← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 139

Sashe 82

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sauran gurin ta kamo ta ɗaga shi ahankali sannan ta kwanta tare da juya masa baya abun rufar ne baigama rufe ta ba sai ta ƙara matsawa kusa dashi sosai har bombom ɗin ta na ɗan gogar jikin sa saida ta tabbatar ko ina ya rufu sanann ta rufe kanta tare da sauke ajiyar zuciya jin ɗumi yafara ratsata ai tuni ta ƙara lulawa duniyar bacci...........✍️✍️✍️

tofa wanga ɗiyafa zata jawowa kanta bala'i ke wa ga aike ki bakinsan yagama korankiba daga ɗakin amma shine harda hawar masa kan gado abun harda su cikin bargo🤔🤔🤔

                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[7/2, 8:56 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️77&78

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

             "ruwa ake sosai kamar da bakin kwarya,

yayin da bayin Allah biyun nan suke sharar baccin su hankali kwance tare da mannewa da juna batare da sanin su ba meer cikin bacci ya runggumo ta saboda duk atunanin sa filo ya rungume ita kuma batasan ma yana yiba baccin ta kawai take shara (daman kunsanta da bacci gashi kuma daman ta kwana batayi ba  ga lafiyayyen gado da bargo ga kuma dumin jikin sa ina ai tuni ta manta aduniyar da take hankali kwance take baccin hani'an sunkai wajen awa  daya suna bacci lakacin kuma ruwa yafara tsagaitawa,

ruwa na gama daukewa meer yafara juyi alamun zai tashi hannun sa yadago da niyar cire abun rufar daga kansa amma sai yaji hannun yayi masa nauyi alamun kamar andanne masa hannun ahankali ya shiga bude idon sa yana budewa kwa ya saukesu akanta da sauri yasake ta daga rikon da yayi mata saida hannu daya yasamu damar janyewa dayan kuma tana kai ta danne masa tsoro ne yakamasa lokaci guda jin mutum akusa dashi dan baigama ganin fuskar ko wacece ba kuma shi harga Allah yama manta da babun ta shiyasa bai kawota aransa,
tunani ya shiga yi waye akusa dashi rashin me basa amsa da ɗayan hannun ya ɗaga bargo ya buɗe su gaba ɗaya tsulum idonsa ya sauka akan fuskarta daman facing ɗin juna suke yi zaro dara daran idon sa yayi akan ta yana mamakin ganin ta kwance akusa dashi daman duk gargaɗin da yayi mata bataji ba bayan yace kar yatashi yaganta agidan ma gada ɗaya amma shine abunna ta har kan gadon sa kuma kusa dashi akan hannun sa wannan wacce irin yarinya ya haɗu da ita  anya ba mayya bace ko aljana daga haɗuwa tabi ta nace masa ta maƙale masa yau ya ɗebowa kansa bala'i,  

da ƙarfi yaja hannun sa da take kai zai janye amma ga mamakin sa sai kawai yaga ta riƙo hannun da sauri tare da kwantar da kanta akai taci gaba da baccin ta mamaki ne ya kuma cikashi dan atunanin sa tana sane take masa haka, tunanin abun da zai mata ya huce ya shiga yi dan haushin ta da yake ji yagama cika da taƙaicin ta,

meƙewa tsaye yayi tare da zare hannun sa da ƙarfi yana zarewa yaje wajen kayan sa cajar wayarsa ya ɗauko ya nannaɗeta yadawo inda take kwance sannan yaye bargon daga jikin ta yana yayewa yaga ta wani haɗe jikin ta waje ɗaya alamun sanyi take ji amma duk da haka bai tausaya mata ba ya shiga tsula mata ajiki da iya ƙarfin sa,

amugun razane ta miƙe zaune tare da fashewa da kuka me ƙarfi  baidaina ba kuma yaci gaba da zuba mata wayar cazar ta ko ina,

  sosai ta shiga rera masa kuka tana jawo bargon dan ta rufe jikin ta amma sa yasa ɗayan hannun ya janye yaci gaba saida ya tabbatar da ta daku sannan yace get out of my room before in canza miki kammani bance kar na tashi naganki acikin gidan nan ba shine harda hawar min kan gado uban wa yabaki izinin kwanciya kusa dani ya faɗa yana daka mata tsawa memakon ta tashin saita ƙara matsawa kusa da fuskar gadon tana kuka tana girgiza masa kai,

   "baza ki tashi kifitaba ina miki magana ƙin tashin tayi ta ƙara mannewa da bangon tana karkarwar jiki,

girgiza kansa yayi sannan yace wannan baki ɗaku bane jefar da cazar yayi yaje ya ɗauko ballet ɗin wandaon sa ya tunkaro ta tunda tagansa ta saki wani kukan me sauti tashiga basa haƙuri amma da tagade da gaske dukan nata zaiyi da sauri ta sauka daga kan gadon ta nufi hanyar ƙofa tana zuwa wajen ƙofar cikin rashin sa'a ta zame agun ta faɗi wata ra zananniyar ƙara tasaki sakamakon buguwar da ƙashin ƙafarta yayi da jikin ƙofar,

dafe kansa yayi tare da ajiye ballet akan gado ya nufo inda take tsayawa yayi akanta tare da buɗe ƙofar yace fita ihu gagara yi tana cewa wayyo ƙafata wayyo ƙafata ƙafata zata cire wayyo Allah na dadda ta fadada ƙafata,

tsugunnawa yayi zai fara janta ya fita da ita saiga Ummy ta shigo da saurin ta ganin su ahaka yasa tayi turus ta tsaya tana binsu da kallo dakatawa yayi da niyar fitar da ita ɗin ya miƙe tsaye yana kallon ummyn tasa,

da mamaki ummy tace hayatee me nake gani mace aɗakin ka me yafaru waya shigo da ita daga ina take tun ɗazu nakejin kukan mace na ɗauka ko maƙotane Saida nafito najide anan samane me ya haɗaka da ita me kuma kayi mata?

