← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 139

Sashe 66

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda tafara maganar yake bin bakin ta da kallo har saida tayi shiru sannan yace to shikenan na haƙura badan halinki ba,  sunana Ammar duk danasan ma kinji abakin su Ni yayane awajen su inafatan kema zaki ɗaukeni amatsayin yaya ni kuma zan ɗaukeki amatsayin ƙanwa kamar su ina fatan hakan ba wata matsala,?

   "ba komai nikuma sunana Ameesha

    "nice to meet you"
  "same here" ta bashi amsa
sosai ya shagala da kallon ta shide ganin ɗaya yayi mata amma duk tagama tafiya da imanin sa jiyake kamar ya tashi yayi ta tsalle ya rungume ta saboda yanda yake ji acikin ransa,

  "yaya bari muje mu shirya

"Ok"
  kawai ya iya basu amsa sukuma suka juya suka nufi hanyar fita
tunda suka fita yake zubawa bayan ta ido bai ɗauke ba saida suka fita daga falon yadena ganin su sannan ya miƙe shima yana ƙara sakin murmushi da saƙe saƙe fal zuciyar sa ya nufi nasa part ɗin dan shiryawa shima,

tunda suka fita suka fara tsokanar ta wai daga gani fa yayansu ya ƙyasa da ita itade saidai tayi musu murmushi batace musu komai ba har suka ƙarasa part ɗinsu suka shiga da murnar su suka sanarwa momma dake falo tana jiran shigowar su,

  itama da murnar tace kaga ƴan gatan Ammar to sai kuyi sauri kar kuɓata masa loƙaci yace ya fasa musamman ke Amra me shegen nawar shiryawa sai kiyi sauri tace momma ai ni zan fara shiryawa ma duk saina rigasu shiryawa,

momma tace  dade bansan halinki ba sai kice haka,

"Wallahi momma da gaske nake,

momma tace "to Allah yasa da gaskenne,

  "tace "Ameen" tana dariya

   Hamra tace "wallahi momma karma ta shirya taga inzamu jirata tana zama zamuyi tafiyar mu mubarta taji asalan sa,

   "ku kun isa ku tafi kubarni ai wallahi indai banje ba to babu me zuwa aciki kinku gwarama ki gyara maganar ki yarinya,

  "au nice yarinyar taki ni kike cewa yarinya momma kina jin abun datace ko,

    *Momma tace "ku tsaya faɗa ku ɓata loƙacin ku anan ku daman ai ba a abun arziƙi da ku lafiya sai kunsa mutum yi da baki,

ƙwafa Hamra tayi tare da jen hannun Ameesha suka wuce tana gunguni ƙasa ƙasa,
Amra ma bata ƙara cewa komai ba tabi bayansu suka tafi ɗakin su.....

    da kallo momma tabisu tana jinjina irin wannan halin nasu na faɗa da bazasu taɓa zama lafiya ba sai kaji kansu ko yaushe zasu girma su dena wannan halin nasu......

"Assalamu alaikum ina masu gidan nan ?

sallamar ce ta katsewa momma tunanin da take da sauri ta miƙe tsaye tana washe baki tace lale marhaban hajiya gwaggo yau kece awajen namu sannu da zuwa tafaɗa tana nuna mata waje,   zama gwaggo tayi itama
fuskarta dauke da murmushi 

bari inkawi miki abun motsa baki gwaggo dan nasanki da kwaɗayi bakin ki besan tsofa ba,

   dariya gwaggo tayi tace naci ƙaniyar ki kinji mun yarinya nikike cewa ina kwaɗayi yo inama ruwanki da bakina daman baki na tsufa to saidai ko inna uwacen taki ne ya tsufa amma banawa ba dannawa yama fi naki kwari aradun Allah, ni yi saurima kisamo min abu me ɗan daɗi daɗi kinsan banason barin bakina hakan nan ba abu acikin sa nafiso kullum inganshi yana motsi,

