← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 139

Sashe 104

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan duk sundawo sun zauna dadda tana so tayi magana akan Meer amma takasa saboda taga ba kalar tabane tunda tazo bai kalli inda take ba kuma taga babu wanda yayi masa magana dan haka tayi tunani ma ko sojane shi idan yana abu ba tanka masa shiyasa iyayen sama suka kasa yi masa magana, ina ga ita kuma taje tayi masa magana ya zuciya ya harbeta agun bada itaba wannan kasadar shiyasa taja bakin ta tayi shiru amma duk da haka akai akai sai taɗan saci kallon sa ta gefe cikin rashin sa'a tayi masa wani kallo shima loƙacin ya ɗago jajayen idon sa suka haɗa ido da sauri ta kawar da idon ta tana tsoron Allah yasadai kar yace ta fito tundaga loƙacin bata ƙara gigin kallon inda yake ba ta maida hankalin ga hirar da akeyi acikin mutane tabar batun wancen me zubin yahudawan,

sam dai yakasa yin sukuni agurin saboda tunda yaji an ambaci masarauta kuma baiji masarautar inba hankalin sa yaƙi kwanciya dan yana tsoron yaji ance masarautar suce akayi wannan zalincin duk da inma hakan ta kasance akwai wacce yake zargi daman aikwa idan yakasance gaskiya masarautar su ake nufi ai kai tsaye ita zasu damƙa basai sunjira wani dogon bincike ba,

bossay ne yaƙara inda suke su biyu shima ya zauna akusa dasu tunda sauran ma duk suna surutu dan haka ba lalle aji maganar da zaiyi ba,

kusa da kunnen sameer yakai bakin sa yace wai ya banga kana farin ciki ba kamata yayi kaima ka shiga cikin su nanfa duk ƴan uwanka ne wacen sojan ma dakukayi dambe ashe faɗan ƴan uwantakane,

gabansa yaji ya faɗi yace wai kana nufin wannan labarin da masarautar mu yafaru wannan matar papa ce,
bossay yace eh mana kai alabarin bama ka fahimci inda ake nufiba kenan kamanta loƙacin da muka haɗu dasu har na cemuku suna kama da Ameesha kace zaka tambayar mana kakan ka ko yasan ta ashema matar sace da ka tambaye da kaji me zaice,

Shettima yace "kai to ai koni ban fahimci komai ba sai yanzu daka faɗa kumafa ka kallesa ka kallesu sai yanzu naga suna kama da wancen yafaɗa yana kallon inda Meer yake caraf suka haɗa ido ashe duk abun da suke idon sa akan su shi da yariga yasan komai akansu yasan ƴan uwane amma baijin zai iya karɓarsu amatsayin ƴan uwa dan har yanzu haushin sam yakeji da yasa ta dalilin sa mahaifin sa yayi masa abun da yafi tsana aduniya mari dan haka sai yarama akansa zaiji daɗi aransa kuma bazai taɓa kallon sa amatsayin ɗan uwaba,

suna haɗa ido da shettima Meer yace"uban me kuke cewa anan kun haɗa kai kuna munafurcin mutane harda magana ƙasa ƙasa munafukai kawai sai nayi maganin ku dukan ku duk ɗagowa sukayi suka kalle harda su maama kallon sa sukayi saidai kuma idan ka kalli bakinsa sai ka rantse bashi yayi maganar ba saboda yana gama faɗar abun da zaice yamayar da bakinsa yanda yake,

maama ce ta girgiza kai bata yi masa magana ba kawai ta mayar dakanta kan su sam da hannu tayi masa alamar yazo,

jiki babu kwari yatashi yafara takawa har zuwa inda take zai tsugunna agabanta kenan tayi saurin saka hannu ta ɗagosa tare da rungume sa tace kasan ko ni wacece shine yanzu ma bazaka gaida niba  ni daman nasan taurin kan nan ba abanzaba na gwaggwo ne shiyasa ranar tun kan naga kamannin ka nagane halayen ka shiyasa ma na tsawatar maka danaga zaka yimin rashin kunya,

