← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 139

Sashe 135

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu ya sa ya dafe gefen fuskar sa yana kallon ta shi har yanzu abun mamaki yake basa, ƙara nana ta mata tambayar da yayi mata a farko ya yi amma still bata basa amsa ba saida ta ɗauki loƙaci tana shashsheƙar kuka sannan cikin kuna tace "yunwa nake ji kuma nasha wahala nayi mana kazo ka cinye gaba ɗaya, tana gama faɗar haka ta ƙara sakin wani kukan saboda baƙin cikin da ga kuma taso mata taso taci tunda tayi take haɗiyar yawu daman arayuwar tana son dankalin turawa da ƙwai idan akayi agidan su Rasheeda har guziri take ta tafi dashi gida saboda son da take masa shiyasa ma da ta rasa abun yi ta yi musu shi  ko ɗanɗa nawa bata yiba saboda batason tajiyo daɗin sa tun kan tazo ci   saboda tasan bacci zaiyi da yawa idan yagama sai ta cinye gaba ɗaya to kuma gashi yanzu ya ɓata mata bojet  tana ji tana gani  a gaban ta ya cinye bai bar mata ko ɗaya ba,

Tunda tayi maganar yakasa motsawa daga gun  ido kwa bai yarda sun haɗa ido ba saboda wata irin kunya ce ta kamasa wai abincin mutum biyu ya cinye shi kaɗai tabb akwai matsala yanzu bai san ma yanda zai yi da ita ba, 

Sai yaji ta basa tausayi kuma ta basa dariya da tasan bata ciba ta kawo masa kuma harda jin haushi dan baici ba yanzu kuma yaci tazo tana masa tijara,

kukan natane ya ishe shi sai ya kalle ta yace "me yasa baki gaya min ba, da kin gaya min ni ko ci ma ba zan yi ba, daman ni ai banyi niyar ci ba kece kika takura min naci abun ma da ko daɗi babu kinzo kinsa zuciya ta sai tashi take ni banyi kukan ba sai ke to wallahi ki min shiru tun kan ranki ya ɓaci a gunnan ni nace kibani, sai kiyi haƙuri kisha tea kawai ko kuma kije kiƙara yin wani bada akwai ba, yayi maganar yana haɗe rai waishi a dole kar ta kawo masa wani raini a ciki idan ba haka ya yi mata yasan baza su zauna lafiya ba dan ta fahimci yarinyar a kwai tijara yanzu sai tasaka masa ciwon kai,

Jin maganar da yake mata kawai ta koma ta kwanta aƙasa taci gaba da kukan taƙaici biyu ya haɗar mata maimakon ya bata haƙuri amma shine zai rufe ta da faɗa duk abun da tayi masa bai gani ba ba sannu bare na gode saidai ma ya ƙara mata da wani laifin kuma ya hauta da masifa saboda shi ya kawo faɗa duniya,

Duk yanda yaso ta tsoratar da ita tayi shiru amma taƙi yi, uzuri yayi mata saboda yarinya ce kuma yasan shine da laifi kowa akayi wa haka bazaiji daɗi duk da ba da sanan saba ya yi hakan,

Abun da bai taɓa ba yau shi zaiyi tashi yayi da kansa ya nufi kitchen ɗin dan yi mata wani yasan duk abun da zai mata bazatayi shiru ba kuma yanzu halin da take ciki bazai iya dukan ta ba idan ma ya dake ta kukan sai yafi haka kuma babu yanda zai yi da ita ga bazai iya driven yanzu ba shiyasa amma da ɗaukan ta zaiyi su tafi gida shiyasa gwara ya bi da ita  a hankali su rabu lafiya,

Tunda ya shiga kitchen ɗin yake faman sakin tsaki yake tunani yafara yi yama ake yin dankalin yasan tunawa yayi ashe fa sai an fere da sannan a soya tab zai iya kuwa, ji yayi ina bazai ɓatawa kansa loƙaci ba wajen yi juya yayi ya fice daga kitchen ɗin yana fita yaƙara hango ta har yanzu kukan take wani tsakin ya kuma ja sannan ya juya ya koma idan ma baiyi ba ransa zai ta ɓaci gwara yayi mata ya hutawa ransa,

Da sauri yaje ya ɗebo dankalin tare knife ya fara fere sa yana ajiye wa akan drowar saida yafere wajen guda biyar da ya ajiye ya samu wani ɗan benci dake gefe ya zauna ya huta sannan ya tashi ya cigaba wajen guda ashirin ya fere sannan ya yayyan ka su yana yi yana zama ya huta agurin yankan kuwa saida ya ɗan yanke a hannun amma wuƙar bata shiga sosai ba, daman man da ta gama suyar dashi yana kan gas ɗin bata ɗauke ba dan haka sai ya kunna kawai baijira ya ɗau zafi ba ya antaya duka dankalin aciki ya koma kan bencin ya zauna yana jiran ya soyu ɗan jimawa kaɗan ya tashi yaje ya jujjuya sa yaga har yanzu bai fara soyuwa ba kuma baya tafasa, komawa yayi yaƙara zama bai daɗi ba ya ƙara dubawa still dai yana nan yanda yake,

