← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 139

Sashe 125

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dagan nan kuma papa da su maama suka fito atare dan nufar part ɗin ta suna fitowa aka fara sakin saraiwa ana hurata ga kuma ganguna da wasu suke bubbugawa na murnar dawowar gimbiya sabreena saboda gaba ɗaya ilahirin Masarautar babu wanda baiji labarin da wowar ta ba kuma an fahimtar dasu cewar daman ba mutuwa tayi ba shiyasa suka haɗa wannan abun da su nuna farin cikinsu akan hakan suna waje amma babu labarin da bai riskesu ba daman na saukar sarki agaban su akayi basa buƙatar ƙarin bayani, kiɗa suke sosai wasu kuma ma rawa tsofaffin bayin da suka santa mata suma suka dawo ta bayanta suka fara take mata baya tare da kwararo mata kirari nan da nan maama tafara jin kanta asama tunawa da baya da tayi daman tafiyar ta ta daɗe da canzawa ta koma gimbiyoyin ita da papa ne agaba sai Meer da ta riƙo hannun sa badan yanaso ba kawai yake binta, sai su Abu da ummy da dadda baya su Ameesha kuma suna tsakiyar su ita da Azeema da ta riƙo hannun ta, harda gwaggo ma itama tana cikin tawagar su bata bari anbarta abaya ba,

ahaka suka ringa tafiya anayi musu kiɗe kiɗe tare da kirari har aka rakasu part ɗin sannan suka dakata masu kiɗan matan kuma Saida suka rakasu har ciki sannan aka sallame su tare da yi musu godiya,

Sam, bossay, shettiman, harda hamza ma da suka jawo shi ta ƙarfin tsiya saboda tausayin sa suke yi atare suka fita sai suka wuce part ɗin fulani gaba ɗayan su dan su samu su huta kuma su tattauna,

su waziri ma da sarki Salahudden ahaka dai ɗaya bayan ɗaya dai ƴan cikin fadar suka ringa ficewa daga ciki Ammah ce ƙarshen fitowa daga ciki tana tafiya tana harhaɗa hanya saboda jirin da yake ɗawainiya da ita ganin yanda akayi watsi da ita anma manta da ita agun sunyi gaba sun barta hakan sai taji babu ɗaɗi aranta ga kanta da yake mata wani irin ciwo ahaka ta daddafa taƙarsa har part ɗin ta tashige ɗaki tare da faɗawa kan gado tana sauke numfashi,

su papa ma bayan sun shiga wata hirar suka ƙara ɗorawa kiran sallah ne kawai ya tashe su shima kuma suna idar wa suke kara dawowa su ɗora daga inda suka tsaya abinci kwa mai rai da lafiya akayo musu daga part ɗin momma sukaci suka ƙoshi basu suka dakata da hirar ba sai dare sannan aka raka su Abu inda aka gyara musu Ameesha da dadda kuma suma aka basu ɗaki ɗaya harda Azeema, sai kuma wani ɗakin dake ciki maama tace jikantane zai zauna meer ya zauna tare da ita bataso yayi nesa da ita su zauna part ɗaya gwaggo madai da ƙyar ta iya tafiya makwancin ta,

zuwa loƙacin kuma su sam har sunje sun dauko su baban sumy da wanda suka ɗauko a Abuja saida ba azauna dasu ba anbari sai zuwa gobe suma kuma su bossay duk gida suka tafi shi da shettiman yarage daga sam sai hamza da yakasa sakin jiki kwata kwata yanayi abu kamar marar lafiya......✍️✍️   

                     💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 97

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

     washe gari yanda aka kwanta da farin ciki haka suka tashi da farin ciki kowa ka tsinta acikin masarautar yana farin ciki da dawowar ahalin masarauta labaride ya karaɗe ko ina da ina har ƴan wajen gari ma sunji labarin abun dake faruwa shikenan yanzu za afara mulkin adalci, kowa yayi Allah wadaran da halin da  fulani ta tafka shekara da shekaru ana mulkin zalinci acikin masarautar yau gashi rana ɗaya Allah ya kawo ƙarshen abun,

suna zaune a part ɗin maama gaba ɗayan su bayan sun gama yin breakfast suka dawo falo suka zauna har gwaggo ma har tazo falon yacika maƙil da mutane wannan yazo yafita wannan yazo fita ana ta zuwa tayasu murna wasu kuma gulma ke kawosu suzo su ganne wa idon su abun mamaki,

basu suka daina karbar baƙi ba saidai aka kira sallar Azhar sannan aka dakatar da kowa bayan sunyi sallah sun dawo suka ƙara cin abinci rana sannan aka ƙara baje babin hira kafin daga bisani papa ya umarci su sam da suma duk ana falon tare dasu, yace "suje su ɗauko mishi mutanen da suka ɗauko jiya amma can cikin fada zasu kaisu zai zo ya samesu dan haka ba ɓata loƙaci sukaje suka kwaso su daga inda suka ajiyesu suka kaisu cikin fadar kamar yanda papa ya basu umarnin haka sukayi sannan suka dawo suka sanar dasu,

da papa da gimbiya sabreena da dasu gwaggo kusan dai su duka suka ƙara fita suka nufi fadar tare da fadawansu dake taka musu baya,

