← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 139

Sashe 19

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannun sa har karkarwa yake wajen budewa datar sa ya shiga WhatsApp yana shiga messages suka fara shigowa amma ga mamakin sa bega sabuwar number ba har yaja tsaki zai fita daga WhatsApp din sai yaga saqon my man ya shigo be dubaba yajuyo ya kalle sa sai yaga bama ya falon har ya fita daga ciki hakalin sa ya maida kan wayar sannan ya bude message din sameer dan ganin abun da yaturo masa saboda begane rubutun dayayi ba aqarshe yaga de 3  messages besan saura biyun me ya turo ba da haka yabude kanasa tsaye danshi har alokacin ransa bai kawo masa komai ba saida idon sa yasauka akan video da hoto guda daya amma basu gama budewa ba saboda ahaka ya saita wayar sa duk hoto ko video sai yayi downloading dinsa dakan sa shiyasa bega meye ba sai kawai ya dannan videon gabansa ne yafadi ganin sa kan yarinyar da yataimaka ashe tun lokacin da yake danna mata qirji kuma dake ta baya ya dauka sai ka rants wani abun yake aikatawa sai lokacin da ga tsugunna yana goge mata baki da likacin da ya bude mata baki dan ganin farare ne ko yellow ne dan iskancin daukar tasama kuna sai yasa stop agurin da yasa hannu ya toshe mata hanci be dauka dannan ba saikawai gurin da yasaka bakinsa cikin nata muraran kana gani zakace kissing dinta daga nan kuma sai gurin da suke kallon juna har qara zumin din fuskikin su yayi suka fito da kyau kana ganin kwalliyar fuskar ta nanma idan kaga kallon da sukewa juna zakayi zaton irin angana kiss dinnan anayiwa juna kallon love irin kowa nawa kowa kallon bangaji nan ba  muqarayi wani be isheniba fassarar kallon da sukewa juna kenan awayar 😂 Lol
ganin yaqare yasashi fita daga videon yakoma ya bude hoton shikuma hoton lokacin dazata tashi yayi saurin kai hannun sa yace ta koma ta kwanta daidai inda yasa hannun sa ajikin ta daidai gurin ya daukesu jiyayi kamar ya fasa wayar dan ta qaici fasa zuwa inda yayi niyar zuwa yayi kawai ya juya tare da yin kwafa yabi bayansa yana ayyana irin rashin mutuncin da zaiyiwa sam idan yakamasa shiyasa ashe yabar falon to kwa yau zai nemosa duk ma inda ya shiga..

