Sashe 133
Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahaka yaci gaba da zama loƙaci zuwa loƙaci yakan harare ta duk da baya kallon fuskar ta amma hakan bai hanasa ai ka mata da harara ba gashi ya manta sunan ta bare ma ya kirata ko zata tashi, kuma ya rasa da me zai kirata shiyasa kawai ya fasa yi mata magana,
Yana zaune agun yajiyo kiraye kirayen sallah a Masallatai zaro manyan idanun sa yayi waje saboda tsabar mamakin da yayi kenan ahaka ya kwana ya akai haka ta faru yarinyar nan ta barsa ya kwana anan aƙasa, wani tunanin ne yayi saurin faɗo masa rai ya akai yaji sauƙi haka har ya iya tashi da kanshi kuma yagan sa ba a cikin asibiti ba alhalin duk ranar da ruwa ya taɓa sa baya dawowa cikin hayya cin sa da wuri sai yafi sati a kwance, Duk da bai fi sau biyar hakan ta taɓa faruwa dashi ba shima kuma tun yana yaro ne da girman sa kuma sau ɗata yataɓa ritsawa dashi ranar kuma yafi sati biyu bai samu lafiya ba to amma yanzu ace a rana guda ya dawo cikin hayyacin sa harma yana tunawa da abun da ya faru haka cikin sauƙi ba wata matsala, to ya akai hakan ta kasance waye kuma ya shigo dashi cikin gidan bayan a waje abun ya faru, yasan dai ba ta yanda za ayi wannan yarinyar ta iya jawo sa, a fili yace "hakan bazai taɓa yiyu wa ba zata min bayani, yana gama faɗar haka ya maida duban sa gare ta da ɗan ƙarfi ya ɗan ɗaga murya yace "keee....., shiru ba bata motsaba saboda yanayin da yake ciki yasa duk da ya ɗaga muryar amma ba ta fitowa sosai saida yayi mata wajen sau uku sannan ta ɗan motsa kanta ta gyara kwanciyar ta aƙasan capet ɗin ta ɗaga masa hannu, kamar tasan abun da yake so kenan ta ɗaga masa, Saidai kuma tana ɗagawar yaji hannun ma yafi da zafi ya sanƙame saboda daɗewar da tayi akai har yayi tsami sosai,
Oh my God! Ya faɗa cike da gaji yawa da halin da yake ciki ya rasa yanda zaiyi da ƙyar ya iya motsa ƙafar sa, amma hannun dai har yanzu yakasa motsa sa, gashi har antayar da sallah amma yana kwance wannan shi kaɗai ne abun da yafi ci masa rai kenan, ba ƙaramin abu ne ba yake hana sa zuwa sallahr asuba amma yau gashi abun da yaɗauka ba komai ba ya zame masa komai tunawa da ya yi cewar halin da ya shiga jiya ma ai da tuni yanzu haka baisan ma duniyar da yake ba kamata yayi ma ya godewa Allah da yakawo masa sauƙi da wuri....,
Haushi ne ya ishe shi ganin har yanzu tana kwance hankalin ta kwance yasa ya ƙara kiran ta da ƙarfi! juyi tayi fuskar ta ta dawo saitin sa suna facing ɗin juna saida ta fara yin miƙa saboda itama da ciwon jikin ta tashi saida ta gama miƙarta sannan ta shiga buɗe idanun ta a hankali har ta idasa buɗesu gaba ɗaya. Tana gama buɗewa suka sauka akan fuskar Meer maimakon ta janye idon ta, ta tashi sai kawai ta tsaya tana kallon shima itan yake kallo har saida yaga kallon nata yayi yawa sannan ya wurga mata harara tare da jan tsaki a hankali ya furta "mayya saidai kici kanki.
Hakan da yayi mata yasa ta saurin janye idon ta akan sa sannan ta yunƙura da ƙyar ta tashi zaune tana hamma tare da yin wata miƙar azaune tana duban garin yanda ya ɗan fara yin haske hakan kuma ya tabbatar mata da safiya har tayi daɗi sosai taji saboda tunawa dole ya tashi su tafi da zarar tayi sallah, tunani ta shiga yi to shi ne yake agun akwance har yanzu da alamar ma ko sallah baiyi ba ko uban me yake jira da bai tashi ba oho masa,
wani tsakin taji ya ƙara saki yana kawar da kansa gefe, da mamaki ta kalle sa a ranta tace masifaffe kayi ka gama kaci kanka ba kulaka zanyi ba, a fili kuma sai ta taɓi baki haɗi da miƙewa tsaye sanin bata da inda zata tayi alwala a ɗakunan yasa ta nufi kitchen direct taje can ta ɗibi ruwa sai ta fita ta ƙofar baya acan tayi fitsarin tayo alwalar ta dawo falon, Har yanzu yana inda ta barsa ko motsawa baiyi ba bata bi ta kansa ba ta fara tunanin da hijabin da zatayi sallahr,
Tsaye tayi taba ɗan dube dube ko zata samu amma bata ga komai ba sai mayafin da tazo dashi shi taje ta ɗauka akan kujera daman doguwar rigace a jikin ta kuma bata kamata sosai ba ga dogon hannu sai kawai ta yafa shi a kanta sannan ta hau kan Capet ɗin ta tayar da sallahr. Duk abun da take yana kallon ta yana jin taƙaici a ransa har ta idar tayi addu'ar ta ta ɗora da Azkar ɗin safiya ta ƙara yin wata addu'ar ta shafa, sai ta juya ta kalle sa tana juyawa suka haɗa ido maimakon yajanye saboda kamansan da tayi yana kallon ta sai kawai maze tare da harar irin ita yagani tana kallon sa,
Ɗan jinjina kai tayi kawai sannan tace tace "ina kwana, da sauri ya juyo yana kallon ta dan yayi mamakin wannan gaisuwar tata bai taɓa tunanin zata iya gaida shi ba,
Itama anata ɓangaren batayi tunanin zai amsa ba sai taji yace "lfy daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba"
So yake yace ta taimake sa amma ya kasa saboda yana gudun kar ta raina sa, da yayi mata maganar ta gwamma ce yaci gaba da zama a haka zuwa ɗan anjima ko zaiji sauƙin jikin sai ya tashi da kansa,
Abunne yafara bawa Ameesha mamaki ganin dai har yanzu bai motsa ba sai ta ɗan tsorata da hakan ta fara tunanin kodai yakasa tashi ne tuna hakan yasa ta ƙara maida duban ta gare sa, sai tace "Kayi sallah kuwa?
