← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 139

Sashe 118

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"nakai mata kawai yace da ita sannan ya ɗauki tea 🍵 ɗin da ummy ta haɗa masa yafara sha,

kallon kallo ummy da maama sukayiwa juna ba wanda yace komai sai kawai ummy ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin tana zuwa taga ƙofar abuɗe shiga tayi taga ɗakin wayam ba kowa aciki kiran ta tashi ga yi, tana ƙarasa shiga cikin tsakiyar ɗakin,

daga cikin bathroom ɗn Ameesha ta amsa tare da buɗe ƙofar ta leƙo saida taga ita kaɗai ce sannan ta fito daga ciki tace ummy shine kika aiko sa badan nayi hanzarin ganin saba da tuni yayi min dukan mutuwa,

ummy tace "wallahi banma san yazo haka nace kawai yakawo min in kawo miki shine ya taho dan bansan ma loƙacin da yashigo ba har yashigo nan baidai yi miki komai ba ko,

"eh ummy Allah ya taimakeni bai kamani ba ai,

to yanzu yi sauri kisaka muje sai ɓata mana loƙaci kike tun ɗazu ke muke jira,

da ƙyar dai ta yarda ta shirya sannan suka fito tare, tana ta ɓuya abayan ummy har suka ƙaraso gurin can kusa da abu ta zauna tunda tasan idan tana kusa dashi ba lalle yayi mata wani abun ba,

saida ta zauna sannan duk ta gaida su amma bata gaida meer ba kuma babu wanda yayi mata magana dan basu lura bama amma shi yana sane da ƙin gaidashi ɗin da tayi,

ba ɓata loƙaci suka shiga cin abinci batare da kowa ya ƙara magana ba,

suna cikin ci wayar ummy tayi kara dubawa tayi sai taga number Ammi ce da ta karɓa jiya take kiran ra da sauri ta ɗaga tare da saka wayar a speaker tace hello daga can ma Ammi tace hello ina kwana  dafatan kun tashi lafiya,

ummy ta amsa mata da lafiya lau,

sannan Ammi tace daman yanzu yaron gidan masarautar nan ya kira  yace baida Number ku yace ku hanzarta kushir ya nan da ƙarfe goma za ayi wani taro acan kuma yanaso ayi agabanku saboda ansamu wata gagarumar matsala acan kuma yanaso ayi komai agaban ku dan haka yace kuyi gaggawar halattar taron,

ummy ta ɗago ta kalli maama sannan tace to shikenan gamunan sai kuma kushirya muna zuwa sai mu wuce yanzu zamu fito,

Ammi tace "to shikenan sai kun ƙaraso,  daga nan sukayi sallama,

maama tace tofa me kuma yafaru haka da sassafe za ayi taro, ummy tace nimadai nayi mamakin hakan amma dai muyi sauri muje sai muji abun dake faruwa,

nandai sukayi shiru sukayi sauri suka ƙarasa cin abincin daman kowa yayi wanka dan haka basu wani ɓata loƙaci ba suka gama shiryawa suka fita daga gidan,

Meer da Abu agaba sai su maama abaya,

yanzudai bayi wannan mahaukacin gudun ba yana tafiya ahankali har suka iso gidan su bossay,

loƙacin da suka shiga suma duk sungama shiryawa su kaɗai suke jira,
Hajiyar shettima ma da shi kansa shettiman duk suna cikin gidan  sun daɗe da zuwa saboda su  zasuyi musu jagoran ci zuwa cikin gidan batare sa an tsayar dasu tamabayar su waye ba ko daga ina suke,

saboda kiran da sam yake tayi musu yasa basu wani tsaya gaisuwa mai yawa ba suka ƙara fitowa gaba ɗayan su harda dadyn bossay sai Ammi da bossay shettiman da hajiyar sa sai kuma dadda gaba ɗayan sudai haka sukayi mota mota wajen motoci haɗu sukayi suka nufi masarautar.........,

*******************************

________*masarauta*_________

   :A daren jiya dai babu wanda yayi bacci me daɗi kowa ya kwana zuciyar sa  babu daɗi wasuma basu samun damar  rintsawa ba yanda suka ga rana haka suka ga dare kowa na tunanin me zai faru ba iya waɗan da abun ya shafa ba har sauran ma'aikatan gidan da akayi komai agaban idon su tun adaren kuwa labari ya karaɗe lungu da saƙon cikin masarautar babu wanda baiji ba dan magana ma harta fara fita waje kan cewar sarkin gari ba ɗan masarauta bane baida alaƙama da masarauta haka dai sukai ta yamaɗiɗi tare da ƙara gishiri da magi akan maganar dan tafi armashi saboda ba iya abun da yafarau ake faɗa ba sai anyi ƙari,

aranar yau kuma papa shima yadawo cikin hayyacin sa kuma shima Ammah tagaya masa abun dake faruwa ba ƙaramin ɓaci ransa yayi ba dan haka dan da nan yasa akafara sanar da duk wani wanda yake da alaƙa da masarauta akan ahallara ƙarfe goma daidai acikin fadar da kuma ƴan cikin fadar manya manya amma banda yara ƴan ƙananu iya iyaye da samarin gidan waɗanda suka mallaki hankalin kansu irin su sam kenan.....,

tun wajen ƙarfe tara akafara hallara acikin fada ɗaiɗai kune basu zoba kawai,

    *_10:am_*

kowa ya hallara daga ciki sarki Salahudden ne karshen shigowa shi da Azeema suka shigo normal kayane ajikin sa dan ko hula baisakaba haka yataho kamar bashi ba tunda ya shigo papa dake zaune kan kujera ya ke binsa da kallo tunda ga sama har ƙasa ya kafe sa da ido bashi kaɗai ba sauran mutanen gurin ma duk kallon sa akeyi can ƙasa daga gefe babu kowa agun nan ya nufa ya zai zauna aƙasa papa yayi saurin dakatar dashi tare da cewa me yasa zaka zauna aƙasa kuma ina kayanka ka saka waɗannan kayan kuma ko hula baka saka  ba akan wane dalili?

