← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 139

Sashe 30

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"cike da mamaki baba yace daman kana da aure shine amma baka taba gayamin ba a ina matar take baba yafada cike da zumudin jin ta bakinsa ,
"dariya hamza yayi har kana iya ganin fararen haqoransa sannan yace baba naga har ka qagu kaji ko to nibanda aure kuma bantaba yiba yanzu de nakeson inje infara farautar samowa duk da bansan ina zangan taba amma koda tana wajen waccen wahalalliyar ne sai naje na nemota wauyar ta in fita amma ina fita zansan komai akanta " baba yace bakasan taba ma shine kakecewa matar ka a ina ka taba ganin ta? da har kake kiran ta da matarka?
" tsayuwa ya gyara sannan yace baba kasan ance so gamon jini akwai wanda kuna haduwa zaka ji ya kwanta maka to nima hakance ta faru dani, "kallo daya bisa qa ida naimata zuciyata sai ta kamu "
Wacce nace maka dazu tazo nemana tsohuwa ta aikota to ita zanje nema yarinyar tamin gashi kuma naga alamar ma bakuwace saboda bantaba ganinta ba sai yau kaga kwa dole inje injiyo news akanta,
saboda mamaki kwa baba yakasa cewa dashi komai saidaga baya "yace to Allah yabada sa'a nide ba ruwana aciki idan ka dawo kanufi dakin ka kar inji kar ingani sai komai ya daidaita ka rage neman fitina sai kadawo,

murmushi hamza yaqara saki tare da fadada fara'ar fuskarsa "yace baba wallahi ba inda zan koma ina nan idan nagama ganota ma harnan dakin zankawo ta itama daga qarshe innema mata 'yancin kanta tadena bautawa waccen matar,
"baba yace dawa zaku zauna saidai idan ni zanbarmuku dakin amma bada niba aciki,"kai baba wallahi kafiya tsoro kai da kake dani kuma meyasa zaka ringa tsoro ko yatsa wani yanuna maka saina karya masa yatsa dan haka kadena tada hankalin ka ka kwantar da hankalin ka kamar kayi bako ya mutu "kaga ni ka isheni da surutu tafi kaban wajen Allah ya tsare dan Allah tafi cewar baba yana magana yana nuna masa qofa,

kafada ya daga sama sanna yace ai ko baka koreni ba yanzu zantafi yafada yana nufar qofar fita tare da fara yin waqa.........

*Dakece zanyi wuff, zanyi wuff.....
Dakece zanyi wuuf zanyi wuuuf...
zanyi wuf.......
"Kece tawa innda rai da raboo... amanar zuciya kedamketa....*

Ahaka yayitayin waqarsa yana tafiya har yafice daga sashen su ya nufi cikin masarautar kai tsaye da shi kansa besan ta inda zai faraba neman taba.....😜😜😜😜🫣🫣,(Allah kutayani da addu'a kar mukai wajen shekara bamu gama ba, wlh yanzu banason yin typing ina farawa sai inji nagaji😂 bansan me yasaba yaseen gaba daya sai ahankali) pray for me ko zanringaji inayi dayawa batare da nagaji ba
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿27&28

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

    *__Bossay__*

    "bayan ya fito daga gida yashiga mota yabar gidan ransa yana danyi masa zafi saboda maganar auren nan da akayima sa shikadai yasan abun da yakeji,
aransa yana ayyaba irin abun da zaiyiwa wannan yarinyar bade tanace sai ta aure shiba kuma ta shiga tsakanin sa da mahaifinsa shine zata biyo masa ta wannan hanyaryasan halin mahaifinsa indai yace sai yayi abu to ba wanda ya isa yacanza masa ra'ayi dan haka. bashida wani abun cewa dole yayi hakuri yakarbi auren ta amatsayin qaddarar sa jiyake kamar yayi hauka afili ya furta duk ni najama kaina da tunfarko bance inason ta ba da shikenan amma yanzu gashi nan tazo ta zamemin qarfan qaya ana korarta tana qara naniqemin sai kace mayya mtsww ya buga tsaki kamar tana gurin,
ahaka yayi ta tafiya saida yaje wajen wata kwana bayan ya shiga layin sai yasamu gefen titi yayi parking a gefen hanyar sannan ya dauko wayarsa yayi kira ana dagawa yace yawwa na shigo layin ina zanyi ko intsaya kafito,
bansan me akace masa ba daga can bangaren kawaidai naji yace tom shikenan ganin nan zuwa kashe wayar yayi yana qara jan tsaki afili yake cewa yanzu dan rashin mutunci muyi wayar dakai zanzo amma ka wani ce min kuntafi asibiti cike da takaicin maganar da shettima ya gaya masa,
kwafa yayi  tare da tayar da  motar sa yayi rivers yaja motar sa ya nufi hospital din kai tsaye dan bazai iya hakuri ba tunda ya fito dan yaganta dole sai yaga hasken idanusa  zaiji dadi..

bewani bata lokaci ba ahanya sakamakon gudun da yake kwararawa adan qanqanen lokaci yaqarasa bayan yayi horn me gadi ya bude masa yashiha yayi parking a parking lot sannan ya fito ya shiga ciki kaitsaye ya nufi office din shettima tunda daman yasani kuma yana kyautata zaton dole suna can shiyasa be qara kiranshi ba ya nufi gurin,
"nocking yayi daga ciki akace masa "Come in" turawa yayi yashiga da sallama abakin sa, "amsa masa shettima yayi shikuma yaqarasa shiga ya zauna akan kujerar da take facing din shettima tare da miqa masa hannu suka gaisa yadan fara dube dube yana neman Ameesha dan murmushi shettima yayi yace neman ta kake ko dan sosa kai bossay yayi alamar yaji wani iri sakamakon kamansan da yayi,

"tana ciki bacci take cewar shettima "
joyowa yayi ya kalle sa "yace bacci kuma at this time?

