← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 139

Sashe 93

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuka tashigayi masa tana roƙonsa tana ƙoƙarin kwace jikinta amma ya hanata damar yin hakan,

da ƙarfi fulani ta turo ƙofar ta shiga ciki,

kitchen ɗin ta shiga bi da kallo sai ta juyo ta kalli me aikin da alamar tambaya a cikin idon ta,

kafeta da ido Fulani tayi kafin tace ya banga kowaba kinsande babu abun da nafi tsana arayuwa ta kamar ƙarya baki tabbatar ba kikaje kika taso ni har inda nake

  girgiza kai tana cewa wallahi ba ƙarya nake ba ta faɗa tana  bin kitchen ɗin da kallo tana inda inda tace wallahi Allah anan nabarsu dakansa ya koreni daga ciki itama kuma tana ciki ya rufe ƙofar tayi maganar tana rarraba ido da tunanin to ina suka tafi sunsa taji kunya  ance ƙarya take,

wallahi saidai idan ɓuya sukayi amma suna cikin nan gurin ni nasan basu fita ba bari induba ko ina suna cikin nan ba inda sukaje,

"kin tabbata suna cikin nan?
"eh wallahi"

su Azeema dake laɓe abayan ƙofar store  ɗin kayan abinci dake kitchen ɗin tunda sukaji muryar su dab da shigowa cikin kitchen ɗin yayi sauri yajata suka shige suka ɓuya, Azeema jin batun za afara dubawa ta tsure saura kaɗan ta saki fitsari jikin taba ɗaya ya ɗauki ɓari,

  ahankali yace "ke ki nutsu babu abun da zai faru baza sugan muba,

"Wallahi sai sun ganmu gashinan fa zasutaho wallahi duk kai kajamin nashiga uku jin zata tona musu asiri yayi saurin toshe mata baki da hannun sa shi ba tsoro yake jiba kawaide yasan idan aka gansu abun akanta zai ƙare kuma ya ƙudartu niyar wallahi sai yaci uban matar nan da taje ta faɗa ma fulani gobe ma idan akace taje tayi munafurci bazata yiba ko aiken ta akayi bazata faɗa ba,

ɗan ɗaga murya Fulani tayi tace "tunkan ku wahalar dani wajen neman ku inkunsan kuna ciki kuyi gaggawar fitowa ku amsa laifin ku idan kuma ba hakaba kuka bari na nemoku da kaina to bazakuji da daɗi ba nagaya muku,

sosai Azeema ta ƙara tsurewa ƙafafun ta har suna karkarwa zasu kasa ɗaukan ta sanin halin ta kuma tasan tabbas aka duba sai ankama su,kuma abun da tafaɗa sai ta tabbatar dashi musamman ita dan tasan ba lalle shi a hukuntashi ba kamar yanda za a hukun tata,

dan haka tunkan ake ga nemosun ta yanke shawarar tayi magana kawai aji inda suke wataƙil idan tayi haka hukuncin yazo mata da sauƙi kamar yanda taji fulanin ta faɗa,

dan haka ta buɗe baki zatayi magana tunkan ta idasa buɗe bakin shettima da ya fuskanci abun da take shirin yi,shima atsorace yayi saurin ɗora bakin sa akan nata dan ya hanata damar yin maganar...
zaro ido tayi aranta tana ayyana lalle wannan mutumin bashida saiti su da suke cikin wannan halin na tsaka me wuya amma yakeso yaƙara jawo musu wani laifin yanzu idan aka gansu ahaka da da wane ido zata kalli mutane,

ƙoƙarin ƙwace kanta tafarayi ya riƙeta sosai gudun kar ta tona musu asiri shi kansa zaiji kunya idan hakan ta faru.......,

me aikin ce ta fara takawa taje ta leƙa wani lungu dake gefe can kitchen ɗin sannan ta leƙa ta ƙofar waje ko zata gansu amma bata gansu ba,

Fulani kuma ta shiga takawa zuwa ɓangaren store ɗin tana zuwa ta tura ƙofar store ɗin tare da saka ƙafar ta ɗaya aciki......😜😜😜

Kai wannan page ɗin akwai yawa nasan kowa saida yagaji da karanwa 😬 ku jinjina min

                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[7/8, 9:24 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 84

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

____HAMZA___

tun loƙacin da yataho ruwa na dukansa ya ƙarasa ɓangaren su ɗakin su yashiga yana shiga ya tadda baba azaune wajen sa yaje ya tsugunna duk da kayansa sunjiƙe amma hakan baidamesa ba burinsa kawai ya bawa baba labari,

gyara zama yayi yana washe baki kamar gonar auduga yace "baba albashirin ka?

baba shima yana kallon sa da ƴar fara'ar sa akan fuskart yace "goro"

"baba yau munyi magana da ita har waje tafito wannan ruwanne ya hanamu yin soyayya amma de nace mata zan koma idan ya ɗauke kuma tace to sannan kuma na sanar mata dakai zaku gaisa ɗin anjima ta amince,

sosai baba yanuna masa jin daɗin sa akan nasarar da yayi yau,

  ,"gaskiya nataya ka murna Allah yasanya alkhairi Allah yasa matar kace yanda kake sonta Allah yasa itama tasoka,

  "Ameen' Ameen" baba Allah ya amsa ,

ince dai ba dole kayi mata ba ya akai ma ta amince dakai yanzu bayan kace koda yaushe wulaƙantaka take?

hmmm baba bawa ai ba a cewa komai kaide kawai kacigaba da tayani addu'a amma yau ai har marin da ba ayi min ranar nanba shi aka sauke min yau,

"mari fa Allah dagaske kake wai mace ce ta mareka lalle so ba abun da bayasawa nikam dole inga wannan yarinyar da takeyi maka abun da kaga dama kuma karabu da ita lalle ta ciri tuta jarumi guda irin ka ta ɗaga hannu ta mare ka?