Ameesha kam tun asubar fari su Amra da sukaji labarin ƴar uwar su ce sukaje gurin ta suka ɗauko su ita da Azeema suka koma part ɗin momma sukaci gaba da shagalin su da taya juna murna,

su papa na ƙarasawa cikin fada kowa yasamu wajen ya zauna saidai fa har yanzu kan karagar mulki babu wanda yake zama akai so ake sai angama komai sannan a nutsu ayi babban shagali a ɗora sabon sarki, yanzu dai kusan papa ne akan gaba shi zai ringa juya komai kafin nan gaba saboda acikin su babu wanda yasan kan mulkin dole sai yana nuna musu komai ahankali,

bayan kowa ya zauna fadar ta ɗauki shiru aka umarci su baban Meer da su ma tso gaba su gabatar da kansu da kuma laifin da ake tuhumar su,

Matsowa sukayi jikin su ba karkarwar tsoro duk sunyi zuru zuru da su ga wahalar zaman da sukayi su sukaɗai baci ba sha saboda sam yama manta dasu babun da ake basu,

baban summy ne yafara ɗagowa cikin mawuyacin halin da yake ciki yace yace wallahi wallahi bansan komai ba kuma banda masaniya akan komai iya abun danasani kuma nagaya musu, yana maganar yana ɗan tsatstsorata yana kallon gefen sa sakamakon ganin Meer akan sa yana zagaye sa yana mishi wani irin kallo hakanne yasashi dakatawa da maganar da yake cike da tsoro da fargaba,

Papa ne yatsareshi da ido yana nazarin maganarsa kafin daga bisani ya ɗan numfasa yace "katababar maganar da kafaɗa iyaka gaskiyar ka kenan....?

kai abban sumy ya ɗaga masa tare da cewa "eh"

jinjina kai papa yaƙara yi sannan yace "tom naji bayanin ka amma fa kasani idan bincike yayi bincike aka gano kasan wani abun bayan wannan to wallahi hukuncin ka sai yafi na kowa ka yarda? yace "eh"

bayan yagama nasa bayanin aka koma wajen ɗayan da yake ta faman rarraba ido kamar ankama ɓera arami,

papa yace muna sauraron ka kagaya mana inda ka mayar mana da ɗa kuma waye yake saka,

cike da fargaba ya ɗago yana kallon papa sanna yace wallahi wallahi wallahi nayi muku rantsuwa har uku na rantse da mahallici na ni kaina bansan wannan mutumin da kuke magana akai ba hasalima ban taɓa ganin sab........,

baikai karshen maganar ba meer dake gaban sa ya kwashe shi da wani irin gigitacen mari tare da kai masa naushi afuska Meer bai sake shiba yakuma jin wata uwar shaƙa daga gurin sam da ransa yagama ɓaci da jin rainin hankalin da yake neman yayi musu, dan haka shima ya tashi rai aɓace ya shaƙesa da ƙara masa wani naushin sannan cikin ɗaga murya sam yace "mu zaka rainawa hankali da wata banzar maganar ka ko ka mayar damu ƴan ƙwaya ne ka kiramu da kanka kayi mana wani gargaɗi da tsoratarwa kuma shine yanzu zaka zo mana da wata banzar magana how dare you ehhhh.....! ya ƙarasa maganar tare da buga masa wata iriyar gigitacciyar tsawa idon sa har ya canza kala saboda tsantsar ɓacin rab da yafara zuwan masa,

jin haka yasa meer yaƙara karɓar sa daga hannun sam suka fara pacing pacing da shi suna neman kasheshi da duka, sannan su Abu saukayi saurin dakatar dasu da ƙyar aka iya rabasu aka kwace sa daga hannun su,

ahakan ma saida papa yasa baki sannan suka dakata su ka koma gefe kowa jikin sa na tsuma duk wanda yagansu dole su furgita ka su baka tsoro ko basu ce da kai komai ba kallon yanayin su kaɗai zai sa ka shiga taitayin ka,

shikam da aka gama luguda yana yashe aƙasa sai faman sauke ajiyar zuciya yake akai akai dan yaji ƙanshin mutuwa,

maama ce tace masha Allah tun ba aje ko ina ba kenan kadai ji ajikin ka ko dan haka sai ka taso ka faɗa mana gaskiyar magana idan kuma kace kwana kwana ɗin zaka cigaba dayi bazaka faɗi gaskiya ba to kai zaka sha wahala gaka ga su zasu ɗora maka daga inda suka tsaya ne ba ruwan mu saboda haka katai maki kanka kayi abun da yakamata dan tsiratar da ranka in kuma zakaci gaba da rufawa wani asiri to kaine aruwa dan abanza zasu kashe ka kuma sun kashe banza sai ka zaɓa idan sirrin su yafi ranka to in kuma ranka yafi sirrin su yarage naka.....,

ai ba shiri ya tashi zaune yana gyara zaman sa yanda zaiji daɗi saboda jikin sa duk amace yake yayi tsami,

saida ya taro nutsuwar sa sannan yafara magana cikin sunkuyar da kai yace "zan faɗi duk abun da nasani kuma iyaka gaskiya ta,

amma dai kamar yanda nace muku bansan shiba ban taɓa ganin saba to hakanne saidai zan baku number wanda muke communication dashi ta waya dan koni yaƙi bari insan shi ko in haɗu dashi bamu taɓa haɗuwa ba saidai ya ɗorani ne akai duk ranar da wani abun yafaru insanar dashi......,
Chapter 125 · 0% Book details