Sashe 68
Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Atare suka jera gwanin ban sha'awa suna tafiya abun su har suka karasa part din Ammah suka fara zuwa tundaga qofar shiga wata jakadiya ta sanar dasu cewa basa nan,
part din fulani suka nufa saida kashe nan ma suna shiga basuga kowa a falon ba dan haka sai hamra da Ameesha suka zauna afalon ita kuma Amra ta qarasa can cikin dakin fulani bayan tayi sallama an amsa mata ta shiga sai ta samu fulani ita kadai nan suka gaisa sama sama saboda har yanzu bata dawo daidai ba daga abun da gwaggo tayi dazu,
mama fulani dan Allah gwaggo fa bata shigo nan ba?
data shigo ai da kinganta da kika shigo ko,
oh ai nazata ko ta shigo ta fitane shiyasa na tambaya,
" to bata zoba,
Ok to sai anjima....
tana fadar haka ta juya ta fice daga dakin,
tana fita tace bata nan muje kawai idan mundawo sai muje har inda take mu same ta..
dukansu mikewa sukayi suka qara fita daga part din,
tundaga waje suka hango Ammar har ya fito cikin shirin shi tsaf yayi kyau kuwa abun sa daman kuma me kyau din ne sai kuma ya qara da wanka sai abun yayi gwanin sha'awa yayi kyau sosai,
da sauri suka qarasa inda yake suna yabon kyaun da yayi shikam sai faman sakin murmushi yake daman yana sane yayi wankan dan ya burge Ameesha sai kuma gashi ya burgeta din duk da batace komai ba amma yasan aranta ta yaba da kyaun nasa,
da kansa ya bude mata gaban mota yace ta shiga qin shiga tayi ta juya ta kalli su Amra suna hada ido suka dage mata gira daya tare da bude bayan motar suka shige sunyi mata dariya qasa qasa,
bayanda ta iya haka ta ta shiga batare da ta kalle saba,
tana shiga ya rufe shima ya zagaya ya shiga ba bata loqaci yatayar da motar yajata suka fita daga masarautar ransa fal da murna,
saida suka dau hanya sannan yajuyo yana kallon ta tare da yi mata magana yace awace unguwar kuke shiru tayi taba tunanin amsar da zata basa jin bata basa amsa ba yasa yaqara cewa wacce makarantar kike nan tabashi amsa da haka de yadin ga jefo mata tambayoyi wasu ta amsa wasu kuma tayi masa shiru so yake tasaki jiki dashi amma hakan ya gagara amma yabawa kansa daga nan zuwa gobe sai ta saba dashi,
wajen wani shaqatawa yakaisu yasa kowa ya zabi abun da yake so akawo masa saida yajira ta zabi nata sannan shima yace akawo masa irin sa,
bayan ankawo musu sunci sun sha kowa yaci itana kuma bata tsaya fulako ba tasaki jiki taci abun ta son ranta,
daga nan kuma yaqara dibansu sukaje wajen wasanni zuwa loqacin kuwa har yayi nasara dan tafara warewa dashi su Amra sai tsokanar ta suke, bata biye musu saidai tayi murmushi kawai wani kuma tace musu su dena bata so ahaka suka wuni suna zagaya gari sai dab da magariba suka nufi wani dan qareran shopping mall nan suka tsaya bayan sun fito daga mota suka shiga ajere shida ita agaba su Amra abaya suna gulmar su har suka shiga ciki nan fa kowa yafara diban abun da yake so kuma harda ita batayi fulako ba anan ba ta zage duk abun da taga sun dauka itama idan ya burgeta sai ta dauka hakade sukaita daukan abubuwa kala kala sannan suka hakura suka barshi haka bayan kowa yagama kwasar abun da yakeso,
wajen biyan kudi sukaje aka lissafa Ammar ya biya aka saka musu kayansu aleda kowa da ledar sa,
Ammar ne yafara kwasan ledojin masu nauyi yayi gaba dasu sukuma yace su dauko sauran amma banda Ameesha ita ba ta dauki komai ba,
Su hamar ne kawai suka kwaso sauran kayan sannan sukayi gaba ita kuma tana binsu abaya,
wajen motar suka qaraso inda Ammar yake ajiye kayan abayan mota suma nan suka nufa suka ajiye nasu sannan ya rufe yace su shiga shiga sukayi shi kuma ya zagayo dayan barin dan budewa Ameesha sai yaga bata wajen ciki ya leqa amma nanma baiganta ba sai ya leqa gurin su hamra dasuke ta faman surutu akan kayan da suka dauko sai yaga su biyune kawai aciki,
ina take ne nagan ku kukadai ina kuka barta kallon sa sukayi gaba dayan su tare da cewa aa tare fa muka fito,
to ko komawa tayi cewa Ammar,
bude motar sukayi suma suka fito sukace to watakil bari muje muduba ko ta manta wani abunne nan suka sake komawa ciki gaba dayan su,
suna shiga tundaga farkon qofar suka tambaya ko wata yarinya ta dawo sukace gaskiya bayan fitar sude ba yarinyar da ta dawo amma de su shiga su duba kobasu lura da shingan ta ba, shiga sukayi suka fara duba lungu da saqo suna nemanta amma ba ita ba dalilinta wajen suka qara dawowa suka dudduba amma basu ganta tofa abu kamar wasa yana shirin zama gaske hankalin sune yafara tashi ciki suka qara komawa akaci gaba da naimanta tun suna abu su kadai har ya koma ga kowa ma yaji nan aka shiga nemanta har manajen wajen ma saida yaji hankalin kowa yatashi wajen nemanta........
