Sashe 14
Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi go war jakadiyane yasata tsaida gwajegwajen da takeyi ta dauki daya kawai tasaka da hartasaka ta daidai yanda akeyi tayi rolling da mayafin sai kuma ta tuna ashefa bawai amatsayin wayayyirta zata zauna ba sai kawai tayi saurin kunce daurin datayi rigarma sai ta cireta gaba daya sai ta dau wata rigar marar ado sosai brown color sai dan wani ado da akayi aqarshen rigar da qarshen hannu sai wuyan ma duk akayi ado da coffee sai mayafin ta shima brown amma sai ta ajiye dan kwalin rigar ta dauki na wata rigar amma shi yellow ne itakanta saida tabawa kanta dariya ganin irin hadin ganbizar datayi kawai sai ta daura shi kamar dan kwali ta dauko red din hijabi ta sake daurawa akai kuma bekai mata har qasa ba kana kallonta zaka ga kalar rigar da kuma kalar dan kwalin da ta daura ga kuma jan hijabi sai ta fito das abinta kamar jakar kauye daga kanta tayi ta kalli wani dan tebur dayake cikin dakin an dan jere abubuwa akai qarasawa tayi tana zuwa kuwa taga wata hoda akai sai kwalli taso tasamu janbaki akai amma babu shi sai kawai hoda da kwalli kuma hodar ba mudubi ajiki bata damu daganin madubiba kawai ta hau shafa hodar ahaka tasan ta isa amma sai ta qara gogo wata ta qara dan barawa tanasane ta ringa shawafa har kan hijabin da kuma kan yellow dan kwalin data daura hmm abun ba acewa komai dan bazakace ga da hallitar datayi kamaba gaba daya ta canza kamanni kwalin ta zaro taqara ranbadawa akan idon ta harda yin jagira tajata atsaye kamar dogon yaro idan baka qura ido bama zakayi zaton bata raba girar ba saboda saura kadan ta hadesu bangama tsorata da itaba saida naga space din data bari na jagirar sai taja fashin goshi agurin(wannan abun da wasu sukeyi yanda ake zanen bille shima haka akeyinsa akan goshi wasuma tunda ga farkon gashin su ake jamusu shi har zuwa tsinin hancin su zakugansa an tsgawa mutum shi to itama irinshi tayi da kwalli), tana gama zanawa sai kawai ta dawo kan bakin ta nanma ta zana amma saboda ba kallon madubi take ba saikawai tazana ya kusan cike mata duka leban nasama da naqasa bayan tagama nan kuma sai kawai ta dawo kan kuma tunta taqara jan bille awajen dayan bangaren kumatun kuma sai taja abu guda biyu amma atsaye suke kuma ba wanda ya hade da wani guda dai dai ne saidai rashin kallon madubi yasa daya yafi daya tsawo taso tayi miyau miyau(uku uku nagefen baki da akeyi) amma tana tunanin bazata iyaba saboda zata iya cike fuskarta da baqi gaba daya shiyasa kawai tabarshi tanayi tanawa kanta dariya aciki ciki saboda kar jakadiya tajita tsayawa tayi tana tunani kuma me zata qara sakawa dazaisa de asan itafa yar qauye ce bata san komai ba bata da gata kuma ba kallon madubi take ba batasan tayi ba yanda kowa zai qara yarda da ita kuma bata yanda wani zai zargeta saboda shirmen dazata ringayi musu tsawar da jakadiyar ta daka matane yasata katse tunanin datake ubanwa yace kitaba min kayana waya baki izini tafada tana tunkaro inda take itakam takasa motsawa daga gurin bare tayi tunanin tashi duk dataji tahowarta kusa da ita bata gama tunanin ba taji matar tasa hannu ta tayar da ita tsaye tare da juyo da ita suna facing din juna hannu ta dafa zata kaiwa fuskarta mari amma sai ta dakata sakamakon tozali da tayi da fuskarta asukwane ta saketa tare da sakin dan qaramin ihu tana ja da baya baqaramin firgita tayi ba da ganin fuskarta ba gashi dama tubarkallah tana da idanu gasu farare tas kuma sai ta qara waro su akanta tana kallon ta da mamkin abun da yasata shiga wannan tashin hankalin harhaka batasan kuma zaro idon datakeyi matane yasa ta qara tsorata da itaba jakadiya na ja da baya itama tana qara binta hakan yasa jakadiya qara rudewa ganin tana qara tunkarota gashi bata bar zazzaro idanun da take ba kana kallon fuskar ta bayan haukan da tayi sai idanun zaka gani da kyar jakadiya ta iya budar baki tace dd...an...Allah kuyi ha....kurrrrrrri taqara da wata irin murya wace kanaji kasan mutum yagama tsotara tana fada ta kulle idon ta rufff harda dorawa da tafikan hannun ta wajen rufesu bakomai yasata hakan ba sai washe bakin da Azeema tayi mata fararen hakoranta suka bayyana sai tasake canza kamanni gaba daya ko farin sani kayiwa Azeema ayaude kallo daya baze sa ka ganetaba saidai idan tsayawa kayi sosai ka qura mata ido shima da kyar zaka iya ganeta bare kuma wanda ba wani sanin taba yayi sosai kana ganin ta zakace wannan ba halittar bil adam bace saidai jinsin jinnu(aljanu) abangaren Azeema kuwa sai da riyar taqe yi amma bata bari sauti ya fito ba dan ita saidaga baya ma tagane kwaliyar da tayine ya tsorata jakadiya shiyasa tana sane ta qara wangale mata haqora dan taqara firgita ta daman haushin ta tajeji saboda tun farkon ganinta ta nuna