Azeema dake kwance jin shiru yasata dan bude ido tashi tayi zata zauna tana juyawa taga shettima a tsaye sai tayi saurin komawa ta kwanta saboda atunanin ta ko fita sukayi dataji shirun yayi yawa ashe yana nan to meyake atsaye kuma ina dayan dataji muryar sa agun shi ina yake tunda taji muryar shi taji tanaso taganshi saboda yanda yake magana muryasa tayi mata dadi murya ahankali ba wani daga murya acikin ta kanaji zakasan me ita baqaramar nutsuwa ce dashi ba tun amuryarsa zaka gane hakan tana so taganshi amma tsoron shettima yagane ta yasa takasa bude idon ta ta kalleshi amma har cikin ranta ta qosa da ta gansa amma ba hali Allah yasa wataran yaqara dawowa taganshi,
tanajin takun sa alamar ya juyo tayi saurin rufe idonta saida yagana fita daga falon sannan ta bude idon ta tare da tashi zaune zama tayi tana sauke ajiyar zuciya bi falon tayi da kallo sai yanzuma tafara tunani wai ya akayi ma ta ganta anan tunawa tayi lokacin da suka fito da papa har tazo zata gaida su to me yafaru da ita tasande Ammah tace ta gaida su yayintane hannu tasa abaki irin mutum yanason ya tuna wani abun tayi wajen minti 1 tana tunani sai kawai tayi zunbur ta miqe tsaye tana girgiza kai wlh shine shi naqara gani akaro na biyu arayuwa ta to amma meyasa inde nagansa bana qara ganin sa gashi idan nagansa rannan ance min na suma kenan yauma suman nayi to me hakan yake nufi inde ba aljani bane meyasa nake suma idan nagansa alhalin kaf duniyar nan banda wanda nake burin ingani inbashi ba banida burin da yarage min arayuwa irin inga gani gashi wake daya koda besoni ba duk danasan ma daman baze taba sona ba amma ni koda ganin sa ne ma kadai akabarni hakan ma zaimin dadi gashi kuma sai gizau yake min yana tsoratani hartakaini ga suma na shiga ukuna ni Azeema meke shirin faruwa dani kar aljanu subude min ido Allah na roqeka kaciren shi azuciya ta Allah kasa ba aljani bane idan kuma aljanine Allah kamin tsari dashi Allah kasa kar nasake ganin sa arayuwa ta mutum ne kamar ke taji anbata amsa daga bayan ta saurin juyawa tayi gabanta na faduwa Ammah ce ta qaraso inda take tana kallon ta ganin yanda  tashiga tashin hankali ne yasa amma cewa dukan su da kika gansu jikoki nane kuma duk anan suke nima nayi mamakin sumanki daman saboda nayi tunanin idan kika ganshi zaki iya suma saboda kyaunshi da kuma mamakin da kika shiga duk su suka haddasa miki doguwar suma,
Jikin tane ya shiga karkarwa shikenan watakil taganota  Allah yasade bataji duk zancen datakeyi ba da kyar ta iya hadiye wani abu da yatokare mata makogaro sanna  ta bude baki daqyar zatayi magana kenan
Ammah ta dakatar da ita tare da cewa kar kice komai kije daki ki goge kwalliyar nan sannan kisaka kaya complete mayi maganar daga baya  ina nan inajiran ki bata da zabin da ya wuce bin umarnin ta kamar wacce kwai yafashe ma aciki haka ta daga qafar ta datayi mata nauyi da kyar take janta jiki asanyaye gabanta na faduwa fat fat tabi ta gabanta batare da tace komai ba ta nufi dakin da tafito ranta fal da tunani kala kala ahaka taje dakin tana zuwa ta shige bandakin sai kawai ta fashe da kuka da ita kanta batasan dalilin yinsa ba sai da tayi me isarta sannan tayi shiru wayar ta ta dauko ta kira saleem taci sa'a kuwa bugu daya ya dauka tare da cewa salamu alaikum auta qanwata ta kaina Allah yasade kiran nan inji alkhari sunan shi takira tace "yaya"
yana jin muryarta yagane ba lafiya ba cikin dan tashin hankali yashiga tambayarta lafiya cikin shashsheqar kuka tafara yimasa bayanin duk abun da yafaru amma bata gaya masa ganin sam ba saitace masa wannan mutumin da mukaje office dinshi abokin aikin sa wanda inde taje yake cewa ta zauna agunsa yace eh yagane sa nande tabashi labari banda ganin sam alabarin nata shima ya shiga tashin hankali sosai nande yarsa shawarar da zai bata saikawai de ya kwantar mata da hankali tare da cewa ba abun da zai faru amma kartasake ta fadi gaskiya kawai tace tasaba ganin sane amafarkin ta shiyasa yau da tagansa take tunanin ko aljani ne idan tafadi hakan za ayarda to tace masa tare da daga masa kai kamar yana gabanta sannan tace ya turo mata da number shi mutumin da to yace mata kawai be tambayeta dalili ba ya katse wayar ba jimawa ya turo mata dubawa tayi ta dauka tayi saving dinta sannan ta shiga tayi typing din message zata tura masa amma bata turaba sai kawai tabar wayar awajen in case koda lokacin turawar yayi sai ta tura masa ba tare da wani ya kula da ita zatasan yanda zatayi kar akamata  tunawa da anajiran ta yasa ta maida wayar gefe sannan tayi saurin daukar sabulu ta wanke fuskarta saida tayi wajen wanki hudu ta tabbatar da fuskar tafita sannan ta dauko wayarta tafito wasu kayan ta dauka tasaka amma bata fita da mayafin ba sai ta dauki wani hijabin da yayi kala da kayan ta saka ta fito das da ita farin ta da kyawunta suka bayyana tafito a Azeemar ta tada sannan tafito falon inda tabar Ammah ana ta dawo ta sameta tana zaune tana jiran ta tunda tafito Ammah take binta da kallo har ta qaraso ta zauna aqasa daga gefen qafar ta tare da sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta gaban ta na faduwa  tana jiran taji abun da zatace mata,
Ammah ta bude baki zatayi magana kenan taji sallamar shettima hakan ya dakatar da ita daga abun da tayi niyar fada qarasowa yayi yana ta kunfar baki saboda suk inda yake sa ran zaiga sam yaje begansa ba shiyasa yaqara dawowa nan ya duba ko zai gansa ya bude baki zaiyiwa Ammah magana sai kawai yaji maganar ta makale sakamakon tozali da idonsa yayi masa da Azeema qarar message dinne ya katse masa tunanin da yake shirin fara yi Ammah dake binsa da kallo tanajiran taji me zaice tace ya akayi ne ina me sunan baban yake be bata amsa ba yazaro wayar sa daganin me kuma yaqara cemasa dan shi duk atunanin sa ko shine yaqara turo masa da wani abun yana dubawa yaga bakuwar number budewa yayi ransa na qara bace gefe kuma ga tunanin ganin Azeema dayayi yarasa ma wane tunani zaiyi fara karan ta sakom yayi kamar haka

       *dan Allah dan annabi na roqeka kar ka nuna
           kasanni zanyi maka bayani daga baya na    
           roqeka kayi min wannan alfarmar banzo
           nan dan na cutar da wani plss and plsss
           karkace komai akaina plsssssss*

kurawa message din ido yayi bayan yagama karantawa tana satar kallon sa ta dauka ma baze taimake ta dan har tacire rai ma sai kawai taji yace Ammah daman nida wannan tuzurun naki ne yayi min wani babban laifi naje kuma na duba ya buya narasa inda yaje sai yanzu ya turo min wai inke waje insame shi yafada yana juyawa zai bar gurin tace baku gaisa da ita bafa gata ta wanke kwaliyar tayi hakane dan tanaso tagane acikin su waye yasa ta suma amma ganin yanzu ba ta suma ba yasa tagane amsarta watakon me sunan babane yasata ta suma zai fita kenan taqara tsayar dashi tace abincin naku fa kace masa yazo kuci kar ya kwanta ahaka dan nasan halinsa watakil shikenan baze dawo nan ba said da safe yace mata "to" kawai dan lokacin har yakai qofar fita budewa yayi ya fice daga falon nauyayyir ajiyar zuciya Azeema ta sauke aboye ganin ko kallon inda take ma beyiba ya fice hakan da yayi ba qaramin jin dadi tayi ba ranta taji ya kwanta tana murna aranta,
Chapter 19 · 0% Book details