Nimade hankalina yatara tashi shin Ameesha ina kika shiga kika boye????
💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(ster lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)
*6,BABY
by(mhiz innocent)
[6/24, 7:10 AM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤
💅SARKI SAMEER...💅
(wasa farin girki)
💖*the talent troupe writer's*💖
*Book 2*
*sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200 bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*
🅿️65&66
✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨
✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨
Bismilah............✍️
tofa wata sabuwa inji dan caca ana wata ga wata anduba ko ina na wajen babu Ameesha babu me kamar ta sama ko qasa babu Ameesha,
Allah sarki twins har sunfara kuka hankalin su gaba daya baya jikin su dan sun fara fita hayya cinsu sai faman kwala mata kira suke kamar sunganota awani wajen duk sunbi sun furgita shima Ammar dauriya kawai yake yana basu baki dan shi yama fisu shiga tashin hankali saboda shi yadauko su yanzu idan ya koma me zaice taya zai fara tunkarar gida da wannan zacen ace yarinya sukutun guda anne meta anrasa gashi kuma bakuwa ce danshi da ace acikin twins ne bazai tada hankalin sa kamar yanda yaje ji akanta ba babban yayan sune ya fado masa arai take yaji wata sabuwar zufa na wanke masa jiki duk addu'ar da tazo bakinsa karanta yake kansa ya qulle gaba daya yama rasa wane irin tunanin zaiyi abun abun mamaki ace yanzunan su fito tare kuma ace anne meta anrasa to kode sace ta akayi, kai a'a wata zuciyar ta basa amsa to idan ba sace ta akayi ba ina tashiga ai duk inda taje da suganta to inama zataje ita datake baquwa ba inda tasani,
kawai hannu ya dora akai yanaso hawaye suzubo masa ko ya samu rangwamen abun da yakeji game da wannan al'amarain da yayi mugun daure masa kai,
cikin kuka Hamra tace yaya mu koma gida ko zamu ganta acan,
dagowa yayi ya kalleta jin shirmen da takeyi yama kasa tanka mata sai faman binta da ido da yake azahiri ita yake kallo amma a badini bahaka bane hankalin sa ba akanta yake ba,
Amra ce itama cikin hawaye shabe shabe da ya wanke mata fuska tace yaya mutafi gida muje mudubo ta ni nasan tana gida watakil tsokanar mu take ta tafi ita kadai kataso mutafi,
duk surutun da takeyi itama ba sauraron ta yake ba,
tashi yayi daga bakin mall din da yake zaune yaqara komawa ciki dan ji yake kamar zai ganta amma yanda ya shiga haka yaqara fitowa shikadai wajen suka qara dubawa har tafiya suka danyi aqasa me tsayi suna nemanta wai ko zasu ganta tabi wata hanayar amma shiru basu ganta ba,
ba yanda suka iya haka suka koma mota suka shiga sannan yaja motar da kyar suka dauki hanyar gida zuciyar sa na ta bugu saboda baisan me zai faru ba idan akaji wannan batun agida,
ahaka yaringa tuqin hankalin sa rabi akan tuqi rabi a tunani da haka har suka qaraso gida bayan an bude masa gate ya shiga yanufi parking lot yayi parking amma da yayi parking din sai yakasa fitowa daga cikin motar yana fargaba suma su Amra ganin baifito ba sai suma suka kasa fitowa sai sukaji wani tsoro ya qara dirar musu loqaci guda,
juyowa yayi yakalle su ganin sunyi tsuru tsuru sun hade guri daya sunkasa motsawa sai suka bashi tausayi da saboda su kawai yadan yi qarfin hali ya bude qofar sannan ya bude musu sunma yace sufito kamar jira kwa suke haka suka fito da sauri suna fitowa basu tsaya bi takansa ba suka kwasa aguje suka nufi part dinsu,
da sauri shima yabi bayansu yana kiran sunan su amma ina har sunyi nisa basu saurare saba, saurin yaqara shima yabi bayan su cikin sarssarfa gudu gudu sauri sauri saboda so yake shiyafara fada kafin su sufada saboda bazasu fada cikin sigar kwantar da hankali ba shiyasa bayaso suriga sa zuwa,
aikin gama yagama domin kwa yana saka qafarsa a falon, "Amra nacewa momma ansace Ameesha,
tsayawa yayi cak tare dacewa damm it yana furzar da iskar bakin sa me zafin gaske,
momma da fitowar ta kenan daga kitchen taji maganar wani iri ban barakwai ta dake ta, tunanin ta ko bataji abun da Amran tace bane dan haka tayi saurin matsawa kusa da ita tana riqeta tace ke menaji kince kode kunena ne yaji min ba daidai ba,
"momma bamuga Ameesha ba mun nemata munrasa, hamara tafada cikin sanyjn murya tana goge hawayen fuskarta,
mutuwar tsaye momma tayi tamakasa kwakkwaran motsi da kyar bakinta na rawa tace bangane abun da kuke nufi ba kuyi min bayani yanda zan gane j na kuka baro yar mutane kuma har kuka iya dawowa cikin gidan nan batare da ita ba,
ina take !!!?