← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 139

Sashe 43

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   ______MEER
    "Tunda safe da yatashi yayi sallah be komaba yafara shiri yayi wanka ya shirya ƙarfe shida yafito daga part dinshi taku yake kamar baya don taka qasa a nutse yakeyin ta tamkar wani basarake farine sosai innace sosai irin sosai dinnan dogone amma ba can ba yana da faffadan qirji da cikar haiba sai sumar kansa da tayi wata iriyar kala me shegen daukar ido ko da kallon sumar aka barka sai ka kusan kwana agun kana kala batare da kagajiya ba saboda wani irin gyara da akayi mata gata awani irin kanannade kanannade tadan zubo gefen goshin sa ta barin hagu da barin dama sai tsakiya da shi gashin wajen baikai sauran tsawo ba wani style din akayi dashi can kuma tabayan ƙyeyarsa yadan sauko masa har wajen wuyan sa saida aka saita qarshen yanda suka tashi duk kai ɗaya kuma annade shi taciki sai yazamana idan ya motsa shima gashin sai ya motsa saboda ba amanne yake da kansa ba abunde duk yanda zan fasalta muku baza kugane ba har sai kungani da idon ku ammade kuyi qoqarin yin imagine din kannasa nasan zaku dan hasaso ko kadanne,
kan fuskar sa nadawo inda yake kwantacciyar gira waɗan da suke ajere kamar anyi shaving dinsu sai eye lashes dinsa da sukaiyi zara zara idan yabude idonsa sai sun kusan tabo girar sa idonsa farine tass ƙwayar idon kuma brawn color ce dan zagayanta kuma yadanyi Goulding sai idon yanada wata iriyar kala me daukan hankali ga idanun sexy ne sai dogon hancinsa siriri wanda yaqara qawata fuskar tasa sai kwantaccen gemun sa da yafaro tundaga wajen sajensa zuwa habarsa kana gani shima kasan baqaramin kudi ake kashe masaba wajen gyarawa sai dan karamin bakin sa red colar kamar ya shafa masa janbaki gwani burgewa  wanda yake dauke da jerarrun haqora farare masu kyan gaske sai wushirya atsakiya data qarawa haƙoran kyau ga dimpuls dinsa sun lotsa sosai koya yadan motsa baki sai kaga sulotsa kana ganinsa kaga farin balarabe alarabawan ma irin masu kyau dinnan  kyaudai iya kyau kamar shi ya kanshi Allah ya hore masa indai kyaune ba ƙarya saidai kowa yabiyo bayansa duk da hakama fa wai dan baku gansa ba duk yanda zan fasalta muku shi u can't never imagine,

  "lokacin da ya sauko qasa ummyn sa bata nan daman kuma yasan bazai sameta ba,
sai masu aikin gidan suna ta aikace aikacen su suna ganin shi suka shiga gaidashi amma kamar da gini suke haka ya wuce yabarsu agun daman kuma sunsan za arina sunsan halinshi dan wasuma da basu dade da zuwa ba sai su rantsi basutaba jin muryar saba wadanda suka dade na baifi aqirga ba suka taba jin maganar sa ba,

  yana fita yanufi parking lot saidai kafin yaqarasa driver dinsa ya rigasa qarasawa sauri yayi ya bude masa qofa shi kuma ya shiga sannan yazagaya ya shiga shima tare da tare da motar suka fita daga gidan basu dau lokaci ne tsawo ba suka qarasa asibitin bayan sun shiga ciki driver ya daidaita parking ya fito ya bude masa yafito cike da takunsa na isa da qasaita yake tafiya duk da ya matsu yaganta amma hakan baisa shi yayi sauri ba saboda shi haka yake a rayuwar sa bai iya sauri ba ko gaggawa komai a hankali cikin nutsuwa yakeyinsa ba garaje a harkarsa,

ahaka yake tafiya har yaqarasa bakin qofar dakin da take kwance tura qofar yayi ahankali sannan yasaka qafa ɗaya sannan yaqara saka ɗayar yashiga tura qofar yayi sannan ya jingina da qofar tare da harde hannun sa ya zuba mata idanu sai yanzu yaji sanyi aransa da yazo yaganta akwance kamar yanda yabarta yakai wajen minti biyu awajen kafin yaɗaga qafarsa ahankali yafara takawa zuwa wajen gadon da take kwance kujera yaja ya zauna tare da zubawa fuskarta ga mamakin sa kawai sai yaga hawaye yana zubowa daga idonta zunbur yayi ya mike tsaye yana qara dubanta da kyau hannun sa yakai zai share mata sai kawai yaga ta bude idon ta dakatawa yayi tare da maida hannunsa yadan ja baya kadan ganin irin kallon da take masa kamar ya sha bambam da sauran dan yanzu sosai ta tsare sa da idanunta shima kallon nata ya tsaya yanayi,
rufe idon tayi sai kuma taqara budewa juyawa taqara yi ta kalli gefen ta taqara juyowa ta kalli ɗayan gefen da aka daddaure mata hannu wani hawayen ne yaqara zubo mata,
kallon sa taqarayi tana so tayi magana amma takasa,
sukai wajen minti shabiyar ahaka batare da kowa yayi magana ba,

"INA ƊANA?
abun da yaji tace kenan da sauri ya juyo yana kallon ta da kayu tare da zaro kyawawan idonsa kana kallon sa zaka ga mamaki qarara a idon sa,
matsawa yaqarayi daf da ita dan atunanin sa ko kunnuwasa ne suka jiye masa ba daidai ba,