"hmmm baba abar maganar kawai nidai yanzu ka shirya anjima da yamma zamu ƙara komawa,

"to Allah yakaimu ammade wannan abu yaban mamaki wallahi mari tabb,

"baba dan Allah kabar maganar nan wai sai nanatawa kake ni banɗauke sa komai ba dan ko zafima banji ba,

burina kawai ta kulani kuma ta kulani naji daɗi kuma anjima ma zata kulani,
bai basa labarin yanda sukayi da fulani ba,

"baba yace "natayaka murna sosai  Allah yakaimu jimawar da rai da lafiya,

"yauwa baba Ameen abun da nakeso inji kace kenan,

tashi yayi daga gurin ya hau cire kayan jikin sa sannan ya canza wasu busassun yayi kwanciyar sa yana ta tunanin yanda sukayi da fulani shikenan yasan yanzu duk sanda yake buƙatar ta zai ganta akoda yaushe wayyo daɗi zai ringa kasancewa da ita koda yaushe,

baba na kallon sa duk abun da yakeyi amma saidai kawai yayi murmushi yana jinjina irin son nan da yakewa yarinyar nan abun har mamaki yake basa........

  'Fulani  kuma ta shiga takawa zuwa ɓangaren store ɗin tana zuwa ta tura ƙofar store ɗin tare da saka ƙafar ta ɗaya aciki......✍️

da sauri me aikin nata ta taho dan itama ta leƙa saidai cikin rashin kula tabi ta wajen sa Azeema take wanke wanke kuma ta zubar da ruwa agun dan haka tana takawa ta ta zame ta faɗi ji kake timmm ƙatuwar mata aƙasa ta faɗi da bombom ɗin ta tayi zaman dirshen agun, ihu tasaki me ƙara sakamakon zafin da taji abombom ɗin nata,

hakan da tayi ya dakatar da fulani daga ƙoƙarin shiga store ɗin datake ta juyo dan ganin abun da ke faruwa,

azaune ta ganta tayi zaman dirshen tana wurwur ga ido kamar na mujiya,

fulani tace "me yasameki kikewa mutane irin wannan ihun? haba murja sai kace wata ƙaramar yarinyar... kinsan dai bana son haniya da yawa bare kuma aringayi min ihu aguri,

"fɗuwa nayi  nataho da sauri  ban kula da ruwan ba na zame,

  fulani tace to ai sai kitashi tunda ba wani ya yarda keba gobe idan kin taho sai kiringa kallon gabank......

bata ƙarasa ba sakamakon jin ringing ɗin wayar ta dake hannun ta yasata katse maganar da takeyi,

duba wayar tayi dan ganin me kira da sauri ta ɗaga kiran saboda daman shi take jiran  tsammani tunɗazu,

tana ɗagawa tayi saurin ficewa daga kitchen ɗin har tana haɗawa da ƴar sarsarfar ta gurin yin sauri,

taƙaicine ya ishi murja yanzu ta faɗi maimakon tayi mata sannu amma saima faɗa da zata hauta dashi sannan kuma tayi ficewar ta saboda bata da tausayi, da ƙyar ta iya yunƙurawa ta miƙe tsayi azaba tasama ta manta da waɗanda take nema daman ta gama girkin da takeyi jerasu yarage dan haka kawai itama tafita daga kitchen ɗin dan sai taje tayi jinya kafin ta iya ci-gaba da aikin.....

duk abun dake faruwa akan kunnen su Azeema dan haka suna jin fitar su Azeema tafara ƙoƙarin ƙwace kanta sakin ta yayi yana kallon ta itama shi take kallo sai tayi saurin janyewa saboda hakannan sai tafara jin kunyar abun da yayi mata yana ganin haka yasaki kayataccen murmushi sannan yace ,"matsoraciya kawai daman haka kike da tsoro to wallahi ki rage tsoro,

bata ce masa komai ba ta ɗago ido ta hararesa tare da cewa ni matsamin in wuce wallahi kar ka ƙara zuwa inda nake bazakajamin bala'i ba ina zaman zamana inji da abun da yake damuna ma basai ka ƙara da naka ba,

"au hakama zakice ko danma kinsamu na taimakeki shine kuma yanzu zaki min rashin kunya to wallahi inbaki bini ahankali ba sai in ƙara wani yanzu kuma inbari har sai kowa yazo ya ganmu ahaka ana tambaya kuma ince ke kika jawo ni,

"inbaka fasaba dake su basu da hankali sai su yarda dani najawo ka ƙarfinka nafi da zan iya jawo ka kuma ka biyo ni ai duk wanda ma kagayawa wannan abun babu wanda zai yarda dakai saboda wannan ai maganace da ba wanda zai yarda,

"haka kika ce to bari inyi sai mugani,

"wai me zaka ƙara yi?

kashe mata ido ɗaya yayi yace "shan sweet sweet ɗin nan akwai daɗi yafaɗa yana ɗora hannun sa akan lip ɗin na ƙasa yaɗan shafa shi,

wani irin yam taji jikin ta yayi mata da sauri ta kai masa duka a hannun tanaso tayi magana amma takasa sai faman hararar sa take kamar idon ta zai faɗo,

dariya yayi kawai tare da cewa "kinaso kina kaiwa kasuwa ko to shikenan zo ki wuce kar na ɗora ki akan network dan naga kina niyar hawa,
Chapter 93 · 0% Book details