"kai ɗan waye acikin gidan dan nasandai ba kai ba ɗan sarki Muhammadu bane, saidai jika,

kansa asunkuye dan gaba ɗaya jikin sa yagama mutuwa kunya da nauyin matar duk sun mamaye sa yayi dana sanin abun da yayi musu ahanya baisan haka abun zaije yadawo ba gashi yanzu shike da kunyar abun,

ahankali yace "eh ni jikan sane kuma jikan ɗa ga munbiya itace mahaifiyata,

Masha Allah kai jikan Sa'adatu ne kenan Allah sarki matar nan akwai mutunci munyi zaman amana da ita  tana nan lafiya dai ko,

"Eh" kawai ya iya ce mata

ita kuma taƙara ce masa ina maryama itama tana nan ko,

Eh yace maimakon ya kalli ta sai kawai ya gun da dadda take duk da halin da yake ciki saura kaɗan yasaki murmushi sannan yace ai da itama sukayi faɗa da wannan tsohuwar ya nuna dadda,

kai kai maryaman ce take faɗa da wani ammadai to saidai idan ƙarshe ta kaita matar da take da haƙuri tunda muke bantaɓa jin ta ɗaga murya ga wani ba gaskiya saida idan ƙarshe aka kaita,

ai kafin ma sameer yabata amsa dadda tayi saurin karɓe maganar da cewa wanna shegiyar matar ce ba ruwan ta to kwa saidai idan sanin da kikayi mata dan nidai akamannin ta banga haƙuri akan fuskarta ba ko kaɗan baya dashi da wani kanta kamar murhun giya,

wai daman inda naje ne nanne masarautar da kuke magana akai ai bansani ba sai yanzu muna da alaƙa da cikin gidan ai zama bai kama muba yakamata kutaso yanzu muje gidan ko,

maama ce ta ɗanyi murmushi sannan tace a'a bayan zuba sai mun fara bincike domin mugayen acikin gidan suke kuma bamu san suwaye ba dan haka muke so sai mun fara samun hujjoji tukun zamu je yanda muna zuwa muna da hujjar da zamu kama duk me hannu aciki yanzu daman waɗannan muke jira suzo su gaya mana abinciken da suka fara me suka gano tafaɗa tana kallo sam da yake zaune agaban ta,

kai kai waɗannan mutanen saidai Allah yasaka muku dan sunriga da suncuce ku saidai muce   Allah ya isa tsakanin mu dasu mugaye azzalumai in Allah ya yarda sai Allah ya toni asirin su kuma ba wani ɗaga ƙafa da za'ayi wai sa anfara bincike wannan maganar ma ku manta da ita dole daga yau zuwa gobe ahaɗu amasarautar idan kuna nan taya zaku gane mugayen ai zuwan musu za ayi kai tsaye inyaso daga baya ayi binciken acikin gidan wannan shine babbar masalaha dan wallahi muna nan bata yanda za ayi agano su waye saboda ba ƙaramin shiri sukai ba ƙananun mugaye bane tsaf yanzu kina nan ke baki gano suwaye ba su su ganoki suƙara rabaki da gidan ko su salwantar da rayuwar ku gaba ɗaya tunda har suka koreku daga gidan baza su taɓa bari ku koma cikin gidan Indai suka gano kuna raye nidai anawa ganin gwanda kawai aje musu zuwan bazata atayar musu da hankali mukuma anan zamu zuba ido akan kowa mugane take taken marassa gaskiya sai mu maida hankalin mu kansu duk wani motsinsu yazamana akan idon mu zasuna gudanar dashi daganan har loƙacin da zamu kama mutum dumu dumu sai mukamasa da hujja ina ganin hakan sai yafi mana sauƙi kuma tahakane zamuyi saurin gano su,

