← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 139

Sashe 112

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda ya kirata ta juya tana kallon sa tare da amsa kiran da yayi masa, kafeta yayi da ido tare da takowa ahankali har yakaraso gabanta bai dauke idon sa ba daga kanta, sunan ta yakara kira still dai idonsa akanta ko kiftashi bayayi kuma ya hade fuska tamau kamar baisan wani abu aduniya ba wai shi murmushi ko kuma farin ciki haka ya koma mata,

cikin bacin rai yace "kina sane kika aikata wannan abun kuma kinsan da zaman sa meyasa baki taba gaya min ba daman duk abun da kike fada min ba gaskiya bane me yasa me yasa kika aikata haka da hannun ki kika raba da mahaifan sa kika kawosa nan aka dorasa akan zalintar mutane da cutar dasu yanzu da ban kiraki ba yakashe mahaifinsa da kansa kina tunanin iya shikadai za ayankewa hukun ci ke da kika rabasa dasu kuma kika sani baki sanar dashi ba hukuncin ki awajen ubangiji sai yafi nakowa kinsan gaskiya kuma kin take wannan wace irin rayuwa ce kika dorawa kanki nayi da nasanin kasancewa ta da agareki me yasa me yasa zaki aikata hakan amatsayin ki na musulma wannan wane irin mugunta ce wallahi bana ganin laifin kowa sama da naki kinfi kowa laifi aciki ahaka kuma kike cewa wai zaki tafi ki tafi ko ni da nake da awajen ki bazan bari kibar gurin nan ba batare da an hukuntaki daidai da abun da kika aikata ba yanda za a hukunta kowa kema dole ki tsaya ki karbi sakamakon ki duk da ke kika fallasa abun hakan bazai hana a hukun takiba,

wallahi bantaba tunanin zaki iya aikata haka ba nawa ake biyanki da har kikayi wannan danyen aikin umma? yayi maganar cike da bacin rai yana tsatstsareta da ido,

tunda yafara maganar hajiya sarah take zubar da hawaye yau wai yau dan cikinta ne yake gaya mata magana, tasan tabbas ta aikata kuskure amma shima baisan dalilin ta nayin hakan ba itama bada son ranta tayi ba dan ba yanda ta iyane shiyasa ta aikata hakan,

kamo hannun sa tayi tana kallon sa yayin da hawaye suka gama wanke mata fuska suna hada ido yajanye idon sa gefe ta budi bakima zatayi magana sai kawai ya dakatar da ita tare da kwace hannun sa daga nata hannun ya juya mata baya ya koma gurin baba tsugunnawa yayi ya kuncesa sannan yaje ya kunce Azeema ma sannan ya shiga basu hakuri,

yaudai yan masarauta sunga abun mamaki kuma sunji abun da basu taba tunanin ba basu taba kawowa ba kowa yana tsaye agun yana jiran yaji karshen zancen amma ba wanda yasamu damar yin magana saboda suna tsoron aji bakin ka agun yanzu wasu su sauke haushin su akansu shiyasa kowa yake zancen sa shikadai daga shi sai zuciyar sa amma kowa munafurci cinsa yake so yake yayi da dan uwansa amma ba dama dole sukayi shiru kowa ya zuba ido yana bawa idonsa abin ci,

abangaren fulani kam tunda hajiya sarah tayi magana takasa koda motsawa bare tasamu karfin halin yin magana agun saboda tasan karshen ta yazo tunda har ta riga ta fallasa shikenan komai ya karye kamar yanda bokan yace duk sanda aka samu wani ya fadawa akunne mutane da yawa sukaji tofa asirinta zai tonu kowa dawo gani daidai sannan papa ma bazai kara yarda da itama shima kuma zai dawo cikin hayyacin sa ta daina juyasa yanda take so ya daina yi mata biyyya kamar yanda yake mata abaya daga yanzu komai zai canza,

baba bakaramin mamaki yayi ba yanaso ya gasgata abun da suke fada amma yakasa gani yake duk kamar mafarki yake yaza ayi ace wai dan sarki guda shine dansa kai gaskiya wannan matar ba gaskiya ta fada ba idan hakane me yasa shi bai gane taba kuma dansa sa hannun sa ya binne sa ya riga da ya mutu kuma kawai kwatsam lokaci daya tawani zo tace wai dansane gaskiya karya take shi baida wani da araye bayan saleem da Azeema shikadai shima yake ta faman saka da warwarar sa,

abangaren Azeema kam tayi mamaki batayi mamaki ba domin tunda matar tace dan babane ta kura masa ido sosai taga kamannin sa da yan gidan su kuma ta yarda da yayan natane duk da ba ataba gaya mata suna da yayan da ya mutu ba amma aranar da ta fara ganin sa taga mugun kamar da suke da yayan ta saleem saida abun da yasa bata tada hankalin taba tayi tunani gizo yayi mata aranar ko kuma tsorone yasa taga kamar dasuke kuma tunda ga ranar bata kara ganin sa ba face to face kamar yanda ta gansa ranar shiyasa tayi watsi da maganar kamar da suke saboda bashi ya kawota ba daman khma basu kuma haduwa ta gansaba duk sanda zasu haduma kanta na kasa,

sarki da jikin sa yayi mugun sanyi saboda yagama yarda da maganar matar nan gaba daya saboda ya fahimci mahaifiyar sa fulani bata da gaskiya amma duk da haka bai gama tabbatar wa ba sai yakara samun hujjoji aransa yana ayyana mudun hakan ta kasance gaskiya bazai bar duk wanda ya rabasa da iyayen sa na gaskiya ba gashi ya kamo mahaifin sa da hannun sa yasa kuma an hukuntasa agaban sa da Allah bai rufa asiri ba da tuni ya kashe mahaufinsa da kansa ji yayi kansa gaba daya yadau wani irin matsanan cin ciwo shi kadai yasan halin da yake ciki ayau din nan,
ahankali yafara takawa har zuwa gaban baba ga mamakin mutane sai sukaga sarki sukutun da guda ya tsugunna agaban baba cikin kasa da murya yace "da gaske kaine mahaifina ?