   "Ganin baiyi maga magana ba yasa tace ka kunce ni mainayi muku dan Allah,
saura qiris numfashin sa ya dauke jin abun da baitaba tunani ba baitaba tunanin wannan ranar ba wai matar nace take magana haka cike da nutsuwa kamar ba itaba,

kasa ko motsawa yayi saida taqara yimasa magana sannan yadawo hayyacin sa kamar marar laka ajikin sa haka yakai hannun sa ya kunceta kamar yanda tafada saidai yakasa iya yi mata magana,
"yana kunceta ta yunqura zata tashi amma taji ta kasa ganin hakan yasa shi taimaka ta tashi zaune zama tayi tare da dafe kanta da duka hannuwan ta biyu,
da kyar ya iya budar bakinsa yace mata sannu,
dagowa tayi ta kallesa batare da ta amsaba,
"bayan ta janye idon ta akansa ta shiga bin dakin da kallo sai kuma taqara juyowa ta kallesa,"inane nan kuma ina dana ina mijina da 'yan uwana  me nakeyi anan gurin kuma kai wane? shide shiru yayi yanajin yanda take jero masa tambayoyi batare da ta jira ya bata amsaba,,

"yanda take kallon sa tana jiran amsa daga garesa shima haka yake kallon ta yana tunanin amsar da zai bata dan baisan amsa ko ɗaya ba daga tambayoyin ta wata dabara ce ta fado masa sai kawai yace mata duk suna gida ke kuma baki da lafiya kin sumane shiyasa bakisan lokacin da aka kawo ki ba,
  "Amma kuma naga andaddaure ni me yasa aka daure ni ta tambayesa tana qara kallon sa,
ki kwantar da hankalin ki yanzu zankaiki gida idan munje zakiji komai ammade yanzu babu inda yake miki ciwo kina jin kwarin jikin ki kai ta daga masa kawai sannan tafara qoqarin zuro qafafunta daga kan gadon datake,
daram ta ajiye su aqasa tare da daidaita tsayuwar ta ta juyo ta dan kallesa sannan tace muje ka kaini gurin su inson ganin ƊANA,

  "shide anasa bangaren baisan wane irin tunanin zaiyiba koma sa ya tsaya yakasa gane shin farin ciki  zaiyi ganin ta dawo hayyacin ta  ko kuma damuwa zai shiga ganin irin tambayar da take masa da baisan ta yanda zai fara yi mata bayani ba gashi kuma yayi mata qarya yace tazo yakaita gurin su idan yake kuma taga bahaka ba to wani irin tashin hankalin zata iya shiga gashi baya son yagaya mata anan aganin sa gwara ummynsa tayi mata bayani bisa ga dukkan alamu ada duk bata cikin hayyacin ta batasan me takeba sai yanzu hankalin yadawo jikin ta tunda gashi har tana tambayar 'yan gidan su akaita wajen su,  "tabashin datayi ne yasashi dawowa daga duniyar tunanin da ya lula,
hannun sa ta kama tace muje mana inafa son ganin babyna nasan yanzu yana can yana ta kuka,

   Allah sarki cike da tausayin ta yake kallon ta  abun nata abun tausayi ita kanta bata san adadin shekarun da tayi a kwance ba har take tambayar danta da baby watakil yanzu in yana da rai ma yazama qato dashi gudun karta qara yi masa magana yasa shi kallon ta sannan yace to shikenan muje amma ki kwantar da hankalin ki danki yana nan cikin koshin lafiya ba abun da yasameshi yanzu hakama yana can yana wasan sa,

acewarta sai tace a'a baya wasa da kowa nasan yan can yana kuka wai nama kwana anan gurin tun yaushe aka kawoin nandin meyasa ma baku barsa anan ba nifa bana son arabani da dana koda yaushe so nake makasan ce tare tafada cikin murya me sanyi,
be qara yi mata magana yakama hannun ta saidai kuma sai yanzu taji qafarta tana dan yi mata nauyi kamar bazata iya takawa ba jin tana tafiya da kyar yasa shi dafata yace kibi ahankali jikin ki ba kwari sai ahankali zaki dawo daidai kai ta daga masa sannan itama ta dafashi tare da riqeshi yanda zataji dadin tafiya,
ahaka suka ringa takawa ahankali har suka zo bakin qofar fita sai wata mace ta kawo kai zata shiga ciki sukayi karo ahanya tsayawa tayi saurin yi tare da dan basu hanya sannan tace good morning sir bai kulata bare ya amsa mata gaisuwar tata gaba yayi ta bisa da kallon irin wannan wullakancin nasa tanama so tace wa me jiki ya jikinnata amma ba fuska dole ta hakura ta koma inda ta fito,

Ahankali suka cigaba da tafiya da kyar har sukakai wajen qofar sai ya zaunar da ita yace bari yakawo motar nan sai ta shiga,
bamusu tayi zamanta agun da yazaunar da ita dan daman ta gaji da tafiyar yana zuwa wajen motar driver yana gurin daman baibar wajen ba yana jiran fito warsa yana qarasowa da sauri ya bude masa qofa atunanin sa ko shiga zaiyi amma sai kawai yace masa key baigane me yake nufina sai yadan duburbuce alamun yana jiran qarin bayani amma yakasa tambaya,
Chapter 43 · 0% Book details