← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 139

Sashe 64

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

shettima ma yace zancen kenan nima nafi tunani ko haɗuwar wani gurin ce abu yashiga tsakanin su da yasa ta riƙeshi ko kuma soyayya kasan papa akwai ɗaukar wanka ga kyau inajin ko ya yaudare tane kode makaman ci haka,
"hararar sa sam yayi yace me kake nufi kenan kakan nawa kake cewa  mayaudari to kwa kamar a kunne sa kafaɗa dan sai nagaya masa,
"ɗan murmusawa shettima yayi yace to ai ba ƙarya nayi ba wallahi indai kaga mace tayi kuka ko ta shiga wani yanayi idan aka ambaci mutum to ya yaudare tane ko kuma tasoshi shikuma be sota ba tayi son maso wani daga baya kuma harta haƙura ta auri wani to sai kaga idan suka haɗu dashi ko kuma ƴaƴan sa kode wani abun da ya tuna musu dashi sai kaga sun tsinci kansu cikin wannan halin....

"Sameer yace to nide bansanu ba zan tambaye sa inji idan yasanta zai gaya mana inda take daga nan kuma sai munemi yanda zamuyi idan tana da amfani sai mune meta idan kuma munga ba abun da muke tunani bane akanta kawai sai murabu da ita kawai muyi focusing ɗin abun da ke gaban mu,

  bossay dake baya yace to yanzu meye abun yi danni yanzu hankalina ma gaba ɗaya ya tafi kan waccen matar dan gaba ɗaya tafara canzan tunani
yakamata muyi nazari akanta sosai wannan abun yana buƙatar tunani da dogon nazari  amma de Ubangiji shi yabarwa kansa sani shiyasa ya haɗamu da su kuma muka rabu dasu akwai abun dazai faru watakil rabuwar ce mafi alkhairi shiyasa muka rabu batare da munji wani ƙarin bayani ba sai yazamana kamar ansaka mu cikin duhu da wani tunani amma de kuma idan muka ƙara nazarin faruwar wannan abun da haɗuwar tamu zamu fahimci kamar wani ƙarin haske ne Allah ya nuna mana a binciken da zamuyi ina ganin ayanzu idan muka samu matar nan akusa damu zamu samo bakin zaren wani abun, ɗan dakatawa yayi da maganar sannan yace ko ya kukace maganata abar dubawace kuyi tunani akai sosai zaku gane abun da nake nufi amma fa ni anawa ganin kenan da kuma hasashen da nakeyi wannan matar itace muƙullin wata ƙofar tamu wanda saida ita zamu shiga wani wajen.... shiru yayi yana jiran jin ra'ayoyinsu game da bayanin da yayi musu,

   "shiru motar ta ɗauka gaba ɗaya kamar babu kowa acikin motar,

  sam ne ya katse musu shirun da cewa  "zamu duba maganar ka amma sai mun samu loƙaci sai muƙara tattaunawa akai amma saima na tambayi papa abun da yace duk saimu tattara maganganun muga inda kuma yakamata mu dosa....

    shettima yace hakan yayi kaga loƙacin komai zai fara tafiya bayan munɗauko wannan mutumin shima kuma awajen sa zamu samu ƙarin baya ni duk sai mu haɗa su waje ɗaya,
to hakan ma da kukace yayi Allah ya dafamana ya shige mana gaba akan abun da mukasa gaba Allah ya taimakekum da tai makon sa yabamu ikon cika alkawarin da muka daukar wa kanmu,  

    "Ameen!"
suka amsa masa dashi gabaɗayan su.,

    daga nan ba wanda yaƙara magana Sameer ya tayar da motar suka juya saboda daman banan hanyar zasuyo ba unguwar da mahaifin sumy ya kwanta ta musu suka nufa tunda suka fara tafiya bawanda yaƙara magana saidai kowa yana tasa maganar da zuciyar sa kowa na saƙa da warwara shi kaɗai.............,

      *maama*

  "dan Allah maama kiyi haƙuri kiyi shiru  wallahi muma zaki iya saka mu kukan ummy ce me maganar muryarta cike da damuwa take bawa maama haƙuri da tunda suka baro wajen ta fashe musu da kuka kuma tambayar duniya sunyi mata akan tafaɗa musu dalilin kukan nata amma taƙi buɗa bakin ta sai kuka kawai harda me sauti  take duk tabi tasaka su a damuwa(daman idan babba yana kuka ai kaima dole kaji kamar kayi kukan nidai saida nayi ma😭, wallahi koya kaga nagaba da kai na kuka saikaji jikinka duk yayi sanyi😢😢)

     "da ƙyar suka samu ta ɗan tsagaita kukan nata baya fita sosai yanzu ahaka suka ciga ba da tafiya ba wanda yaƙara magana suna so su tambayeta amma suna tsoron kar su tsokano ta taci ga ba daga inda ta tsaya shiyasa kawai suka rabu da ita suka bari idan sun sauka ta dawo daidai sai su ƙara tambayar ta........

