← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 139

Sashe 21

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Azeema datayi zaune awajen tarasa wane irin tunani zatayi ita rashin maganar da batayi mata ba yafi tsaya mata arai taso tace mata wani abu amma tayi shiru batasan wane irin mataki zata dauka ba tana gurin har papa yaahigo saida taga ya wuce sannan ta miqe da kyar ta tafi daki zuciyar ta namata wani iri duk adagule take jinta duk dade a wani bangaren taji dadin ganin bata koreta ba kuma batayi mata fada ba to amma hakan bazaisa tayi sukuni ba har saitaji abun da zatace mata kafin ta saki jikin ta kayan jikin ta tacire ta shiga ta dauro alwala tazo tayi sallah aranar de bata jin zata iya cin wani abu kuma bazata sake fita ba dan haka tana idar da sallar tayi nafila tare da roqon Allah Allah yashige mata gaba akan abun da tazo yi Allah yasa tacika alqawarin da ta daukarwa kanta addu'a sosai tayi kafin ta cirehijab din tahau kan katifar dakin ta kwanta tareda nannadewa guri daya tana kwanciya taji shigowar mary ga mamakin ta saitaji mary nayi mata magana cikin lallami batare da daga murya ba tace kitashi kici abinci gashi nakawo miki dan Allah kiyi hakuri akan abubuwan da namiki bazan qaraba dan murmushi tayi aranta tace lalle ma matar nan haryanzu tsoron be bartaba kenan tashi tayi zaune tace ba komai komai ya wuce amma de nakoshi da abincin bacci nake ji kinga bandade da cin abinci ba (kunsa tade daman bawani abinci take ciba sosai saboda bata daci)
duk yanda taso tace abincin nan amma taqi ci bayanda ta iya haka tafita da abincin dan mayarwa kitchen daman Ammah ce tace ta takurata taci kuma taqi ci dan haka kawai ta mayar dashi saidai kuma bata gayawa Ammah cewa bata ciba kawai taje taci abinta ta qoshi sannan ta dawo dakin lokacin da tadawo har Azeema tayi bacci tunanin tafara anya kuwa ta kwanta akusa da ita dan itafa har yanzu bata gama yarda ba aljana bace a tsorace take da ita dan lallabawa tayi ta leqa idon ta dan ta tabbatar tayi baccin ko batayi ganin de da gaske bacci take yasata daukan abun rufar kan katifar ta shinfida aqasa ta dauko filo daya tayi kwanciyar ta aqasa dan sai tafi jin dadin hakan sai tafi samun kwanciyar hankali,

*shettima*
yana fitowa zuciyar sa taf da tambayoyi kala kala me yakawo yarinyar nan dole yasan dalilin zuwan ta gidan da wuri badan dare ma yayi ba da ayau zaije gidan su yaji ko ansani agida amma yabarwa gobe ki beje gidan suba idan yaje asibiti zai tambayi yayan ta yaji da haka yaqarasa wajen motar sa kdaman yagaji da neman sam shiyasa kawai ya yanke shawarar sai gobe yasan dole zasu hadu bude motar yayi yatafi gida dan zuciyar sa da tunanin sa gabada suna kan ganin da yayiwa yarinyar nan da tunane tunaneta yaja motarsa yabar masarautar yatafi gida,

Sam ya na ganin fitar sa yafito daga cikin wata mota yana bin motar sa da kallo aransa yace nasan da na tsaya da tuni kacika min kunnuwa da surutan banza kazo ma ka qara min ciwon kai inji da wanda yake damuna yana ayyana hakan yana tafiya har yakai bakin parta din Ammah sannan ya bude qofa yashiga saboda daman akwai maganar da yakeso suyi tun dazu amma waccen banzanr aljanar tazo ta bata masa lokaci da yaga be ganta a falo ba sai kawai yanufi dakin ta kai tsaye dan yanaso suyi sugama yaje ya kwanta dan bacci yakeji kwan kwasa qofar yayi aka bashi izinin shiga ya bude ya shiga abakin gado yazauna yana jiran Ammah ta idar da sallah suyi yatafi papa ne yace qaton banza kawai baka ga mutane ba kashigowa mutane guri ba sallama shiru yayi be kula masa ba papa yaci gaba da cewa au ga dan iska yana maka magana ko ciki ciki yace papa nayi fa saidai idan bakaji ba yafada yana hade rai saikace wanda akayiwa wani abun papa shiru yayi masa dan baya so yaci gaba da magana ransa yabaci saboda har yanzu haushinsa yakeji akan abun da yayi masa dazu shiyasa shirun sai yafi alkhairi dan zai iya gaya masa ba dadi shikuma daman ba hankali garesaba komai yazo bakinsa zai iya gaya masa shiyasa ya maida hankalin da kan littafin sa,

Sam yana sane yayi masa haka shikuma anasa tunanin idan yabiye masa zai iyayimasa maganar yarinyar cen shiyasa ya hade masa rai dan karyasamu fuskar yi masa maganar kuma hakan da yayi sai yaga yaci nasara be kulasaba hakan ba qaramin dadi yayi masa ba Ammah ce da ta idar dasallah tayi masa magana dacewa ina abokin naka yace yatafi gida tace gida kuma ince yakira ka kuci abinci shine yakama hanya ya tafi to kwa zaidawo yasame ni kai taso muje yace Ammah nima na qoshi muje de waje ina son magana dake tace aikam baka isaba sai kaci inba hakaba kuma ba maganar da zanyi dakai daganan ma ka tashi kaitafiyar ka tafada tana juyar dakai gefe irin taji haushinan saida yagana binta da kallo aransa yace idan akace maka tsoho tofa sai ahankali burkitattune sai kabisu yanda sukeso ahankali ya bude baki yace naji muje inci tace karma kacidin yace Ammah....yafada cike dagajiyawa da surutun dasuke yace wai bani nace zan ciba kuma sai kin qara batamin lokaci yafada yana miqewa tare da nufar qofar wake itama miqewa tayi tabi bayansa tana mita mutum sai bakin hali shi yayi yanda yake so amma kai idan kayi masa sai yanuna maka yaji haushi tana mita tafita lokacin har yakusan fita daga falon tayi saurin dakatar dashi cak yatsaya dande yanaso suyi maganar ne amma da baze saurarera ba dan haka kawai sai yajuyo be kalli inda take ba kawai ya wuce kan dinning kaitsaye yana zama tazo ta zuba masa saida yadauke kai sannan yafara ci beci wani me yawa ba yace mata ya qoshi ganin fuskarsa ahade yasa bata takura masa akan sai ya qara dole ba ta rabu dashi sannan tace to ina sauraron ka gyara zama yayi yana fuskantar ta da kyau itama duka hankalin ta ta miqa garesa dan taga kamar magana me muhimmaci zamata tunda taga ya tukara kansa haryayi abun da baiyi niyaba dan badan maganar ba tunda yace bazaici ba da baze taba ci din ba ko mai zatayi masa
ina sauraron ka taqara cemasa akaro na biyu...........
Chapter 21 · 0% Book details