sunkuyar da kansa yayi tare da cewa aimin afuwa amma bazan iya kara saka kayan ba saboda badani yadace ba kujera ma kuma nagama zamanta koda ace hakan ba gaskiya bane bare ma kuma na tabbatar da bani da alaƙa da ita tuba nake mai martaba amma bazan iya bin umarnin ka ba akan sai nahau kujera koma nasaka wani abu da ya shafi sarauta yana gama faɗar haka ya zauna a inda yayi niya tun farko Azeema agefen sa ya zauna tare da hade gwiwowin sa ya kifa kansa akai bai ƙara kallon kowa ba har mahaifin sa dake gurin,

fulani kam yau itama ba kan kujera tana ƙasa kamar yanda kowa yake mutum biyu ne kawai akan kujera daga papa sai Ammah amma kowa na ƙasa, kujerar sarki kuma tana gurin itakaɗai ba kowa akanta,

wayar Azeema ce tayi ringing da sauri tasaka ta a silent tare da miƙewa tsaye ɗan ɗaga murya tayi tace agafar ceni zanje in shigo da mamana sun ƙaraso,

Ammah ce tace "to ki hanzarta ana ta ƙara ɓata loƙaci kowa ya hallara daman su muke jira,

da sauri ta fita daga cikin fadar,

papa ne yace "wai banga gwaggo ba ko ba asanar da itaba ne najita shiru har yanzu ko sai an ƙara kiranta,
Ammah tace " inagadai ko wani abunne ya riƙeta Ammar je ka kaƙara kiran ta,

da sauri ya miƙe tare da cewa to sannan ya fita,

yanama fita suka haɗu da ita tana daf da shigowa dan haka sai suka dawo atare suka shiga suna shiga ko sallama gwaggo batayi ba tace "nashiga uku ni ƴar nan me nake gani haka daman abun da ake faɗa min gaskiya ne suwa nake gani aƙasa sarki naga kanka haka ko hula kuma aƙasa azaune lalacewae har takai haka  ina munafukar take hatsabibiyar almura  amma dai kedai bakida imani tunda nake bantaɓa jin irin wannan ɗanyaen aikin ba ke naki watakon yafi na kowa nidaman tun farko banyarda dake ba saboda daman zubinki zubin munafukai duk wanda yaga ƙwayar idonki yasan ƙungurumar munafukace da kanta kamar ƙullin maganin bokaye,

har gabanta taje tare da ɗago kanta da hannu ta fara duddun gure nata kai tana cewa "Allah ya toni asirin ki yau wai mema akejira ba ayiwa yara tsira taba  tunda ga hujja an samu kuma me yarage ai naso inzo inga an sauya mata kamanni amma sai inzo inganta ras da ita babu wani tabo to ni wallahi bari infara yi mata dan idan naganta haka zaune lafiya ƙalau raina bazai min daɗi ba amma idan naga ana magana tana cikin wani halin sai nafi jin daɗi tana gama faɗar haka ta ɗaga wani ɗan katako da tazo dashi daman saboda dukan ta ta taho dashi ƙwala mata tayi akai zata ƙara sauke mata wani papa yayi saurin riƙeta yace haba gwaggo kiɗan dakata mana afara yin magana dan Allah ki rabu da ita ki samu waje ki zauna yanzu ba wannan loƙacin bane,

kasan Allah bazan rabuda ita hakannan ba sai na tsiyayer mata da ido,

daƙyar papa yajata amma duk da haka saida ta ƙara ziro katakon ta gefen sa ta bugawa fulani akafaɗa sannan tabar wajen,

Allah sarki fulani tana zaune ta sunkuyar da kai takasa ɗaga ido ta kalle kowa ranta duk yabi ya dagule ji take kamar ƙasa ta tsage ta nutse ciki saboda jin kunya da taƙaicin abun da ake mata gashi kuma batasan ma me zai faru ba wane irin hukunci za a yanke mata ba,

zama gwaggo tayi amma duk da haka bakinta yaƙi yin shiru da ƙyar aka samu tayi shiru sai kuma ta koma hararar ta tana girgiza kai sai karkarwa take jikin ta tsima yake kawai so take taga jikin fulani jaga jaga da jini an kunkunbura mata wani gurin sannan hankalin ta zai kwanta amma yanzu gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta,

suna cikin haka saiga su Azeema sun shigo ita da mana da saleem, bakin su ɗauke da sallama suka shiga,

amsa musu akayi  tunda suka shigo kallo yadawo kansu kowa su yake kallo yamaida hankalin sa gare su musamman ma ma mama da kana ganin ta kaga sarki Salahudden kuma suna kama da saleem ma sosai,

dan haka tun kan ace komai ma kowa ya tabbatar da cewa lalle waɗannan jinin sane sune ƴan uwansa ba ƴan cikin masarauta ba,

itadai mama batasan komai ba game da maganar saboda ba asanar da itaba kawai Azeema haka tace mata suzo ana nemansu masarautar saboda angano ta kuma gata ga baba komai lafiya babu wani abu da yasame ta dan ta kwantar musu da hankali har suzo shiyasa tayi musu haka,

amma ganin kowa yana ta kallon su sai yasa duk suka tsargu dan haka ababakin ƙofar suka samu waje zasu zauna,
Chapter 118 · 0% Book details