bata sonta ga abubuwan da take mata dan haka itama yanzu tasamu zata rama, jakadiya na kyarma jikin ta gaba daya sai faman karkarwa takeyi gashi sotake tafita daga dakin amma takasa daga qarfata daga gurin ganin hakan yasa Azeema qarasowa inda take daf da ita ta tsaya sai tasa hannu tacire hannun jakafiyar data rufe fuska dashi jakadiya najin anriqe hannun ta taqara damqe idonta tana so tayi magana amma bakin ta sai karkarwa yake takasa budeshi Azeema sai faman dariya take tanaso tayi mata magana amma tasan tana bude baki dariyar da take zata fito ahakan ma saura qiris dariyar ta kwace mata ta fito fili sai kawai tayi saurin sakar mata hannun tare da juya baya tan sa hannu tana kunshe dariyar ta aciki, jakadiya kam jin ansakar mata hannu yasata bude ido daya tana dan kyallowa aikwa tana kyallo bayan ta alamar ta juya baya yasata qarasa bude idon ta dan tabatarwa kanta abun da tagani datade ga da gaske ne ba kallon ta take ba sai kawai takwasa aguje ta bude qofa ta fita daga dakin tana gudu tana kiran nashiga uku wayyo Allah na tawa taqare yau nayi ido hudu da aljana tana cikin gudun tazo zata fita daga dakin kenan taji tayi karo da mutum qara rudewa tayi dan duk atunanin ta aljanar ce ta fito tasha gabanta wanu ihun tasaki tana neman hanyar fita taji andaka mata tsawa da cewa ke mahaukaciya inace baki da hankali daman wajen gudu ne da har zaki ture mutane saboda tsabar jahilace ke bakisan me yakamata ba nutsuwa tayi tare da zubewa awajen jikin ta na karkarwa tama kasa bashi hakuri hannu zai maketa yana cewa baki iyayuwa mutum laifiba kibashi hakuri kenan yakusa sauke mata lafiyayen mari kenan aka katseshi da cewa haba babana me yayi zafi haka ayi mata afuwa mana batasani ba kuma ka tsorata tane shiyasa takasa baka hakurin ranshi abace ya dago yana kallon papa da ya dakatar dashi da abun da yayi niya badanshi ba da baze dakata ba sai ya koya mata hankali papa na qarasowa gurin saiga Ammah ta qaraso falon tana cewa wai meke faruwane wa yataban na gaban goshin farin cikina tana fada tana gama qarasowa inda yake tare da ruqo hannun sa sai yanzuma idon ta ya sauka akan jakadiya dake durkushe agurin tana faman muzurai da idanu tare da hamdala aranta da Allah yakawo mata papa da ba abun da zai hanasa yayi mata dan isakan duka dan zuwa lokacin tsoron ganin aljana yabarta tsoron abun da zai matane akan gaba shine fargaban ta dan ba qaramin tsoranshi take ba hakannan ma inde yana gari bata son ko hada hanya suyi saboda dan qaramin abu zakai yahauka da masifa da duka bashida hakuri kwata kwata shiyasa ma mutane dayawa suke tsoron hada hanya dashi gudun matsala.... Ammah ce ta katseta da kiran sunan ta tace mari lafiya naganki anan me yafaru zatai magana kenan papa ya tareta da cewa bata saniba sukayi karo da shi shine zai kaimata duka na dakatar dashi shiyasa kika gansa haka itakuma takasa basa hakuri, saboda ta tsorata kinsan mutumin naki bashida hakuri yafada yana barin wajen ya koma kan kujera ya zauna yana kallon su, Ammah tace ayya Allah sarki mari meyasa baki duba hanaya ba lokaci da kike tafiya da har yasa kika biheshi wannan ai gangancine yakamata idan kina abun kirin ga kallon gaban ki tana fada mata ta maida duban ta kan Sam tace dan lele na kayi hakuri karkasa damuwa aranka manta da ita zata kiyaye nan gaba tafada tana qara ruqosa sanan tace zo muje kaci abin ci dan naga cikin ka yana neman abinci Allah yasama kaci na dare be tanka Mata ba tasan halinsa daman yanda ransa dinan yabaci bazai kula taba dan haka kawai sai taja hannun sa da niyar kaisa kan dinning shettima dake bayansu yayi gyaran murya hakanne yasata juyowa ta kallesa sannan tace daman tare kuke shine kayi shiru ai ban kula dakai ba wallahi shima ita yake kallo yace daman ina zaki ganni hankalin ki yana kansa ni ai komawa ma zanyi inda ake nemana tundade in mutum yazo nan yar wariya ake nuna mishi ido ake rufewa anuna ma basan da halittar sa agunba wannan san kan fa yayi yawa aringa ragewa inba haka ba kuma nidai baza aqara ganin qafata awajen nan ba tunda ba a son ganin mu sai mujanye jikin mu ko yafada yana qoqrin juyawa yabar wajen yana juyawa kuwa yaji saukar dundu abayan sa tare da talle masa qeya sannan ta jawo rigar sa tabaya amma ko gezau beyiba to basamude mutum sai qarfin tsiya yanzu ji yanda na daddage na jawo ka amma kaki motsawa to juyo ka qara gaya min abun dakake fada dannasan basu qare ba shiyasa nayi maka shiru ka qarasa ki juyowa yayi yana sakin murmushi ta can bangaren shima daman ba fita zaiyi ba yasan dole ta dakatar dashi dan sunsaba haka da it, gamin da yaqi juyowar yasata dan sassauta muraya tace kaifa kafiya matsala wallahi tuzuru kawai ina maka magana kayi qeqam sai kace tsohon soja da sauri ya jiyo yana kallon