"Good thinking 👍,

suka jiyo muryar Meer yace,

sai yanzu ya matso kusa dasu sannan ya shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya tare da cewa "wannan tunani ne me kyau hakan yakamata ayi idan kun ɗauki shawarar tafa amma idan ma kuma baku ɗauka ba da banyi niyar sanar daku ba amma yanzu zan gaya muku ko bakujeba ko ninikaɗai me sai naje kuma ayu ɗinnan dan bazan iya barin abun araina ba ace anzalin ce ku kuma kunsan ko su suwaye kuma kunsan har cikin gidan da abun yafaru shekara da shekaru maama ba kya cikin gidan kuma ace ayanzu kindawo hayyacin ki kindawo cikin garin kuma zaki wani zauna aɓoye awani wajen inkikai hakan kina tsoron suma ai tun yanzu yakamata ayi duk abun da za ayi dan banga amfanin yin wani bincike wai abayan idon su abun da wannan matar ta faɗa shine gaskiya nafaɗa muku hakan bawai dan dole sai kunjeba amma nidai yazamemun dole inje kuma inna je zan iyayin abun da ba daidai ba dan zan kama duk wanda yazo hannu na da mai gaskiya da marar gaskiya sannan kuma zan sanar dasu ko ni wane agurin su.......

maama ce ta shiga tafa hannun tace maganar ku gaskiya ce nima na goyi bayan hakan amma ba yau za ajeba mubari sai gobe sai muhaɗu gaba ɗayan mu muje kaima kayi haƙuri kar kace zakaje yau kabari muje tare gobe gaba ɗayan mu,

maƙe kafaɗar sa yayi tare da taɓe baki irin duk yanda kukayi tundaga nan bai ƙara cewa komai ba nan dai suka cigaba da tattaunawa atsakanin su daga ƙarshe su maama sukace zasu koma gida inyaso gobe idan za atafi sai ahaɗu har su Ammi aje gaba ɗaya,
gaba ɗaya sukayi na'am da wannan shawarar akan goben za ahaɗu,

amma fa da jikata zamu tafi dan bazan iya tafiya inbarta ba, tayi maganar tana kiran Ameesha tazo zuwa tayi gabanta sannan ta riƙo hannun ta tace ai zaki bini ko..?

kai ta ɗaga mata tana murmushi,

dadda tayi saurin cewa au yau baya za anuna min shalele na tafiya zakiyi kibarni bayan kinsan nima na daɗai banganki ba ina buƙatar ki kusa dani na daɗe banji ɗumin kiba akusa dani kizauna tare dani tunda gobe zaku haɗu kinji,

Ameesha ce ta kalle ta tace dadda kefa mundaɗe tare dake ita kuma fa yau muka fara haɗuwa dan haka nidai ita zanbi ida kuma baza ki iyaba sai kizo mutafi tare kawai muje can mukwana amma ni bazan zauna ba anan ai komai yana son canji dan haka na canzaki kema tayi maganar tana yiwa dadda gwalo,

dadda ta riƙe baki tace au haka kikace ko to jiki adawo lafiya tsohuwar zuma ai da ita ake magani zaki dawo kisame nine duk inda kikaje, loƙacin kuma nima na daɗai da canzawa zan canza jika ne danma jikan todai bari inyi shiru dana ce wani abu amma dai shirun yafimin alkhairi,

dariya wasu suka sa mata saboda sun gano ta jikan da take nufi Meer ne shikuma bataga fuska ba shiyasa tayi wannan furucin,

Ameesha ma tagane ta dan haka tayi dariya itama sannan tace duk inda zakije ki ɗauko baza ki taɓa jin daɗin zama dashi ba, au🤭 namanta ashefa baki faɗi jikan namiji ne ko mace bamu san wanda kike nufi ba,
Chapter 104 · 0% Book details