kawar da kai baba yayi sannan yace "a'a ni banda wani da dana ya dade da mutuwa kai ba dana bane domin indai kai jini nane baza kataba zalintar mutane ba irin yanda kake dan haka bani da hadi dakai,

da sauri Azeema ta karaso wajen su sannan tace "baba wallahi da gaske ne wannan danka ne bakaga kamar da suke da yaya saleem ba Allah baba wannan matar da gaske take nifa tun ranar nafara ganin sa naga yana kama da yaya saleem kodai baka gane kamannin nasaba, ko kallon inda take baba baiyiba kuma bai kalli sarkin ba ya kawar da kansa gefe kawai,

jin batunsa yasa sarki mikewa tsaye jikin sa babu kwari dan yaji ajikin sa duk yanda akayi da gaske shine mahaifinsa kuma ya tuna lokacin da yazo wucewa yarinya takira saleem da karfi sai yanzu da tafada ya tuna lokacin da ta taba fadadin hakan kuma yakara tabbatar masa da zancen da ake gaskiya ne ahankali ya dora hannu akansa zai fara warware rawani kansa yaji anyi saurin rike masa hannu, hannu ya shiga bi da kallo har zuwa fuskar me rike masa hannun idon sane suka sauka akan Ammah da zuwan ta cikin gurin kenan,

zaiyi magana kenan ta kar kada masa kai ma'ana kar yayi magana kallon yan gurin tayi sannan ta daga murya tace "kowa yakama gabansa banason ganin kowa anan sum sum sum suka fara watsewa daga gurin har suka tafi gaba daya amma wasu ba haka suka so ba sunso har sai sunga karshen komai anyi agaban su,

cikin bacin rai Ammah tace "yanzu meye hakan kukazo kukeyi agaban mutane koma me yafaru ai baikamata ace kun tsaya gaban mutane bayi kuna kace nace agaban su suna jin sirrinku wannan abun da kukayi babu abun zai jawo sai zubewar mutuncin masarauta da rage mata kima da martaba da mutunci wannan abun da kukayi kwata kwata bai dace ba bai kamata ba da girman ku sai kace wasu kana nun yara kuna kallon sa amatsayin sa na sariki yana niyar kunce sarautar sa abainar jama'a koma meye ai a kunceta cikin mutunta da martaba wallahi kun batan rai kun ban kunya ni duk bansan meke faruwa ba sai yanzu aka sanar dani da ban bari hakan ta faru ba da tun wuri na dakatar da komai haba dan Allah sai kace wadanda basa tunani,,
maida dubanta tayi ga fulani da ta sunkuyar da kai sannan tace "wlh ni duk laifinki ma nafi gani da kika kasa
dakatar da abun har takai ga haka ya kuke abu kamar ba manya agidan me yasa ba asanar da papa ba tun wuri ko waziri ko galadima idan kin kasa su ai duk zasu iya ji da komai tunda su mazane idan ke abun yafi karfin ki duk da kina da ikon fada aji amma kika kasa yin hakan,

sosai Ammah ta rufe ido ta hausu da fada babu wanda batayiwa fada ba acikin su sannan tace kowa ya tafi makoncin sa gobe da safe za ahadu afada kuma kada wanda yayi gangancin tafiya daga cikwa harda hajiya sarah,

sannan Ammah tace baba shima ya koma dakin sa shi da hamza gobe za anemesu Azeema kuma ta koma part dinta kartaje part din fulani inyaso ita kuma fulani su tafi da hajiya sarah tunda kawar tace suje su cinye kansu ko kuma su san yanda zasuyu su samowa kansu mafita kafin safiya ba yanda suka iya yau Ammah ita ta koma mai juya kowa har fulani yau bata da wani ikon fada aji dole tabi yanda akace saboda gudun abun da ka iya faruwa nan gaba ji take dama idan ta koma part dinta Allah ya dauki ranta shikenan basai anyi zaman da ita ba da wane idon zata kalli sauran mutane idan maganar nan tagama karade ko ina tasan da kyar idan baza akoreta daga masarautar ba korar ta da za ayi shine babban abun da yafi daga mata hankali ahaka tana tunani bata iya cewa komai ba ta juya tafara tafiya dan bata da bakin magana ahalin yanzu tana tafiya hajiya sarah tabi bayanta da sake sake itama fal acikin ta,,

baba shima saida taimakon hamza ya iya mikewa daga gurin sannan yatai makasa suka tafi nasu wajen,

Ammah da kanta taja sarki takaisa har part dinsa sannan ta gargadi matansa da su bashi kulawa,

sannan ta juya zatabar falon ita da Azeema yayi saurin dakatar da ita,

tsayawa tayi tare da juyawa ta kalle sa da kyar ya iya budar baki yace "ki barta awajena,
Chapter 112 · 0% Book details