"shettima yace eh mana ai ita yanzu   kasan ba daidai take da sauran mutane ba kwakwalwar ta tana bukatar hutu akoda yaushe anfiso ta ringa bacci yanda zatafi samun sauqi da wuri idan tension yayi mata yawa zata iya samun matsala wani lokutan taringa yin abubuwa kamar ba mai cikakken hankali ba,

"cike da gamsuwa da bayanin sa yadan jinjina kai yace ayya Allah sarki Allah ya qara mata lafiya wadanda kuma sukayi mata haka Allah yasaka mata Allah ya toni asirin su,
"shettima yace Ameen thumma Ameen yauwa bari na in tabo sam ingaya masa kana nan kaga sai mufara ma maganar yanzu tunda duk mun hadu sai asan abun yi yafada yana qoqarin dauko wayar sa yana danna wa sameer kira,
"bossay yace gaskiya de nima abun da nakeso ayi kenan wallahi naji shiru be nemeni ba har yanzu,

"shettima dake qoqarin kiran sam yadan dakata ya dago yana kallon bossay shima shi yake kallo,
   "Shettima yace ai inba kiransa nayi ba bazai taba kiranka ba bakasan me kayi masa ba ko ai sa'a ma kaci da yabarka haka ai kabata masa rai duk da kafi bata min raima amma ni nawa me sauqi ne shi sai yafini jin haushi saboda shi beda hakuri ko kadan nayima mamaki da har yayi wannan dadewar awajen batare da yataba lafiyar jikin ka ba,
dariya bossay yayi yace ai naga alama wayagaya maka be tabani ba saida yabani ajiyar mari ai tundaga nan nadan qara tsorata dashi ni nasan ma watakil ba wani girmemin yayi ba amma wai har yadaga hannu ya kwasheni da mari duk girman nan nawa Allah ma yaso ni babyna bata gani da tuni yasani jin kuyarta wallahi wallahi kufara bashi ruwan buta yarage wannan zafi ran dan wallahi idan baidai na wannan halin ba. bazai samu matar aure ba, ba iyayen da zasu dauki yarsu su bashi dan wallahi wataran sai ya baballa musu ita ya cuce su kuma ya kora musu ita gida dan bazai iya hakurin halin mata ba nidai wallahi shawara nake baku kusamu ruwan buta abashi yasha ko bedena ba zai rage,

"tunda yafara maganar shettima ke faman yin dariya saida yaji yayi shiru sannan yace to shikenan zan gaya masa kace abashi ruwan buta zaidena masifar da yake ko,

"zaro ido bossay yayi sannan yace la rufamin asiri dan Allah karkagaya masa kaqara jamin yadena kulani tunda daman haushina yake ji"

"shettima yace ai badaina kulaka zaiyiba wasu marukan zai baka kasan shifa yafi bawa mari muhimmanci fiye da komai "bossay yace ai naga alama tunda yayi min da yasa naga wuta ta wuce ta gefen idona amma de ba haka yakeyiwa mata ba iya maza yake mara "shettima yace har sumana saidai inbasuyi masa laifiba amma sunayi zai mare su kaamar yanda zai mari namiji haka suma zaimusu dan idan ransa yabaci ba ya bambamce mace da namiji kowa ma daya yake daukansa,

"jinjina kai bossay yayi yace amma iya kannen sa dan wallahi idan kamari mace sai ancika tara duk mari daya dubu biyar bare shi nashi na dabanne saidai yabiya dubu goma dan Allah indai irin marin da yayi min ne wata macen saita bakunci lahira ko kuma ya canza mata kamanni hallitar da Allah yayi mata,

shettima yace wayagaya maka zai biya ai ba wanda ya isa yasashi yabiya "bossay yace Allah nidai ina uban yarinya ya marar min 'ya sai ya biyani dan bazan rabu dashi ko yabiya ko in rama mata "shettima yace da kwa kaima kasha marin "bossay yace kasan Allah sai na rama mata kai nifa yanzuma idan yaqara dukana sai inda qarfina yaqare dan sai na nuna mishi nawa dantsen yafi nashi nifa ranar ma da ya mareni bansan meya hanani ramawa ba amma yayi nafarko yayi naqarshe kana ganin shi hakan nan ni ajikina inajin idan zamu danbatu sai nayi qasaqasa dashi dan nimafa ina da qarfin nan hmmm yafada yana cije baki irin zan kamashi dinnan ya dora da cewa Allah ya hadamu idan ya hadamu kar yaraba sai nasa yadena marin kowa aduniyar nan bare kuma mace danni su zan daukarwa ma fansar marin da yake musu dan dakatawa yayi da maganar.....,

"sosai shettima yake dariya saida yadan tsagaita sannan yace to shikenan yanzu muje filin dambe tunda gaka gashi sai kuraba raini nidai ina gefe duk wanda yayi winning zan mishi kyauta me tsoka "bossay yace fadi nawa zaka bayar kai nikuma ko beyi niya sai naje har inda yake nakira shi yanazuwa zanfara nannaushin shi idan yaji zafi sai yarama kaga daga nan sai mufara fadan rabaraini ko ya kace hakan ai yayi fadi nawa zaka bayar?
Chapter 30 · 0% Book details