sauke mu ya tafi da ita amma kar kisaka wani abu aranki muje kawai mujira su yanzu zasu dawo ta faɗa tana riƙo hannun ta ta fara janta,

Hamra tace "ai ni abun da nake tunani ma daban ina tunanin da ƙyar ne ma idan ba wani abun zaiyi mata ba bakuga kallon da yayi mata ba loƙacin da tace ya taho mata da nata kuma daman idan baku manta ba ai tace tsoran sa take ji tayi masa laifi bataso su haɗa, wataƙil wata muguntar tasa zaiyi mata  tunda tace mugune,

Azeema tace "aikuwa dai hakanne ma maganar ki naga daman ta tsorata tanaso ta fito ya ƙulle ta aciki aikam yau ta shiga uku ita da banda abun ta ina ita ina tsokanar wannan mugun, baka yi masa bama ya ka ƙareda shi bare kuma kashiga gonar sa Allah dai ya kareta kar ya cutar da ita,

"Ameen Hamra ta amsa mata dashi cike da jimamin tausawa halin da Ameesha zata shiga, haka sukai ta surutun su har suka ƙarasa part ɗin,

kuma duk surutun da sukeyi Amra bata saka musu baki ba dan ita bata yarda da maganganun suba aganin ta kawai yayi hakane da ya ware su ya ɗauke ta dan tsabar rashin mutun cima saida yabari suka shiga cikin motar suka zauna zai wani buɗe yace su fito da tun can me yahanasa cewa kar subiyo sa saida ga baya zai wulaƙantasu ji take kamar tasaki kuka dan taƙaicin da yake cinta,

da sallama suka shiga falon maama ce kaɗai aciki ta amsa musu Sallamar su tana dubansu da mamakin dawowar tasu, Saida tabari suka gama shigowa ciki suka zauna, ta ƙara kallon su da kyau tace "ƴan matana yana ganku haka kundawo lafiya dai ko koroko yayi?

Azeema tace "eh" tafiya yayi yabarmu,

maama tace "daman nasan zai aikata tunda daman bada son ransa yace kutaho ba amma saida yajaku waje kuma zaice ku dawo dan baida m to Allah ya shirye sa, ina ita Ameeshan take banganta ba,

Amra tayi caraf tace "da ita kaɗai yazaɓa yatafi saboda itace ƴar...... Hamra tayi saurin rufe mata baki tace "maama bayan munfita har munshiga motar fa sai ya buɗe yace mu fito daman Ameesha ce tafara shiga ciki da tazo zata fito kuma sai ya rufe kafin ta fito ya shiga ya ƙulle motar suka tafi shine muka dawo mukuma,

"kai kai kai la'ila ha illallahu Muhammadan ɗan Abdallah yanzu shi duk wannan abun bai haƙura ba saida yayi yanda zaiyi ya tafi da ita dan yaje yaci zalinta duk haƙurin dana basa bai haƙura ba sai ya rama sai kace wanda Allah yabawa zuciyar kuturu da bazai ringa yafita ba,  ashe da biyu yace kutaho daman ya shirya hakan dan ya kamatane yace kutafi sannan ya koroku aikwa ya taɓa min ƴar nan yau sai na ɓata masa rai zai dawo ya same ni, tayi maganar tana riƙe baki,

Amra ce tace "wai maama me tayi masa zaiyi mata haka, tayi tambayar ne dan tadaina tunanin abun da take tunani so kawai take taji zunubin da ta aikata masa sannan hankalin ta zai kwanta,

maama ta ɗanyi murmushi tunawa da abun da ya haɗasu sannan tace "cizon shi tayi,

akusan tare suka haɗa baki wajen cewa "cizoo...!?"

maama tayi dariya ganin yanda duk suka zaro ido suna mamakin maganar,

Amra harda matsowa kusa da ita tace maama cizofa  garin ya akai takai haƙoranta jikin sa ta cijesa,

maama ta kalleta itama sannan "tace muna hanya ne ya ɗora mata ƙafa ita kuma da taji zafi tace ya ɗaga ta yaƙi sai kawai ta cizjeshi a ƙafar shine yake ta so takamata ya rama shiyasa yayi mata wayo yau ya tafi da ita saidai Allah ya kiyaye kawai nasan sai yaci zalin ta wallahi bari insa uwarsa takira sa ta haɗani dashi inyi masa magana,
Chapter 128 · 0% Book details