← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 139

Sashe 42

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wanine ya taho aguje yana cewa yallabai yallabai gashi ance inkawo maka wani file ne a hannun sa yana daf da cimmasu bossay yaqarayin saurin shan gabansa murya qasa qasa yace kai baka san meke faruwa ba ko da dan mamaki saurayin yake kallon sa sannan yace meke faruwa a ina kuma bossay yace kai yanzu tsakanin ka da Allah baka sani ba kode wasa. Kake min yace kamar ya wasa nataho zan basa saqo kuma ka tsareni kana cemin bansan abun dake faruwa ba to kagaya min me yake faruwa ni banji ance komai yafaruba ni matsamin kaga har yakusan kaiwa waje banaso yafita baisa hannnun ba qara shan gabansa yayi yace kai wallahi da akwai abun dake faruwa acikin nan gidan amma nayi mamaki dabaka sani ba to ni ya akai nasani mtsw dayan yaja tsaki yace nibansani kai nifa banma sanka anan ba kuma taya har zakafini sanin abun dake faruwa anan kasan kwa muqamina agidan nan bossay yace kai nima fa ma aikacine anan jiya nafara zuwa shiyasa baka sanni ba amma daga zuwana ni na gane abubuwa da yawa amma nayi mamaki da kai baka gane ba amma de bari indawo kajirani zangaya maka abundake faruwa kaima nasan sai kayi mamaki yanakaiwa nan yayi gaba da dan saurinsa ganin har sun fita daga gate din yana tafiya yana dariyar abun da yayiwa wannan kwata kwat zacen dayake masa bakai ba gindi amma wancen baigane hakan ba kuma yatsaya yabiye masa lalle sokone bashida wayo ahaka shima yafita daga gate din yana fita yaga suna kiciniyar shigar dashi mota saboda suna fitowa daidai minti biyu na cika abun kwa da aka fesamasa yafara aiki take yazube musu awajen Allah ma yasosu babu mutane awajen qaraswa yayi gurin su shima yaci gaba da taimaka musu suka shigar dashi da kyar saboda mutumin akwai dan jiki ba laifi bayan sun sakashi aciki sai sam yace shettima yashiga inda mutumin yake shikuma bossay ya shiga gaba shi kuma zaiyi tuqin gaba dayansu da mamaki suke kallon sa wai zaiyi tuqi da kansa musammanma shettima da shide tunda suke baifi ya qirga saunawa yataba yin tuqiba shima kuma tun loakcin yarintar su,
babata lokaci bossay yashiga inda yace masa din shi kuma ya shiga driver seat yazauna tare da tayar da motar suna tayarwa saiga wannan saurayin ya qaraso wajen da gudun sa yataho yanaso ya tsayar dasu amma ina tuni sam yaja motar a 360 suka bar wajen tare da badeshi da qura suka qara gaba kwafa yayi yace amma yallabai bai kyauta min ba ina tayi masa magana amma yaki kulani daman ance bashida mutunci akwai wulakanta mutane amma shi baitaba yarda ba sai yau kwafa yayi cike da taqaici ya juya yakoma ciki yana tafaman mita dan har ga Allah baiji dadin abun da yayi masa ba,
da gudu yake jan motar kamar zasu tashi sama shettima de da yaga yakasa hakuri saida yayi magana yace dan Allah kabimu ahankali gudun yayi yawa gashi kuma nidai baganin ka nake kanajan mota ba bare ince ka kware gaskiya kabimu ahankali,
Banza yayi dashi saima qara qure giya dayayi dan kamar zigashi yayi haka yaje jan motar ga mugun overtaking din da yajeyi yanda bashi da hakuri a zahira haka atuqima bashi da hakuri baya dagawa mota qafa saidai ita ta daga masa haka yaje tayi akan titin wani wajen ma inyazo ya wuce sai anzageshi saboda irin gudun da yakeyi Allah nedai yakarsu babu abun da yasane su har suka qaraso wani dan qaramin gida sannan yayi parking awaje sannan yace wa bossay je kabude mana gate din budewa yayi ya sauka sannan yaje yabude musu shikuma yaja motar zuwa cikin gidan bossay ya mayar ya rufe sannan yabi bayansu,

har gaban qofar da zata shigar dasu yakai motar sannan ya kashe ya fito lokacin bossay har ya qaraso gurin haduwa suka qara yi suka kamashi suka shiga dashi ciki,falo ne empty babu koma acikin sa wani daki suka nufa dashi suna shiga suka cillasa aqasa tare da rufe qofar sam yace musu su tafi sabar sa ahaka bossay yace idan ya gudu fa yace babu inda zashi zan kullesa ai kuma duk qofar da yataba ma shocking zaiji iya wannan ma kadai ya ishasa kama annan zai tazama har sai nakamo kowa nahadasu sannan inyafadi gaskiya yafita in kuma yayi wasa a fita da gawarsa,
yana kaiwa nan yayi gaba ba wanda yayi magana acikin su sukabi bayansu suka fita daga cikin gidan ya kullosa aciki bayan sun fita ta wajema suka saka kwado ajiki ( padlock) sannan suka nufi motar su amma yanzu sam sai kawai yabude back seat ya shiga da suka ga haka sai shettima yakalli bossay yace yanzu kuma kai sai ka tuqamu tunda abun bidabi yazama ko cewar bossay shettima yace eh mana tunda nayi shima yayi kaga yanzu kuma kaine alayi,,
toshikena cewar bossay sannan ya bude motar ya shiga shima shettima yazagaya ya shiga bossay ya tayar da motar suka bar unguwar sam ne yace mutafi office sai agwada wannan wayar mubincike ta daman akwai dayar nan ma da ban dubata duk sai adubasu yanzu shettima yace eh hakan yayi ma gwara aringayin komai da wuri dannaga alamar akwai aiki agabanmu sai munyi da gaske daga farawa munfara da mai taurin kai Allah yasa sauran kar subamu wahala irin tashi,
bossay dake tuqi yace ai saima ansamu wadanda suka fishi shifa kawai kudin albashi za aqaramasa amma kaji yaqi fada ina wadanda ake turawa kudade kallifa lokacin da aka tura min kudin nan masu yawa yanzu in akasamu wanda baida shi meyema bazasu iya yiba dan ganin sun samu kudin ai ba qaramin shiri zamuyi ba dan sai ya dauke mu lokaci mai tsawo banajin za a iya kamosu duka a lokaci qalilan dole muna buqatar lokaci,
Sam yace awajen ka ne kake ganin haka amma nan da sati sai mun kama duk wani mai hannu aciki indai inyi zamuyi da gaske,