  dariya momma tayi sanann tace kingani ko ai kwaɗayin kenan idan so kike kiji bakinki kullum cikin motsi ai goro yakamara ki nema kamar yanda ko wane tsoho yake ciki idan ya tsufa amma ke saboda kwaɗayi kinƙi cin goro sai abu irin na matasan mutane irin mu kinci zamanin ki kinci na ƴaƴan ki ga na jikokin ki amma duk dahaka be ishe kiba sai kinci na tattaɓa kunnen ki gaskiya yakamata kibarmu haka kiɗan bamu guri musha iska ko masumu muci wani abun muma amma duk kinbi kin handime na kowa,

   uwarki sa'adatu nace uwarki sa'adatu ko bakiji ba in ƙara maimaitawa uwarki sa'adatu tafaɗa tana cilla mata daƙuwa kinji mu da ja'irar yarinya uban me zanyi da goro ai ni haryanzu banyi tsufan da zanci goro ba ke koma nayi bazanci ba cin goro ai na marasa aikin yine abun da inkana cinsa kamar taba yake zamemaka idan bakaciba kashiga wani tashin hankalin gashi kuma daman lafiyar ka kake lalatawa shiyasa ma masu cin suke mutuwa da wuri basu san kashe kansu suke ba,

ke wallahi ma Allah ya isana idan kika ƙara cemin inci goro bansan me yasaba kaf cikin ku kinfi rainani wallahi to wallahi saidai uwarki ta baku gu kusha isakar dan duk sai kun mutu kunbarni sai naga gawar kowa acikinku har ubanna ki daman shi naga harma yafini tsufa da wuri zai mutu wannan wallahi bai gaji jiki irin nawaba duk wanda ya biyo ni bazai mutu da wuri ba amma duk da haka sai ya rigani mutuwa,

    ohh gwaggo ai namanta ashefa ke za abawa gadin duniyar ma gaba ɗaya kece me gadin ta sai kowa na duniya ya mutu ya barki ko hajiya gwaggo,

  aniyarki ta biki komade menene sai kun mutu kun barni ko banyi gadin duniya ba ammade kiris zai rage bankaiba dan ina mutuwa ba daɗewa za ayi tashin duniya kowama ya mutu a huta,

   dariya momma tayi ganin gwaggo zata fara sakin layi yasatayi saurin cewa bari inkawo miki wani abun idan kinci maci gaba daga inda muka tsaya Hajiya gwaggo me ranƙafe Allah ya nuna min ranar mutuwarki ranar har ƙaramin shagali zamu haɗa tana tafaɗa tayi saurin barin wajen amma duk da haka saida gwaggo ta jefe ta da filo tana ƙara sirfa mata wata masifar harda su zagi itade momma dariya kawai take har ta ƙarasa kitchen daman sun saba indai suka haɗu sun ringayi kenan har sai sun rabu kuma daman duk cikin jikokin ta sunfi wasan jika da kaka shiyasa yanzuma da suka gama zaman fadar da harta tafi sai kuma ta fasa tace sai tazo wajen ta.......

    ba jimawa momma ta fito da try cike da kayan marmari data yanyanko mata sai sai juce da kuma snaks duk ta haɗo mata ta ajiye mata agaban ta sannan ta kalle ta tace to acici dame za afara gashinan kicinye idan ma bai ishekeba sai aƙaro wani tafaɗi maganar tana tashi ta koma gefen kujerar ta ta zauna tana kallon ta,

  gwaggo kam sai faman washe baki take saikace bata taɓa ciba ko kuma bata saba ciba haka take intaga abinci itade tana son abinci koma meye kawai taga bakin ta na tauna,

    meat fie ta fara ɗauka takai baki saidai tauna ɗaya tayi masa ta dawo dashi saboda yaji da taji,

    "Amma kede akwai muguwa wallahi kinsan bana son yaji ko kaɗan amma shine kika kawo min shi danki cutar dani ko to ke da Allah ga abunki nan ni nama fasa ci gaba ɗaya sai ki kwashe kayanki hankalin ki ya kwanta naƙi ci daman haka kike so tafaɗi maganar harda hararar ta tana kawar da kai gefe,