Wajen mituna goma yaga dai yagaji da zaman sai ya tashi ya leƙa ta yagan ta a zaune ta haɗa kai da gwiwa tana abun da take,

komawa tayi gurin da yaga yana ta motsi sosai yana ta motsawa alamar zai soyu shikuma daman yaga ji da yaga haka sai kawai yayi tunanin ai yama gama soyuwa plate ya ɗauko ya fara kwaso shi daga cikin mai yana zuba shi direct akan plate ɗin ba wani jiran tsanewar sa kawai da man da komai yake zuba wa a kai, yana gama kwashe wa yakashe gas ɗin yaɗauki plate ɗin dankalin har zai fita sai kuma ya tuna ashe fa da egg ake cin sa a jiye wa yayi sannan ya nufi inda yaga crades ɗin suke yaje ya kwaso guda biyar yazo ya farfasa su ya zuba su a kwana nan da yaga ta yi amfani dashi, sai ya ɗauki maggi har guda uku ya zuba a ciki ya samu gishiri shima ya zuba da ɗan yawa ba laifi daidai misali amma a wajen sa albasa kuwa yama manta da batun ta ko ince ina jin baima san ana sakawa ba, ya kaɗa abun da gwanin kyau a ido yanda yake kaɗawa kai kace wani ƙwararren kukunne ga wani gumi da ya fara tsatstsafo masa na wahala, man da ya soya dankalin ko ince ya gasa dankalin baiyi tunanin ya juye saba ko kuma yarage a'a kawai shaka ya watsa kwan duka a ciki bayan ya zuba yayi kwance aƙasan man sannan ya kunna gas ɗin, ya zuba masa ido yana jiran ya fara tafasa ya soyu kamar dankalin abun da ya basa mamaki sai yaga wai har ya fara tafasa bai ba kamar yanda dankalin ya ɗauki loƙaci ba, daɗi ne yakama sa da yaga yana ta ƙara kunburowa mai na shirin zubowa yana ganin haka yayi saurin kashe gas ɗin sai da ya jira man ya ɗan lafa sannan yasaka ludayin ya fara ɗibo sa sai yayi mamaki gani duk ya dagar gaje bai haɗe jikin sa ba ba kamar yanda ta kawo masa ba, sai yabar hakan kawai azin soyuwa yayi da yawa shiyasa ya dagargaje tsamosa yayi tsaf gaba ɗaya ya ɗora sa akan dankalin sannan ya ɗauki plate ɗin ya nufi hanyar fita dashi, saida yaje bakin ƙofar sai ya tsaya yana ƙarewa abun kallo yadai san shidai a ido ba kamar haka yaci ba ɗazu amma yana da tabbacin dai haka ake, ƙara kallon sa yayi sai yaji wani irin daɗi ya ziyar ce sa wai shi yayi wannan gaskiya yayi namijin ƙoƙari saidai bayajin zai iya ci saboda ya dafa sai yaji duk ya haumasa kai(hmm daman idan ƙwaraiwa tayi ƙwaraiwa ai mutum baya iya cin abincin da ya girka musamman idan yayi kwaɓa irin taka, gaskiya Meer kaban kunya duk wannan iyayin ba a iya komai a kitchen ba daman,🤔😁😁)

A hankali ya shiga takawa cikin falon ya doshi inda take har yaƙarasa gaban ta sannan ya tsaya, bata ɗago ba tana kan gwiwar ta bataji zuwan saba sai wani nannaɗaɗɗen ƙarni da ya nannaɗe yashiga ya lallaɓa ta ƙasa ƙafar ta ya dakar mata hanci da ƙarfi, hakanne yasaka ta ɗagowa da sauri ba shiri dan ganin abun da yake neman saka ta amai......,

Ido biyu tayi da dankalin da yake miƙo mata, sannan tabi hannun sa da kallo har zuwa kan fuskar sa sannan ta ƙara mayar da kallon dankalin da a ido ma baida kyaun gani kana gani kaga ɗanyan abu babu alamar soyuwa ko ɗaya,

Gajiya yayi da tsayiwar har yake jin kamar ya ajiye mata amma ganin kallon da takewa abun sai yayi tunani ko burgeta yayi tayi tunanin ƙoƙarin da yayi,

Hannu tasa kamar zata karɓa sai kawai ta fasa ta miƙi tsaye tana kallon sa tace meye wannan?

Da mamakin rainin hankalin tambayear da tayi masa haɗe rai yayi sosai sannan yace "Idon ki me yagane miki,

Ta manta da kukan da take bata san loƙacin da ta tuntsure da dariya ba ai saikwa ta hau ƙyalƙyala dariya tana kallon sa waishi nan da gaske dankali ya soya tana kalla sai ta ƙara fashe wa da wata dariyar kamar sabon kamu, hannu takai zata karɓa ya janye haushi ya kamasa tama mayar dashi mahaukaci ya sha walaha yayi mata abu kuma tazo tasa shi agaba tana masa dariya ko taga wani abun na dariya ajikin sa, ko kuma abun da yayi ne yabata dariya oho mata,

Ameeaha fa sai an kawo ɗauki ta tafi sai dariya take harda su riƙe ciki ita ƙwanne ma yafi bata dariya yanda yayi wani wara wara kuma tana kalla ta fahimci acikin mai ya zuba sa, shiyafi komai bata dariya ashe duk burgar tasa bai iya girki ba sai iya dukan mutane,

Haushi da taƙaici da ya ishe shi da dariyar da take masa yasa ya ɗaga plate ɗin hannun sa ya kifa mata shi gaba ɗaya a fuska...........✍️✍️✍️

tofa team ɗin Meer a kawo taimakon gaggawa a koyawa Meer girki kar raini ya shiga tsakanin sa da Ameesha dan naga alamar bazata ɗaga masa ƙafa ba wajen dariyar nan tata,

To fa ga kuma bawan Allah ko waye wannan tsohon da yazo gurin Ameesha taya akai yasan ta haka to kodai bokanne kamar yanda Ameesha take zato, Amma dai muje zuwa muji shi kuma dame yazo,

*_to ya kuka ga wannan page ɗin da aringayin irin sa da kuma aringayi kullum duk ƙanƙantar sa wane kuka fi so???????_*
Chapter 135 · 0% Book details