          ************************

                *Masarauta*

__________cikin fada.

     Sarki ne akan ƙasaitacciyar kujerar sa ta mulki wacce aka ƙawata ta da ado kala kala na sarauta ajiki kana kani kasan ba ƙaramin kuɗi aka kashe mata ba wajen ƙawatata iya adon ma da aka yi ado dashi wasu maƙudan kuɗaɗen aka kashe mata ba,

    gefen kujerar sa kuma Fulani ce itama a hakinmce akan tata kujerar sai wata kujerar daga can gefen ta papa ne da Ammah a azaune suma atasu kujerar da batakai ta fulani ƙawatatuwa ba,

    ƙasa kuma su waziri ne da galadi ma da sauran de duk wanda yadace nakusa kusa de duk de ajali ne awajen amma banda yara dan ko su momma babu su aciki iya manyane kawai agun,

waziri ne ya fara ɓude taro da addu'a dayiwa annabi salati kamar yanda yake a addinan ce idan za ayi taro ya wuce mutum biyu zuwa sama anaso kafin afara maganar sai abuɗe zaman da addu'a,
"bayan sunyi addu'ar ne"
"fulani ta gyara zama tare da bin kowa da ido saida ta gama shan ƙamshinta kamar yanda ta saba aduk loƙacin da taga kowa cewar ta yake jira to fa anan ƴan mulkin suke motsawa saitagama ja muku aji da ƙara ɓata muku rai sannan zata faɗa muku buƙatar ta, yanzu made hakan take bata canza zani ba saida tayi musu haka sannan ta fara magana,

"ƙara gyara zama tayi sannan tace tom duk danasan kowa yasan shine dalilin taruwar mu anan maganar da tasa nace kowa ya hallara anan kenan ina fatan kowa yana da masaniya akan abun da yafaru jiya ko? daga cikin mutanen wasu suka shiga jinjina kai alamar eh...
cigaba tayi da cewa jiya wajen yamma ansamu wani babba alamari da ya firgitar da al'umma ajiyan nayi tunanin gabaɗaya duniyar ce ko ince garin nema, saidaga baya kuma nakejin labarin wai iya cikin masarautar ne abun yafaru,
a gaskiya lamarin yayi matuƙar furgita ni yasakani aruɗu kuma yaban mamaki kai ba abunma da baibanba saboda al'amari wanda nide iya tasowa ta arayuwata bantaɓaji ba kuma bantaɓa gani ba abu kamar almara kamar a mafarki, shiyasa na taraku anan dan jin ta bakunan ko da wanda yake da masaniya da abun da yafaru domin wannan ba abun zama bane dole atashi tsaye dan magance gaba karmuje nan gaba muna ciki muji munkifa ankashe mu loƙacin mu beyi ba yakamata asan abunyi,
maganar ta saida tabasu dariya jin yanda ta tsorata kamar ba sarauniya fulani ba yau itace da tsoro ƙarara afuskarta kuma har wai su kifa ko wazai kifar dasu, dan haka saida wasu suka ɗan dara,
itama ɗan dan murmushi tayi tace kuna dariya Allah gaskiya nake faɗa wannan ba abun wasa bane maƙiya kuma meye bazasu iyaba muna zaman zaman mu sai kuga anyi abun da zai halakar da mu gaba ɗaya tunda suka fara da haka danni de wannan abun cewa zanyi turo mana akayi da ranar Allah amma gida yayi duhu ga ƙara yaseen wannan ƙarar turo mana akayi sufa maƙiya da mahassada ba abun da bazasu iyayiba, dan haka dole mutashi tsaye dan kare martabar masarautar mu da tsirar da rayukan mu,

"a'a wannan fa ba wani ture kar kuyiwa wani ƙazafi aradun Allah kuka shuka abunku kuma zaku girba ai ni ajikina wannan ƙarar wallahi domin wanna abun da yafaru ƙullallan makirci ne kawai na asiri shine ya warware saida kuma nima bazan muku ƙazafi ba akan kune saboda daman sarauta ta gaji haka mebi andaɗe da binne shi sai ajiyan Allah yayi kuncewar sa domin sarauta ce daɗaɗɗiya baza ace ga wanda yayi ba amma dole wannan abun karyewar wani asirin ne daman shi asiri ai haka yake akwai wanda in ya tashi karyewa har jijjiga guri yake ginin wani gurin ma zai iya faɗowa wannan ai yazo da sauƙi,
a zamanin mu meye ba magani, irin waɗan nan abubuwan ai tsohon abune awajen na wallahi bayau fara ji ba kuma nasan bayau zan gama jiba saboda wannan haline na mutane ga duk wani wanda ke zaune acikin masarauta sai yayi saidai wani yafi na wani muma da ba muyiba ai da ba mukai wannan loƙacin ba araye, in asirce asircen nanne ba wani ɓoye ɓoye kuma duk munyi saidai namu na hankali mukayi bare kuma ku da kullum kai ƙara buɗewa yake duniya ta zama abun da ta zama,
kuma kuma nasan kunyi kallon ku kawai nake ina kawar da kai duk wani mitsin mutum saidai inbeye agaban ido na ba amma yar nake kallon ku shiyasa ma zakuga bana shigowa saboda inna ce zan dawo nan to wallahi ruwa ma sai ya gagari wasu sha ajirayi ranar ƙin dillaci kuma ajuri zuwa rafi watarana tullun zai fashe ne........
Chapter 64 · 0% Book details