ummy wacce tambaya kike so in amsa miki kinbi sai jero min tambayoyi kike,

hararar sa tayi sannan tace duka zaka bani tana masa magana amma hankalin ta nakan Ameesha ganin de yarinyar da gaske take kuka kuma gashi ta riƙe ƙafarta sai tabawa ummy tausayi cike da tausayawa ummy ta tsugunna agaban tana yi mata sannu tare da kamo ƙafar taba ɗagata kwa taga ƙafar har ta kunbura sunnu tashiga yi mata sannan tace subhanallah garin ya akai haka ta faru ƙafar ai har tayi tsami gashi ta kunbua,

  cikin kuka Ameesha tace" faɗuwa nayi na bugu da ƙofar nan,

  "Ayya sorry amma garin ya akai kika faɗi har kikajawowa kanki wannan abun,

shiru tayi bata amsaba hakan yasa tagane meer ne sanadin faduwar tata waƙil biyo ta yayi da gudu,
amma de yanzu ba wannan loƙacin tambayar tata kamata yayi tafara bawa yarinyar taimako kafin kuma shi yaga mata inda yasamo ta,ajiye tunanin tayi ta maida dubanta ga Ameesha sannan tace bari ayi miki ruwan zafi zaki iya tashi?

kai ta girgiza mata alamar a'a,

miƙewa ummy tayi sannan ta dubesa duk yabi ya wani haɗe rai ya haɗe girar sama da ƙasa yana ciccin magani,

sai ka ɗaukota kafito da ita dan bana raba ɗayan biyun kaine sanadin faduwar tata kayi sauri ka sauko da ita bari in ɗora ruwan ɗumin tana faɗa tafara niyar fita daga ɗakin,

Meer yace ummy ki tafi da ita kawai ni bazan iya daukan ta ba bana son ganin ta dan Allah ta tafi tabar gidan nan kar ta bari in sauko inganta agidan nan wallahi sai kusa ɓaɓɓallata,

da mamakin furucin sa ma ummy ta tsaya tana kallon sa saida yagama sannan tace kamar ya ba fahimci maganar kaba ince bakai ka kawota kuma shine kake wa mutane wani zancen da ban dan bangane masa ba waye ya shigo da ita gidan,

cikin ɗan turo baki kamar wani ƙaramin yaro yace ummy nifa bansan taba nima ɗazu ne kawai dana  ɗan fita in zagaya garin na haɗu da ita yake ta tsokano ƴan iska sun biyo ta shine fa na taimaketa daganan kuma tanace min saida ta biyo ni har gida bayan mun shigo na ce mata tazo wajen ku tagaya muku amma shine da yake ita mayyace ina farkawa daga bacci naganta akusa dani shine......sai kuma yayi shiru.,

ummy tace shine kayi mata me ka daketa kuma ka biyo ta ko haka kake so kace mun ba,

kai me yasa baka da tausayi ban hanaka taba mace ba me yasa baka dauki mace da daraja ba yanzu kamar wannan yarinyar ma yar karama me tasani kamata yayi ai kajata ajiki kaji matsalarta tunda har kaganta cikin wannan halin ai kasan de ba dadi ne yafito da ita daga gida ba kasani ma ko bata da iyayen shiyasa ta nace maka tabiyo ka tunda taga ka taimaketa amma shine zakazo kasaka ta adaki ka daketa kuma kabiyota gashinan yanzu kaji mata ciwo watil kashin ta ya goce yar karamar yarinya itama sai ka nuna mata halin ka wannan ai abar a tausayawa ce amma kai bansan me mata sukayi maka ba da ka tsane su dan Allah na rokeka da Allah karage wannan halin karin ga jin tausayin mutane ko ba komai wannan yarinya ce inma zaka nuna tsanar taka ga wasu amma bai kamata ace har yara zaka ringayiwa haka ba ka can za hali dan Allah wallahi banason ganin kana irin wadannnan abubuwan bana jin dadi daman nice ma me biye maka kasan mahaifinka baya son irin wadannan abubuwan dan haka wallahi tun kan yafito yaji abun da ka aikata kayi sauri ka dauko ta muje agasa mata kafar ashafa mata man zafi idan kwa ba hakaba kasan halin sa sarai ni da kaina zanje in sanar dashi abun da kayi inbanda abunka ma kai da kayi aikin lada ka ceceta daga gurin su ai kamata yayi ka karasa ladan ka ni ko ni ka kawowa ita ai zamu kula da ita sannan muji daga inda take amma kazo ka lalata komai dole ma sai taji sauki kafin mahaifin ka yaganta dan in yaga kafarta haka kuma yaji kaine sila ranka sai ya baci,
Chapter 82 · 0% Book details