Sashe 16
Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
matsoratan sukayi je kikirasu suzo suga abun da suke gudarwa 'yar qaramar dariya Ammah tayi tace lalle kam bari inkirasu tana fitowa daga dan lungun dakin ta hangosu zasu fita, da qyar suka samu qofar ta budu ashe garin saurin su suka murda key din jiki basusan ta shiga luck ba suke ta faman janta ahaka suna murdawa ta budu zasu fita Ammah tayi saurin dakatar dasu tace ba aljana bace sai kudawo matsoratan banza kawai ni mace ma nafiku jarumta wallahi atare gaba dayan su suka juyo tare da sauke ajiyar zuciya sameer ne yace Ammah kunduba kuwa sosai kun tabbatar ba aljana bace tace musu wallahi ba ita bace jin harda rantsuwarta yasasu dawo wa cikin falon suka zauna suna sauke numfarfashi kamar wanda sukayi gudun tsere suna haka papa ya shigo falon tare da Azeema cikin falon kanta aqasa bata kalli kowa ba suka shigo dakin Ammah ce tace 'yata matso nan suganki kinga duk girman nan nasu tsoro ne dasu gaba dayan su yayyanki ne zo ku gaisa tafada tana jawo hannun ta kusa dasu dukan su zuba mata ido sukayi suna jiran ta dago suganta saida Ammah tace ki gaida su mana dago su ganki tana sane take so tadago suganta dan tasan dole su tsorata tunda ba saba ganin irin hakan sukayi ba itakuma daman tasan 'yan kauye suna irin haka shiyasa ma bata sha wahala ba ta ganeta ahankali Azeema ta shiga dago da fuskarta ai bata gama bude ido bama ta kalle su sam yayi zunbur zai gudu Ammah tayi saurin riqeshi tace kai wai wane irin matsoracine ancemaka mutumce kamar kai amma ka wani tashi zaka gudu shide shettima tunda yaga zanen girarta bejira yagama ganin ta ba duka ya rufe idon sa da tafin hannu wansa amma jin batun Ammah yasa yayi saurin bude idon sa yana budewa kwa baiyarda sun hada ido ba yaqara saka hannu ya rufe fuskarsa, dakatawa yayi da tafiya amma sai yakoma bayan papa yana buya a bayan sa tare da leqowa dan yaqara ganin ta da kyau dan shi beyarda ba aljana bace hakan da yayi kuma yayi daidai da dagowar Azeema aikam karaf idon su suka hade da na juna amugun zabure Azeema ta miqe tsaye dan qara tabbatar wa idon ta abun da tagani kode mafarkin da fasaba yine da qarfi ta furta aljani na wallahi na yarda aljani ne aljaniiiiiiii tafada tana qanqame Ammah datake kusa da ita tare da sakin wata uwar qara da saida ta karade duk falon tanayi kuma jikin ta yasaki gaba daya ta tafi luuu zata fadi Ammah tayi saurin tarota, Shettima da yarufe fuska jin muryar da yasani yasashi saurin bude fuskar sa dan ganin inda me muryar take duk da be gama tantance abun da kunnuwansa sukaji ye masa ba..........✍