Ɗan juyowa yayi ya kalle ta baiyi magana ba har ta cire ran zai bata amsa ma sau taga ya girgiza mata kai alamar a'a,
Ta ɗanyi mamaki kaɗan amma sai ta danne tare da miƙewa tsaye ta matsa kusa dashi daf dashi ta tsugunna sannan tace "me yasa, ko ka kasa tashi ne?
Yanzu ma kan ya kuma ɗaga mata kamar wani ƙaramin yaro, Sai taji ya bata tausayi abun da zai hanasa tashi kuwa ai ba ƙarami bane adain iya sanin da tayi masa namiji ne mai dauriya amma tunda ya faɗi haka kuma har takai ga ya kasa tashi to ba ƙaramin abu bane yake damun sa dole ka tausaya masa,
Miƙewa ta tsaye ta kuma yi sai ta miƙa masa hannun ta,
Hannun ya shiga bi da kallo har zuwa kan fuskar ta yana tunanin me take shirin yi taya zata iya ɗaga sa tama mayar dashi ƙaramin yaro janye idon sa yayi batare da yace mata komai ba kuma bai miƙa hannun na saba,
Hannun tane ya fara ƙagewa da miƙa masan da take dan haka sai ta janye ta ƙara tsugunna wa a gaban sa tace katashi in taimaka ma kayi sallah,
A hankali taji yana magana dan bata ma jin abun da yake cewa kunnen ta taƙara matsar wa kusa dashi tace me kace?
"Baza ki iya ba nace"
"Wallahi zan iya ta basa amsa"
Shiru yayi baice da ita komai ba saida ya ɗauki loƙaci sannan yace "Bismillah ya faɗa tare da miƙa mata hannun riƙewa tayi tare da miƙewa tsaye ta shiga jansa amma ko motsi bayayi, in banda wata wahalar ma da take son ƙara masa babu abun da take da ta gaji sai ta saki hannun tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu, da yana dariya da babu abun da zai hanasa yi mata dariya yauɗin nan yanda take ta wani sauke numfashi ɗagasa kawai ɗaga warma da batayi ba amma wai ta gaji,
Kamar wacce aka tsikara tayi sauri ta miƙi tare da nufar kitchen binta yayi da kallo yana mamakin ƙarfin hali irin nata yarinya ƴar ƙarama da ita sai tsaurin idon masifa ita yanzu kallon mutum take wa kanta,
ta daɗe a kitchen ɗin baisan me take ba sai yaga ta fito ɗauke da roba a hannun ta yana kallon ta har ta ƙaraso inda yake ta ajiye robar da ke ta faman tiriri na ruwan zafin dake ciki, tana ajiyewa ta ƙara komawa sai ta fito da wani sabon towel da abayi amfani da shi ba, a gaban sa ta ƙara zama,
Duk yana kallon ta baice mata komai ba dan yagane me take shirin yi kuma ya jinjinawa kaifin tunanin ta dan yana da buƙatar hakan,
kamo hannun sa tayi ta ɗora akan cinyar ta sannan ta saka tsumman acikin ruwan zafin ta matse sai ta ɗaga hannun nasa tasaka shi akan tsinman ta fara ɗan mammatsa masa har zuwa wajen kafaɗar sa saida ta tabbatar da hannun ya gasu sannan ta koma ɗayan ma nan ma tayi masa ruwan yafara salan cewa dan haka ta ta shi taje ta ɗebo wani ta dawo taƙara yiwa ƙafafun su takan wandon jikin nasa take masa har wajen cinyo yin sa gaba ɗaya dai saida ta saka masa ruwan zafi a ko ina ta gasa masa har wajen wuyan sa sai da ta ɗan daddanna masa, sannan tasaka hannu ta ta ƙara ɗan daddanna masa wasu guraren, saidai kayan jikin sa duk sun jiƙi,
Ba ƙaramin daɗin jikin nasa ba kwa yaji dan a cikin kaso ɗari kaso saba'in ya ragu dan har ya motsa hannun da ta gajiyar masa dashi,
Hannun ta ya kamo da ɗayan hannun sa ɗayan kuma ya dafa kujerar da take gefen sa ya yun ƙura zai tashi amma sai yaji ya kasa, miƙewa tsaye tayi tasa iya ƙarfin ta da Allah yabata ga kuma shima yana ɗan ƙoƙarin tashin bai sakar mata duka nauyin saba a haka yasamu da ƙyar ya miƙe zaune,
Sannu tayi masa, ya ɗaga mata kai yana ƙara gyara zaman sa da kyau sai ya jin gina kansa da jikin kujerar,