    "momma saura kiris dariya ta kwace mata ganin yanda tayi saurin kaiwa baki kuma tayi saurin dawo dashi kunshe dariyar ta tayi gudun karta ƙara harzuƙa gwaggo tayi saurin saukowa ƙasa tace haba gwaggo ta kinsan de ai bazan taɓa baki abun da zan cutar dake ba kiyi haƙuri kici wani abun wallahi bansan da yajiba aciki bani nayi ba kuma banci ba ga fruit nan kisha bari insamo miki wani abun marar yaji wallahi bansan da yaji ba Allah da gaske nake, "dalla malama rufe min baki kina sane ai kikawo min bazan taɓa yarda bakisane ba ni bari ma kiga tafiyata basai na ƙara dawowa wajen ki ba bare kicutar dani sokike daman kiga bayana ai to saidai ni inga bayanki duk baƙin cikin ki, tafaɗa harda dungure mata kai sannan ta miƙe tsaye,
da sauri momma ta miƙe itama tace dan Allah gwaggo na kiyi haƙuri kici wani abu inma baza kici komai ba kizauna muyi hira kinga kindaɗe daman bakizo ba kuma nasan inkika tafi zamu daɗe bamu ƙara haɗuwa ba,
"ni bazan zauna ba idan kinason ganina kibiyo ni inda nake amma bazaki ƙara ganin ƙafata anan gurin ba, ke karma kizo inda nake na hutar dake daga yau bani bake munkunce mutun cin dake tsakanin mu mun raba gari dake tunda ke muguwa ce,

"haba gwaggo tunda muke dake haka ta taɓa faruwa banda yau yauɗin ma kuskure akasamu dan Allah kizauna,
da ƙyar tasamu ta lallaɓata ta haƙura ta zauna itama ɗin daman ba tafiya zatayi ba tsokanar ta take kawai,

   zama tayi taci gaba da shan fruit tana sha tana lumshe ido saida ta kusa rabi sannan tadakata tare da kallon momma tace ke wai ina wannan marar mutuncin ɗan naki da baya ganin kowa da gashi naji ance yadawo amma bantaɓa ganin saba,
"ai ya daɗe dawowa ma gwaggo dan yamafi wata ɗaya baizo ya gaidake ba?

    "kinturo sa ne ai bakice yazo ba duk wani hali da yakeyi ai ku kuke ɗaure masa gindi shiyasa yake ƙara raina kowa ni asuwa zaije inda nake harma ya gaida ni yaron da wataran zaka haɗu dashi ahanya amma yanuna baisan dakai aduniyar bama bare yasan kana gurin ai wannan yaron wallahi kaf zuri'ata bame baƙin hali irin nasa ga shegen taurin kai bansan inda ya ɗauko wannan mugun halin ba dannidai bahaka nakeba kuma ƴaƴana ma bahaka suke ba kuma Sa'adatu ma bahaka take ba bare ince ki ita yagado,
cikin sanyin murya momma tace wallahi gwaggo ba wanda yake ɗaure masa gindi kullum cikin faɗa nake masa amma kullum abun nasa gaba yake saidai mucigaba da yi masa addu'a itakaɗai ce zata gyara sa,

taɓe baki gwaggo tayi cikin ko inkula da yanayin da momma tayi magana saima ciga da cewa tayi kedai wallahi baki yi sa'ar ƴaƴa ba hargwangwan da ɗayar ma akan wannan ja'irar yarinya me kama da tsutsotsi kullum cikin mutsul mutsul take sai fitina kamar beranniya batason zama guri ɗaya ni harna tsani ma tazo inda nake ganaci kuma ina koranta tana ƙara danno kai  kace kuma zaka daketa tasa kajiwa kanka ciwo abanza shiyasa bana kulata idan tazo nake mata banza tagama abunta ta tafi dan wallahi tafi ƙarfin.......

  "bata ƙarasa maganar ba taji faɗowar mutum akanta...
Chapter 66 · 0% Book details