Shettima yace to Allah yasa mu iyayi amma nima ta maganar tasa nake ganin kamar zamu sha wahala wajen kamasu tunda kudi za abasu kuma fa kar kamanta koda munkama wannan mutumin shimafa sakashi akai shima kuma zai iya yiyuwa wanda yasashi din shima sakashi akai gano qarshen maishirya wannan abun ba abune mai sauqi ba wallahi,

agurinku ba cewar sameeer daga nan kuma yayi shiru ahalade suka cigaba da tafiya kowa na fadar akbarkancin bakinsa da yanda zasu bullowa alamarin tayanda zaizo musu da sauqi komai batare da wata wahalaba ahaka har suka je asibitin basu dena ba bayan sun shiga sunfito daga mota suna qoqarin shiga ciki suka hadu da saleem da sauri yaqaraso gurin su tare da miqa musu hannu suka gaisa abun mamaki har sam ma baqi bashiba bashi hannun yayi suka gaisa kallonsa yamayar kan shettima yace dr. kwana biyu bana samun ka indai nazo hope dai lafiya fuska asake yace komai lafiya lau wallahi kuma ai ina shigowa kawai dai dadewa ne banayi kaima kuma naga kwana biyu baka zuwa inda nake ,
"yace wallahi dr ina zuwa bana samun ka yace to shikenan tunda haka kace na yarada suna maganar suna tafiya har suka qarasa gurin da zasu benen inda office din sam yake sai saleem yadaka ta yace to dr sai kafito bari nima inje inqarasa wani aiki dr yace to shikenan sai anjiman har yajuya zaitafi sai kawai Azeema ta fado masa shi sai yanzuma ya tuna dan yadan sha'afa ma da ganinta da yayi juyowa yayi yace saleem, saleem da har yadanyi nisa yajiyo kiran da shettima ke masa amsawa yay tare da juyowa yana shirin tahowa inda yake sai shettima yace aa basai kazo ba kawai idan kagama kafin katafi gida ina son ganin ka kanemeni ko awayane idan baka sameni a office ba,
"saleem yace to dr in sha Allah afito lafiya daganan yajuya yaci gaba da tafiya shima shettima haurawa yafara yi dan tuntuni daman sam da bossay sunyi gaba sunbarshi,
yana tafiya yana qara tunanin Azeema ransa fal sai yanzu tunanin ganin nata yadawo masa sabo dan yama manta tun awashe garin ranar yaso yakirata awaya amma ya manta yaukam idan ya koma gida zai kirata koda yaji ta bakin saleem din amma sai ya kirata yaji ta bakinta, tura qofar yayi ya shiga basame su a office din ba dan haka yanufi dakin da yake da tabbaccin suna ciki ajiye tunanin nata yayi agefe saboda kar yahanasa yin wani aikin da yakamata yayi da sallam ya shiga duk suka amsa samun su yayi akan kujera sun zauna bossay na danne danne awaya shikuma sam yana bude yar qaramar wayar da dadda tabasu shima guri yasamu ya zauna yana kallon wayar dake hannu sameeer ganin yana qoqarin budeta yasa shi cewa naga zaka bareta? "yace eh taqi kunnuwane watakil ta lalace shettima yace ba lalle ba watakil cajine babu agwada sakata caji mugani,
miqama sa yayi sannan yace sakata to mugani nima manta nasa kata caji gashinan kasaka bari indan watsa ruwa kafin nan nasan lokacin sallah yayi idan munyi sallah sai mu hau kan aikin ko,
shettima yace najima kamar anfara kiran sallah kayi sauri kafito,
bandakin yanufa ba dadewa yafito sai ya canza wasu kayan sannan shima shettima ya shiga amma shi ba wanka yayi ba alwala ya dauro bayan ya fito yacewa bossay yaje yayo shima tashi yayi ya shiga yayo sannan suka jera suka fita zuwa masallacin dake cikin asibitin..........,✍️✍️

*bakwa comment shiyasa nima banason yi bakusan comment shine qarfin gwaiwar marubuci ba idan bakwayi sai mutum yaga kamar bakwa karantawa shiyasa nima bandamu da sai nayi ba watarana naken made hannuna inqi yi wlh gsky Yakamata ku gyara Ni in faranta muku amma ku bakuso bakwa bani kwarin gwiwa*
[5/28, 10:18 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿39&40

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

                  *Abuja*
Chapter 42 · 0% Book details